Ta Hannun Yohanna 16:1-33

  • Za a iya kashe almajiran Yesu (1-4a)

  • Aikin ruhu mai tsarki (4b-16)

  • Baƙin cikin almajiran zai koma farin ciki (17-24)

  • Yesu ya yi nasara a kan duniya (25-33)

16  “Na gaya muku waɗannan abubuwa ne don kada ku yi tuntuɓe. 2  Mutane za su kore ku daga majamiꞌa. Hakika, lokaci yana zuwa ma da duk wanda ya kashe ku, zai yi tsammani ya yi aikin Allah ne. 3  Amma za su yi abubuwan nan ne domin ba su san Uban ko kuma ni ba. 4  Duk da haka, na gaya muku waɗannan abubuwan ne domin a lokacin da suka soma faruwa, za ku tuna cewa na gaya muku. “Ban gaya muku abubuwan nan da farko ba, domin ina tare da ku. 5  Amma yanzu zan je wurin Wanda ya aiko ni; duk da haka, babu wani cikinku da ya tambaye ni cewa, ‘Ina za ka je?’ 6  Amma don na gaya muku abubuwan nan, kun soma baƙin ciki sosai. 7  Duk da haka, ina gaya muku gaskiya, ku ne za ku amfana daga tafiyata. Domin idan ban tafi ba, mai taimakon ba zai zo muku ba; amma idan na tafi, zan aiko muku shi. 8  Kuma saꞌad da ya zo, zai ba wa duniya tabbaci game da abin da zunubi, da adalci, da kuma shariꞌa suke nufi: 9  na farko game da zunubi, domin ba sa ba da gaskiya gare ni; 10  saꞌan nan game da adalci, domin zan je wurin Uban kuma ba za ku sake gani na ba; 11  saꞌan nan game da shariꞌa, domin an yi wa mai mulkin duniyar nan shariꞌa. 12  “Ina da sauran abubuwa da yawa da zan gaya muku, amma ba za ku iya fahimtar su a yanzu ba. 13  Duk da haka, saꞌad da wannan ya zo, wato ruhun gaskiya, zai taimaka muku ku fahimci kome game da gaskiyar, domin ba zai yi magana bisa ga tunanin kansa ba, amma zai faɗi abin da ya ji, kuma zai sanar muku abubuwan da za su faru a nan gaba. 14  Wannan zai ɗaukaka ni, domin zai karɓi abin da yake nawa kuma ya sanar muku. 15  Duk abubuwan da Uban yake da su, nawa ne. Shi ya sa na ce zai karɓi abin da yake nawa ya kuma sanar muku. 16  Bayan ɗan lokaci, ba za ku ƙara gani na ba, kuma bayan ɗan lokaci, za ku gan ni.” 17  Sai wasu cikin almajiransa suka ce wa juna: “Me yake nufi saꞌad da ya ce mana, ‘Bayan ɗan lokaci ba za ku sake gani na ba, bayan ɗan lokaci za ku gan ni,’ kuma ‘domin zan je wurin Uban’?” 18  Don haka, suna cewa: “Me yake nufi da cewa, ‘bayan ɗan lokaci’? Ba mu san abin da yake magana a kai ba.” 19  Yesu ya san cewa suna so su yi masa tambaya, sai ya ce musu: “Kuna tambayar juna wannan abin domin na ce: ‘A cikin ɗan lokaci, ba za ku gan ni ba, kuma a cikin ɗan lokaci, za ku gan ni’? 20  A gaskiya ina gaya muku, za ku yi kuka kuna ihu, amma duniya za ta yi farin ciki; za ku yi baƙin ciki amma baƙin cikinku zai koma ya zama farin ciki. 21  Saꞌad da mace take haifuwa, takan ji zafi sosai domin lokacin haifuwarta ya yi, amma bayan ta haifu, ba za ta tuna da wahalar da ta sha ba domin tana farin ciki cewa ta haifi jariri cikin duniya. 22  Ku ma, yanzu kuna baƙin ciki, amma zan sake ganin ku, za ku yi farin ciki kuma babu wanda zai ƙwace farin cikin daga wurinku. 23  A ranar, ba za ku yi mini tambaya ba. A gaskiya ina gaya muku, duk abin da kuka roƙi Uban, zai ba ku a cikin sunana. 24  Har yanzu, ba ku roƙi kome a cikin sunana ba. Ku roƙa za a ba ku, domin farin cikinku ya zama cikakke. 25  “Na gaya muku abubuwan nan cikin misalai. Amma lokaci na zuwa da ba zan ƙara yi muku magana cikin misalai ba, zan gaya muku abubuwa dalla-dalla game da Uban. 26  A ranar, za ku roƙi abu daga wurin Uban a cikin sunana; ba na nufin cewa ni ne zan roƙa muku. 27  Uban da kansa yana ƙaunar ku, domin kuna ƙauna ta, kun kuma ba da gaskiya cewa na zo ne a matsayin wanda Allah ya aiko. 28  Na zo cikin duniya ne a matsayin wanda Ubana ya aiko. Yanzu zan bar duniya kuma in koma wurin Uban.” 29  Sai almajiransa suka ce: “Ga shi, kana yin magana dalla-dalla yanzu, ba da misalai ba. 30  Yanzu mun san cewa ka san kome kuma ba ka bukatar wani ya yi maka tambaya. Ta hakan, mun gaskata cewa ka zo ne daga wurin Allah.” 31  Yesu ya amsa musu ya ce: “Kun gaskata yanzu? 32  Ga shi, lokaci yana zuwa, ya riga ma ya zo, da kowannenku zai gudu zuwa gidansa kuma ku bar ni ni kaɗai. Amma, ba zan kasance ni kaɗai ba, domin Uban yana tare da ni. 33  Na faɗa muku abubuwan nan ne domin ku sami salama ta wurina. Za a tsananta muku a duniya, amma ku yi ƙarfin zuciya, domin na yi nasara a kan duniya.”

Hasiya