Ta Hannun Matiyu 5:1-48
-
HUƊUBA A KAN DUTSE (1-48)
5 Saꞌad da Yesu ya ga mutane da yawa, sai ya haura kan tudu; bayan da ya zauna, sai mabiyansa suka zo wurinsa.
2 Sai ya buɗe baki ya soma koyar da su yana cewa:
3 “Waɗanda suka san cewa suna bukatar ja-gorancin Allah,* suna farin ciki, domin Mulkin sama nasu ne.
4 “Waɗanda suke makoki, suna farin ciki, domin za a taꞌazantar da su.
5 “Waɗanda suke da tawaliꞌu,* suna farin ciki, domin za su gāji duniya.
6 “Waɗanda suke son yin abin da ya dace a gaban Allah,* suna farin ciki, domin za su sami abin da suke so.*
7 “Waɗanda suke yin jinƙai, suna farin ciki, domin su ma za a yi musu jinƙai.
8 “Waɗanda zuciyarsu ke da tsabta,* suna farin ciki, domin za su ga Allah.
9 “Waɗanda suke sa a yi zaman lafiya, suna farin ciki, domin za a kira su ꞌyaꞌyan Allah.
10 “Waɗanda aka tsananta musu saboda suna yin abin da ya dace, suna farin ciki, domin Mulkin sama nasu ne.
11 “Ku masu farin ciki ne saꞌad da mutane suka zage ku, suka tsananta muku, kuma suka yi kowane irin maganganun ƙarya a kanku saboda ni.
12 Ku yi farin ciki da murna sosai, saboda kuna da lada mai yawa a sama, domin haka suka tsananta wa annabawa da suka yi rayuwa kafin ku.
13 “Ku ne gishirin duniya, amma idan gishirin ya rasa ɗanɗanonsa, ta yaya za a maido da ɗanɗanon? Ba za a iya yin kome da shi kuma ba, sai dai a zubar da shi a waje kuma mutane su tattaka shi.
14 “Ku ne hasken duniya. Ba za a iya ɓoye birnin da ke kan tudu ba.
15 Idan mutane suka kunna fitila, ba sa rufe ta,* amma sukan ajiye ta a kan sandar riƙe fitila domin ta ba da haske ga dukan mutanen gidan.
16 Haka ku ma, ku zama masu haske ga mutane, domin idan suka ga ayyuka masu kyau da kuke yi, za su ɗaukaka Ubanku wanda yake cikin sama.
17 “Kada ku yi tsammanin cewa na zo ne in sa mutane su daina bin Doka* ko kuma abubuwan da annabawa suka rubuta. Amma na zo ne domin in cika su.
18 A gaskiya ina gaya muku cewa, ko da sama da ƙasa sun shuɗe, babu harafi mafi ƙanƙanta ko layi guda daga Dokar da zai shuɗe har sai dukan abubuwan nan sun cika.
19 Saboda haka, duk wanda ya taka ɗaya daga cikin dokokin nan mafi ƙanƙanta kuma ya koya wa mutane su ma su yi hakan, za a ɗauke shi a matsayin wanda bai dace ya shiga Mulkin sama ba. Amma duk wanda ya bi dokokin nan kuma ya koya wa mutane su ma su yi hakan, za a ɗauke shi a matsayin wanda ya dace ya shiga Mulkin sama.
20 Ina gaya muku cewa, idan adalcinku bai fi na marubuta da Farisiyawa ba, ba za ku taɓa shiga Mulkin sama ba.
21 “Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā cewa: ‘Kada ka yi kisa, kuma duk wanda ya yi kisa, za a yi masa shariꞌa a kotu.’
22 Amma ina gaya muku, duk wanda ya ci-gaba da yin fushi da ɗanꞌuwansa, za a yi masa shariꞌa a kotu. Kuma duk wanda yake zagin ɗanꞌuwansa kuma ya yi masa baƙar magana, za a yi masa shariꞌa a Kotun Ƙoli. Ƙari ga haka, duk wanda ya ce ma wani, ‘Wawan banza!’ za a jefa shi a Gehenna.*
23 “Idan kana kan kai kyauta a bagade sai ka tuna cewa ɗanꞌuwanka yana fushi da kai,
24 ka bar kyautar a gaban bagaden, ka koma, ka sasanta da ɗanꞌuwanka tukuna. Bayan haka, sai ka dawo ka miƙa kyautarka.
25 “Idan wani ya kai ƙarar ka, ka yi sauri ka sasanta da shi tun kuna hanyar zuwa kotu. Idan ba haka ba, zai haɗa ka da alƙali, alƙalin kuma ya haɗa ka da jamiꞌin tsaro, jamiꞌin tsaron kuma ya jefa ka a kurkuku.
26 A gaskiya ina gaya maka cewa, kafin a fitar da kai daga kurkukun, sai ka biya dukan kuɗin* da kake da shi.
27 “Kun dai ji an faɗa cewa: ‘Kada ka yi zina.’
28 Amma ina gaya muku cewa, duk wanda ya ci-gaba da kallon mace har ya yi shaꞌawar yin zina da ita, ya riga ya yi zina da ita a zuciyarsa.
29 Idan idonka na dama yana sa ka yi zunubi, ka cire shi ka yar. Gara ka rasa wata gaɓa na jikinka da a jefa jikinka gabaki-ɗaya a cikin Gehenna.*
30 Idan hannunka na dama yana sa ka yi zunubi, ka yanke shi ka yar. Gara ka rasa wata gaɓa na jikinka da a jefa jikinka gabaki-ɗaya a cikin Gehenna.*
31 “Ƙari ga haka, an kuma ce: ‘Duk wanda ya kashe aurensa, dole ne ya ba wa matarsa takardar shaida na kashe auren.’
32 Amma, ina gaya muku cewa, duk wanda ya kashe aurensa ba tare da matarsa ta yi lalata* ba, ya sa ta a hanyar yin zina ke nan, kuma duk wanda ya aure ta ya yi zina.
33 “Kun kuma ji an gaya wa mutanen zamanin dā cewa: ‘Kada ka yi rantsuwa ba tare da cikawa ba, dole ne ka cika alkawarin da ka yi wa Jehobah.’*
34 Amma ina gaya muku cewa: Kada ma ku yi rantsuwa, ko da da sama ne, domin kursiyin Allah ne.
35 Kada ku yi rantsuwa da ƙasa, domin wurin sa ƙafafunsa ne; ko kuma ku yi rantsuwa da Urushalima, domin birnin babban Sarki ne.
36 Kada kuwa ka rantse da kanka, domin ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya ya zama fari ko baƙi ba.
37 Bari kalmarku ‘E’ ta zama e, ‘Aꞌa’ ta zama aꞌa. Abin da ya wuce haka kuwa daga wurin mugun nan yake.
38 “Kun dai ji an faɗa cewa: ‘Ido a madadin ido, kuma haƙori a madadin haƙori.’
39 Amma ina ce muku: Kada ku rama abin da mugu ya yi muku. Idan wani ya mare ka a kumatunka na dama, ka juya masa ɗayan ya mara.
40 Idan wani yana so ya kai ka kotu domin yana so ya ƙwace rigar ciki da ka saka, ka ba shi har da mayafinka ma;
41 idan wani mai iko ya sa ka dole ka ɗauka masa kaya zuwa wuri mai nisan kilomita ɗaya, ka ɗauki kayan har kilomita biyu.
42 Idan wani ya roƙe ka abu, ka ba shi. Wanda kuma ya zo neman bashi daga wurinka kada ka hana masa.
43 “Kun dai ji an faɗa cewa: ‘Dole ka ƙaunaci maƙwabcinka kuma ka ƙi abokin gābanka.’
44 Amma ina gaya muku cewa: Ku ci-gaba da ƙaunar abokan gābanku kuma ku yi adduꞌa domin waɗanda suke tsananta muku,
45 ta yin haka, za ku nuna cewa ku ꞌyaꞌyan Ubanku ne da ke sama, domin yana sa rana ta yi haske a kan masu kirki da marasa kirki. Kuma yana aiko da ruwan sama a kan masu adalci da marasa adalci.
46 Idan kuna ƙaunar waɗanda suke ƙaunar ku kawai, wane lada ne kuke da shi? Ba abin da masu karɓan haraji suke yi ba ke nan?
47 Idan kuna gaishe da ꞌyanꞌuwanku kawai, ba ku yi wani abu na musamman da ya fi na wasu ba. Ai, waɗanda ba Yahudawa ba ma suna yin hakan.
48 Saboda haka, dole ne ku zama cikakku,* kamar yadda Ubanku na sama yake cikakke.
Hasiya
^ Ko kuma “waɗanda suke roƙo a ba su ruhu mai tsarki.”
^ Ko kuma “Marasa zafin rai.”
^ A yaren Girka, “jin yunwa da ƙishin yin adalci.”
^ A yaren Girka, “za a ƙosar da su.”
^ Ko kuma “Waɗanda ba sa tunanin kowane irin mugunta.”
^ Ko kuma “rufe ta da kwando.”
^ Ko kuma “Dokar Musa.”
^ Wurin da ake ƙona datti a bayan garin Urushalima. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ko kuma “ƙwandala mafi ƙanƙanta.”
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ A yaren Girka, por·neiʹa. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ko kuma “kamilai.”