Ta Hannun Matiyu 9:1-38

  • Yesu ya warkar da mutumin da jikinsa ya shanye (1-8)

  • Yesu ya kira Matiyu (9-13)

  • Tambaya game da yin azumi (14-17)

  • ꞌYar Yayirus; wata mata ta taɓa mayafin Yesu (18-26)

  • Yesu ya warkar da makafi da kuma bebe (27-34)

  • Girbin yana da yawa amma maꞌaikatan kaɗan ne (35-38)

9  Sai Yesu ya shiga jirgin ruwa, ya haye tekun ya je garinsu. 2  Sai aka kawo masa wani mutum da jikinsa ya shanye kwance a kan tabarma.* Da ya ga bangaskiyarsu, sai Yesu ya ce wa mutumin da jikinsa ya shanye: “Kada ka damu ɗana! An gafarta zunubanka.” 3  Da jin wannan, sai waɗansu marubuta suka ce a zuciyarsu: “Mutumin nan yana saɓo.” 4  Da yake Yesu ya san abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya ce: “Me ya sa kuke mugun tunani a zuciyarku? 5  Alal misali, wanne ne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuma a ce, ‘Ka tashi ka yi tafiya’? 6  Amma domin ku san cewa Ɗan mutum yana da iko a duniya ya gafarta zunubai—” sai ya ce wa mutumin nan da jikinsa ya shanye: “Ka tashi, ka ɗauki tabarmarka, ka tafi gida.” 7  Sai ya tashi ya tafi gida. 8  Da jamaꞌar suka ga haka, sai suka ji tsoro, kuma suka ɗaukaka Allah wanda ya ba wa mutane irin wannan ikon. 9  Bayan haka, da Yesu ya ci-gaba da tafiya, sai ya ga wani mutum da ake kira Matiyu yana zaune a ofishin karɓan haraji, sai ya ce masa: “Ka zama mabiyina.” Nan da nan sai ya tashi ya bi Yesu. 10  Daga baya, da Yesu yake cin abinci a gidan Matiyu, sai mutane da yawa masu karɓan haraji, da masu zunubi, suka zo kuma suka soma cin abinci tare da Yesu da almajiransa. 11  Saꞌad da Farisiyawa suka ga hakan, sai suka ce wa almajiransa: “Me ya sa malaminku yana cin abinci tare da masu karɓan haraji da masu zunubi?” 12  Da Yesu ya ji hakan, sai ya ce: “Masu ƙoshin lafiya ba sa bukatar likita, amma masu rashin lafiya suna bukatar sa. 13  Ku je ku koyi abin da wannan yake nufi, wato: ‘Jinƙai nake so a wurinku, ba hadaya ba.’ Domin na zo ne in kira masu zunubi, ba masu adalci ba.” 14  Sai almajiran Yohanna suka zo wurinsa suka tambaye shi: “Me ya sa mu da Farisiyawa muke yin azumi amma almajiranka ba sa yi?” 15  Sai Yesu ya ce musu: “Abokan ango ba su da dalilin yin baƙin ciki muddin angon yana tare da su, ko ba haka ba? Amma lokaci na zuwa da za a ɗauke angon daga wurinsu, saꞌan nan za su yi azumi. 16  Ba wanda zai yi fācin tsohuwar riga da sabon yadi, domin sabon yadin zai sa tsohuwar rigar ta yage, yagewar ma za ta fi ta dā. 17  Kuma mutane ba sa zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna.* Idan sun yi hakan, salkunan za su fashe, ruwan inabin zai zube, kuma salkunan za su lalace. Amma mutane sukan zuba sabon ruwan inabi a cikin sababbin salkuna, ta hakan ba abin da zai sami ruwan inabin da kuma salkunan.” 18  Da Yesu yake kan gaya musu waɗannan abubuwan, sai wani mutum wanda shugaba ne ya zo wurinsa kuma ya durƙusa a gabansa ya ce: “Na san yanzu ꞌyata ta riga ta rasu, amma ka zo ka taɓa ta kuma za ta rayu.” 19  Sai Yesu da almajiransa suka tashi, suka bi shi. 20  Sai ga wata mata da ta yi shekara goma sha biyu tana fama da yoyon jini, ta zo ta bayansa kuma ta taɓa bakin mayafinsa, 21  domin ta yi ta faɗa wa kanta cewa: “Idan na taɓa mayafinsa kawai, zan warke.” 22  Sai Yesu ya juya, ya gan ta, ya ce mata: “Kada ki damu ꞌyata! Bangaskiyarki ta warkar da ke.” Nan take matar ta warke. 23  Saꞌad da Yesu ya shiga gidan shugaban kuma ya ga masu busa sarewa da taron jamaꞌa suna ta hayaniya, 24  sai ya ce: “Ku bar nan, domin ƙaramar yarinyar ba ta mutu ba, amma tana barci ne.” Da suka ji hakan, sai suka soma yi masa dariyar reni. 25  Da aka fitar da jamaꞌar waje, sai Yesu ya shiga gidan, ya kama hannun ƙaramar yarinyar, sai yarinyar ta tashi. 26  Hakika, labarin abin da ya faru ya yaɗu a dukan yankin. 27  Saꞌad da Yesu ya bar wurin, sai makafi biyu suka bi shi, suna kira da babbar murya suna cewa: “Ka ji tausayin mu, ya Ɗan Dauda.” 28  Bayan da ya shiga cikin gida, sai makafin suka zo suka same shi kuma Yesu ya tambaye su cewa: “Kun ba da gaskiya cewa zan iya warkar da ku?” Sai suka amsa suka ce: “E, Ubangiji.” 29  Sai ya taɓa idanunsu, yana cewa: “Tun da kun ba da gaskiya, bari idanunku su buɗu.” 30  Kuma idanunsu sun buɗu. Ƙari ga haka, Yesu ya ja musu kunne yana cewa: “Kada ku gaya wa kowa abin da ya faru.” 31  Amma da suka bar wurin, sai suka yaɗa labari game da shi a dukan yankin. 32  Da mutanen suke barin wurin, sai aka kawo masa wani mutum da bebe ne kuma yana da aljani. 33  Saꞌad da Yesu ya fitar da aljanin, sai mutumin nan da bebe ne ya yi magana. Sai jamaꞌar da suke wurin suka yi mamaki kuma suka ce: “Ba a taɓa ganin abu kamar haka a Israꞌila ba.” 34  Amma Farisiyawa suna cewa: “Da ikon shugaban aljanu ne yake fitar da aljanu.” 35  Daga nan, Yesu ya bi dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majamiꞌunsu, yana shelar labari mai daɗi na Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowane irin cuta da rashin lafiya. 36  Da ya ga jamaꞌa sun taru, sai ya ji tausayin su domin suna kama da tumakin da aka fere fatarsu kuma suna hawa da sauka don ba su da makiyayi. 37  Sai ya ce wa almajiransa: “Hakika, girbin yana da yawa, amma maꞌaikatan kaɗan ne. 38  Saboda haka, ku roƙi Mai Gonar ya aiko da maꞌaikata su yi masa girbi.”

Hasiya

Wani abu ne da aka yi da itace kamar shimfiɗa da za a iya ɗaukan marar lafiya da shi.
Wasu jakunkunan zuba ruwa da aka yi da fatar dabba.