Ta Hannun Matiyu 28:1-20
28 Bayan Ranar Assabaci, da sassafe a ranar farko ta mako, Maryamu Magdalin da ɗayan Maryamun sun zo su duba kabarin.
2 Ga shi kuwa, an yi wata babbar girgizar ƙasa, domin wani malaꞌikan Jehobah* ya sauko daga sama, ya ture dutsen da aka rufe kabarin da shi, kuma ya zauna a kai.
3 Kamanninsa kamar walƙiya ne, kuma rigarsa ta yi fari fat kamar dusar ƙanƙara.
4 Da masu gadin suka gan shi, tsoro ya kama su sosai, sun yi rawar jiki kuma suka faɗi a ƙasa, suka zama kamar matattu.
5 Amma malaꞌikan ya gaya wa matan cewa: “Kada ku ji tsoro, don na san cewa kuna neman Yesu ne wanda aka kashe a kan gungume.
6 Ba ya nan, domin an tashe shi, kamar yadda ya faɗa. Ku zo ku ga wurin da aka kwantar da shi dā ma.
7 Ku je da wuri, ku gaya wa almajiransa cewa an ta da shi daga mutuwa. Ga shi, za shi Galili ya jira ku a wurin. Za ku gan shi a wurin. Ku tuna da abin da na gaya muku.”
8 Sai suka bar kabarin da sauri, cike da farin ciki da tsoro, sun yi gudu don su je su gaya ma almajiransa.
9 Sai Yesu ya same su, kuma ya ce musu: “Na gaishe ku!” Sai suka matso kusa, suka riƙe ƙafafunsa kuma suka durƙusa a gabansa.
10 Sai Yesu ya ce musu: “Kada ku ji tsoro! Ku je ku gaya ma almajiraina su tafi Galili. A can za su gan ni.”
11 Da suke kan hanya, sai wasu masu gadin suka shiga cikin birni kuma suka gaya wa manyan firistoci duk abubuwan da suka faru.
12 Bayan manyan firistocin suka haɗu da dattawa kuma suka yi shawara, sai suka ba wa sojojin kuɗin azurfa mai yawa
13 kuma suka ce musu: “Ku ce, ‘Almajiransa sun zo da dare, sun sace shi saꞌad da muke barci.’
14 Idan kuma labarin ya kai kunnen gwamna, za mu yi masa bayani* kuma ba kwa bukatar ku damu.”
15 Sai masu gadin suka ɗauki kuɗin azurfar, kuma suka yi abin da aka umurce su su yi, kuma labarin da aka ci-gaba da yaɗawa a tsakanin Yahudawa har wa yau ke nan.
16 Amma almajiran Yesu goma sha ɗaya suka tafi Galili, kuma suka hau tudun, wurin da Yesu ya shirya su haɗu.
17 Da suka gan shi, sai suka durƙusa a gabansa, amma wasu sun yi shakka.
18 Sai Yesu ya matso kusa kuma ya ce musu: “An ba ni dukan iko a sama da kuma duniya.
19 Don haka, ku je ku koyar da mutanen dukan alꞌummai su zama almajiraina, ku riƙa yi musu baftisma a cikin sunan Uba, da na Ɗa, da na ruhu mai tsarki,
20 ku riƙa koyar da su su yi dukan abubuwan da na umurce ku. Ga shi kuwa, ina tare da ku kullum har ƙarshen zamani.”*
Hasiya
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ A yaren Girka, “rinjaye shi.”
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.