Ta Hannun Yohanna 12:1-50
12 Kwana shida kafin Bikin Ƙetarewa, sai Yesu ya zo Betani, wurin da Liꞌazaru yake, wanda Yesu ya ta da daga mutuwa.
2 Sai suka shirya masa abincin yamma a wurin, kuma Marta tana yi musu hidima, amma Liꞌazaru yana cikin waɗanda suka zauna suna cin abinci tare da shi.
3 Sai Maryamu ta ɗauki wajen rabin litan mān ƙamshi mai tsada sosai, wanda aka yi da nad* zalla, sai ta zuba mān a ƙafafun Yesu. Kuma ta share ƙafafunsa da gashin kanta. Sai ƙamshin mān ya cika gidan.
4 Amma Yahuda Iskariyoti, ɗaya daga cikin almajiransa, wanda ya kusan cin amanarsa ya ce:
5 “Me ya sa ba a sayar da mān ƙamshin nan dinari* ɗari uku ba, kuma a ba wa talakawa kuɗin?”
6 Ya faɗa hakan ne ba domin ya damu da talakawa ba, amma domin shi ɓarawo ne. Shi ne mai riƙe akwatin kuɗi, kuma yakan saci kuɗi daga ciki.
7 Sai Yesu ya ce: “Ku bar ta mana ta ci-gaba da yin abin da take yi don ta shirya ni don ranar da za a binne ni.
8 Domin a kullum kuna tare da talakawa, amma ni ba zan kasance da ku kullum ba.”
9 Da taron Yahudawa mai yawa suka ji labari cewa Yesu yana wurin, sai suka zo ba domin Yesu kawai ba, amma domin su ga Liꞌazaru wanda Yesu ya ta da daga mutuwa.
10 Sai manyan firistoci suka ƙulla su kashe Liꞌazaru ma,
11 tun da yake shi ne ya sa Yahudawa da yawa suke zuwa wurin kuma suke ba da gaskiya ga Yesu.
12 Washegari, jamaꞌa da yawa da suka zo bikin, sun ji cewa Yesu yana kan hanya zuwa Urushalima.
13 Sai suka ɗauki rassan itatuwan dabino kuma suka fita don su same shi, kuma suka soma ihu suna cewa: “Ya Allah, muna roƙo, ka cece shi! Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Jehobah,* Sarkin Israꞌila!”
14 Saꞌad da Yesu ya sami ɗan jaki, sai ya zauna a kai, kamar yadda yake a rubuce cewa:
15 “Kada ki ji tsoro ꞌyar Sihiyona. Ga sarkinki yana zuwa zaune a kan jaki.”
16 Da farko, almajiransa ba su fahimci abubuwan nan ba, amma saꞌad da aka ɗaukaka Yesu, sai suka tuna cewa an rubuta abubuwan nan game da shi, kuma sun yi masa abubuwan nan.
17 Jamaꞌa da suke tare da shi saꞌad da ya kira Liꞌazaru daga kabari kuma ya ta da shi daga mutuwa, sun ci-gaba da ba da shaidar abin da ya faru.
18 Shi ya sa jamaꞌa suka fita don su haɗu da shi, domin sun ji cewa ya yi wannan abin ban mamaki.
19 Sai Farisiyawan suka soma faɗa a tsakaninsu cewa: “Kun gani ko, muna aikin banza ne kawai. Ga shi, kowa na bin sa.”
20 A cikin waɗanda suka zo bikin don yin sujada, akwai wasu mutanen Girka.
21 Sai suka sami Filibus, wanda ya fito daga Betsaida da ke Galili, kuma suka soma roƙon sa suna cewa: “Maigirma, muna so mu ga Yesu.”
22 Filibus ya gaya wa Andarawus. Sai Andarawus da Filibus kuma suka zo suka gaya wa Yesu.
23 Amma Yesu ya gaya musu cewa: “Lokaci ya yi da za a ɗaukaka Ɗan mutum.
24 A gaskiya ina gaya muku, in ba dai ƙwayar alkama ta faɗi ta mutu ba, za ta zauna ita kaɗai, amma idan ta mutu, za ta ba da ꞌyaꞌya da yawa.
25 Duk wanda yake son ransa, zai hallaka shi, amma duk wanda ya tsani ransa a duniyar nan, zai kiyaye shi don ya sami rai na har abada.
26 Idan mutum zai yi mini hidima, sai ya bi ni, kuma a duk inda nake, a wurin ne mai yi mini hidima zai kasance. Idan mutum zai yi mini hidima, Ubana zai girmama shi.
27 Yanzu na damu, me kuma zan ce? Ya Uba, ka cece ni daga wannan lokacin. Duk da haka, saboda wannan lokacin ne na zo.
28 Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.” Sai wata murya daga sama ta ce: “Na ɗaukaka shi, kuma zan sake ɗaukaka shi.”
29 Da jamaꞌa da suke tsaye a wurin suka ji muryar, sai suka soma cewa: “An yi tsawa.” Wasu kuma sun ce: “Wani malaꞌika ne ya yi masa magana.”
30 Sai Yesu ya amsa ya ce: “Muryar nan ta yi magana ba domin ni ba, amma domin ku ne.
31 Yanzu ana yi wa duniyar nan shariꞌa, kuma za a kawar da mai mulkin duniyar nan.
32 Duk da haka, idan aka ɗaga ni daga duniya, zan jawo mutane dabam-dabam zuwa wurina.”
33 Ya faɗi wannan ne domin ya nuna irin mutuwar da zai yi.
34 Sai jamaꞌar suka amsa masa suka ce: “Doka* ta ce Kristi zai kasance har abada. Ta yaya za ka ce dole a ɗaga Ɗan mutum? Wane ne wannan Ɗan mutum?”
35 Sai Yesu ya ce musu: “Hasken zai kasance a tsakaninku na ɗan lokaci. Ku yi tafiya tun kuna da hasken, domin kada duhu ya sha ƙarfinku. Duk wanda yake tafiya a cikin duhu, bai san inda za shi ba.
36 Saꞌad da kuke da hasken, ku ba da gaskiya ga hasken, domin ku iya zama ꞌyaꞌyan haske.”
Bayan da Yesu ya faɗi abubuwan nan, sai ya tafi ya ɓoye kansa daga gare su.
37 Ko da yake ya yi abubuwan ban mamaki da yawa a gabansu, sun ƙi su ba da gaskiya gare shi,
38 domin a cika abin da annabi Ishaya ya faɗa cewa: “Jehobah,* wa ya ba da gaskiya ga abin da ya ji daga wurinmu? Kuma wane ne Jehobah* ya nuna wa ikonsa?”*
39 Dalilin da ya sa ba su ba da gaskiya ba, shi ne wani abu kuma da Ishaya ya rubuta cewa:
40 “Ya mai da su makafi, ya kuma sa zuciyarsu ta yi tauri, domin kada su gani da idanunsu, kuma su gane da zuciyarsu, har su juyo in kuma warkar da su.”
41 Ishaya ya faɗi abubuwan nan domin ya ga ɗaukakarsa, kuma ya yi magana game da shi.
42 Duk da haka, mutane da yawa har ma da masu mulki sun ba da gaskiya gare shi, amma ba su nuna cewa sun ba da gaskiya gare shi ba saboda Farisiyawa, don kada a kore su daga majamiꞌa,
43 gama sun fi son ɗaukaka daga wurin mutane, fiye da ɗaukaka daga wurin Allah.
44 Amma Yesu ya ɗaga murya ya ce: “Duk wanda ya ba da gaskiya gare ni, ba a gare ni kawai ya ba da gaskiya ba, amma ya ba da gaskiya ga wanda ya aiko ni ma.
45 Kuma duk wanda ya gan ni, ya ga Wanda ya aiko ni.
46 Na zo ne kamar haske a duniya, domin wanda yake ba da gaskiya gare ni kada ya ci-gaba da kasancewa a cikin duhu.
47 Amma idan wani ya ji abubuwan da na faɗa kuma bai aikata su ba, ba na masa shariꞌa, domin ban zo in yi wa duniya shariꞌa ba, amma domin in ceci duniya ne.
48 Duk wanda ya ƙi ni kuma bai karɓi abubuwan da nake faɗa ba, yana da wanda zai yi masa shariꞌa. Abin da na faɗa ne zai yi masa shariꞌa a ranar ƙarshe.
49 Abin da nake faɗa ba daga wurina ba ne, amma Uba wanda ya aiko ni ne ya ba ni umurni game da abin da zan faɗa da abin da zan koyar.
50 Kuma na san cewa umurninsa zai sa mutum ya sami rai na har abada. Saboda haka, duk abin da na faɗa, na faɗa yadda Ubana ya gaya mini ne.”
Hasiya
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Dinari ɗaya ya yi daidai da kuɗin da ake biyan lebura na aikin yini ɗaya.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ko kuma “Dokar Musa.”
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ A yaren Girka, “hannunsa.”