Ta Hannun Yohanna 15:1-27
15 “Ni ne itacen inabi na gaske, Ubana kuma shi ne manomin.
2 Yakan sare duk wani reshe a jikina da ba ya ba da ꞌyaꞌya, kuma ya tsabtace duk wani reshe mai ba da ꞌyaꞌya don ya ƙara ba da ꞌyaꞌya.
3 Ko a yanzu ma kuna da tsabta, saboda maganar da na gaya muku.
4 Ku kasance da haɗin kai da ni, ni kuma zan kasance da haɗin kai da ku. Kamar yadda reshe ba zai iya ba da ꞌyaꞌya ba sai dai in yana jikin itacen inabin, haka nan ma, ba za ku iya ba da ꞌyaꞌya ba, sai dai in kun kasance da haɗin kai da ni.
5 Ni ne itacen inabi; ku ne rassan itacen. Duk wanda ya kasance da haɗin kai da ni, kuma ni ma na kasance da haɗin kai da shi, zai ba da ꞌyaꞌya sosai; domin in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba.
6 Idan wani bai kasance da haɗin kai da ni ba, za a sare shi kamar reshe kuma zai bushe. Mutane za su tattara rassan kuma su jefa su cikin wuta su ƙone.
7 Idan kun kasance da haɗin kai da ni, kuma maganata ta kasance a cikinku, duk abin da kuka roƙa za a yi muku.
8 Za a ɗaukaka Ubana idan kuka ci-gaba da ba da ꞌyaꞌya kuma kuka nuna cewa ku almajiraina ne.
9 Kamar yadda Uban ya ƙaunace ni, haka na ƙaunace ku; ku kasance cikin ƙaunata.
10 Idan kuka bi dokokina, za ku kasance cikin ƙaunata, kamar yadda na bi dokokin Uban kuma na kasance cikin ƙaunarsa.
11 “Na gaya muku haka domin farin cikina ya kasance a cikinku, farin cikinku kuma ya zama cikakke.
12 Dokar da nake ba ku ita ce, ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.
13 Ba wanda yake da ƙaunar da ta fi wannan, wato mutum ya ba da ransa a madadin abokansa.
14 Ku abokaina ne idan kun bi dokar da nake ba ku.
15 Na daina kiran ku bayi, domin bawa ba ya sanin abin da maigidansa yake yi. Amma ina kiran ku abokai, domin na gaya muku dukan abubuwan da na ji daga wurin Ubana.
16 Ba ku ne kuka zaɓe ni ba, amma ni ne na zaɓe ku, kuma na sa ku je ku ci-gaba da ba da ꞌyaꞌya, ꞌyaꞌyanku kuma su dawwama, domin duk abin da kuka roƙi Uban cikin sunana, zai ba ku.
17 “Dokar da nake ba ku ita ce, ku ƙaunaci juna.
18 Idan duniya ta tsane ku, ku san cewa ta tsane ni kafin ta tsane ku.
19 Da ku na duniya ne, da duniya ta so ku domin ku nata ne. Amma da yake ku ba na duniya ba ne, domin na zaɓe ku daga cikin duniya, saboda haka ne duniya ta tsane ku.
20 Ku tuna da abin da na faɗa muku cewa: Bawa bai fi maigidansa ba. Idan sun tsananta mini, za su kuma tsananta muku; da sun yi biyayya da maganata, za su yi biyayya da taku kuma.
21 Amma za su yi muku dukan waɗannan abubuwan saboda sunana, domin ba su san Wanda ya aiko ni ba.
22 Da a ce ban zo kuma na yi musu magana ba, da ba su kasance da zunubi ba. Amma yanzu ba su da wata hujja don zunubansu.
23 Duk wanda ya tsane ni ya tsani Ubana ma.
24 Da a ce ban yi ayyukan da babu wanda ya taɓa yi a tsakaninsu ba, da ba su kasance da zunubi ba; amma yanzu sun gan ni, sun kuma tsane ni tare da Ubana.
25 Amma hakan ya faru ne domin a cika abin da aka rubuta a Dokarsu* cewa: ‘Sun tsane ni ba tare da dalili ba.’
26 Idan mai taimako da zan aika muku daga wurin Ubana ya zo, wato ruhun gaskiya, da zai zo daga wurin Uban, shi ne zai ba da shaida game da ni;
27 saꞌan nan, ku ma za ku ba da shaida game da ni, domin kuna tare da ni tun daga farko.
Hasiya
^ Ko kuma “Dokar Musa.”