Ta Hannun Yohanna 17:1-26
17 Bayan Yesu ya faɗi abubuwan nan, sai ya ɗaga idanunsa sama, ya ce: “Ya Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka ɗanka domin ɗanka ya ɗaukaka ka,
2 kamar yadda ka ba shi iko a kan dukan mutane, domin ya iya ba da rai na har abada ga dukan waɗanda ka ba shi.
3 Abin da zai sa su sami rai na har abada shi ne su san ka,* Allah makaɗaici mai gaskiya, da kuma wanda ka aiko Yesu Kristi.
4 Na ɗaukaka ka a duniya, domin na gama aikin da ka ba ni in yi.
5 Yanzu, Ya Uba, ka ɗaukaka ni a gefenka da ɗaukakar da nake da ita a gefenka tun kafin a halicci duniya.
6 “Na sa mutanen da ka ba ni daga duniyar nan su san sunanka. Su naka ne, amma ka ba ni su kuma sun bi kalmarka.
7 Yanzu sun san cewa duk abubuwan da ka ba ni naka ne;
8 domin na gaya musu dukan abubuwan da ka gaya mini, sun amince da su kuma sun san cewa na zo a matsayin wakilinka, sun ba da gaskiya cewa kai ne ka aiko ni.
9 Na yi roƙo domin su; ba don duniya na yi roƙo ba, amma domin waɗanda ka ba ni ne, gama su naka ne;
10 dukan abubuwan da nake da su naka ne, abubuwan da kake da su kuma nawa ne. Ƙari ga haka, an ɗaukaka ni a tsakaninsu.
11 “Ba na cikin duniya kuma, amma su suna cikin duniya kuma ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai Tsarki, ka lura da su saboda sunanka wanda ka ba ni, domin su kasance da haɗin kai,* kamar yadda ni da kai muke da haɗin kai.*
12 Saꞌad da nake tare da su, na lura da su saboda sunanka wanda ka ba ni; na kāre su, kuma babu ɗayansu da ya hallaka, sai dai ɗan hallaka, domin a cika abin da yake cikin nassi.
13 Yanzu ina zuwa wurinka, kuma ina faɗan abubuwan nan a duniya, domin su sami cikakken farin ciki kamar ni.
14 Na gaya musu kalmarka, amma duniya ta tsane su, domin su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne.
15 “Ba na roƙo don ka ɗauke su daga duniya, amma don ka lura da su saboda mugun nan.
16 Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniyar nan ba ne.
17 Ka tsarkake su ta wurin gaskiya; domin kalmarka gaskiya ce.
18 Kamar yadda ka aiko ni cikin duniya, ni ma na aike su cikin duniya.
19 Ina tsarkake kaina a madadinsu, domin su ma a tsarkake su ta wurin gaskiya.
20 “Ina roƙo, ba don waɗannan kaɗai ba, amma domin waɗanda suke ba da gaskiya gare ni ta wurin kalmarsu,
21 domin dukansu su zama ɗaya, kamar yadda kai Uba kake da haɗin kai da ni, ni ma ina da haɗin kai da kai, su ma su kasance da haɗin kai da mu, domin duniya ta gaskata cewa kai ne ka aiko ni.
22 Na ba su ɗaukakar da ka ba ni, domin su zama ɗaya, kamar yadda muke ɗaya.
23 Ina da haɗin kai da su, kai kuma kana da haɗin kai da ni, hakan zai sa su kasance da haɗin kai sosai, domin duniya ta san cewa kai ne ka aiko ni, kuma kana ƙaunar su kamar yadda ka ƙaunace ni.
24 Ya Uba, ina so waɗanda ka ba ni su kasance da ni a wurin da nake, domin su ga ɗaukakata da ka ba ni, gama kana ƙauna ta tun kafin farkon duniya.*
25 Ya Uba Mai Adalci, har yanzu duniya ba ta san ka ba, amma na san ka, kuma waɗannan sun gane cewa kai ne ka aiko ni.
26 Na sa su san sunanka, kuma zan ƙara sa su sani, domin su kasance da irin ƙaunar da ka nuna mini, ni kuma in kasance da haɗin kai da su.”
Hasiya
^ Ko kuma “su koya game da kai.”
^ Ko kuma “zama ɗaya.”
^ Ko kuma “muke ɗaya.”
^ Da alama wannan yana nufin lokacin da Adamu da Hauwaꞌu suka haifi yara.