Ta Hannun Matiyu 27:1-66
27 Da gari ya waye, dukan manyan firistoci, da dattawan jamaꞌa, sun yi shawara a kan yadda za su kashe Yesu.
2 Bayan da suka ɗaure shi, sai suka tafi da shi kuma suka ba da shi ga gwamna mai suna Bilatus.
3 Saꞌad da Yahuda da ya ci amanarsa ya ga cewa an yanke wa Yesu hukuncin kisa, ya yi da-na-sani. Sai ya mai da kuɗin azurfa talatin ɗin ga manyan firistoci da dattawan jamaꞌa,
4 yana cewa: “Na yi zunubi da na ci amanar mutumin da bai yi laifi ba.” Amma suka ce masa: “Ina ruwanmu? Wannan damuwarka ce!”
5 Sai ya zubar da kuɗin azurfar a cikin haikali kuma ya fita. Sai ya je ya rataye kansa.
6 Amma manyan firistocin suka kwashe kuɗin azurfar kuma suka ce: “Ba zai dace mu saka kuɗin nan a cikin wurin ajiye kuɗi na haikali ba, domin kuɗin jini ne.”
7 Bayan sun yi shawara, sai suka yi amfani da kuɗin suka sayi wani fili* domin ya zama filin binne baƙi.
8 Don haka ana kiran filin, Filin Jini har zuwa yau.
9 Hakan ya cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya wanda ya ce: “Suka ɗauki kuɗin azurfa talatin nan, kuɗin da wasu mutanen Israꞌila suka yarda a biya a kan mutumin,
10 kuma suka sayi filin maginan tukwane kamar yadda Jehobah* ya umurce ni.”
11 Yesu ya tsaya a gaban gwamna kuma gwamnan ya tambaye shi cewa: “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya ce: “Kai ma da kanka ka faɗi hakan.”
12 Amma saꞌad da manyan firistoci da dattawa suke zargin sa, bai ce kome ba.
13 Sai Bilatus ya ce masa: “Ba ka ji yawan abubuwan da suke zargin ka a kai ba?”
14 Amma Yesu bai amsa masa ba, ko kalma ɗaya bai faɗa ba. Hakan ya sa gwamnan ya yi mamaki sosai.
15 A kowane lokacin biki, gwamnan ya saba sake wa jamaꞌar fursuna, duk wanda suke so.
16 A daidai lokacin, akwai wani mugun fursuna mai suna Barabbas da ake tsare da shi.
17 Saꞌad da suka taru, sai Bilatus ya ce musu: “Wane ne kuke so in sake muku? Barabbas ko kuma Yesu wanda ake ce da shi Kristi?”
18 Don Bilatus ya san cewa kishi ne ya sa suka ba da shi.
19 Ƙari ga haka, saꞌad da yake zaune a kujerar shariꞌa, matarsa ta aika masa saƙo cewa: “Kada ka sa hannu a shaꞌanin mutumin nan mai adalci, domin yau na sha wahala sosai a mafarki saboda shi.”
20 Sai manyan firistoci da dattawa suka zuga jamaꞌar su ce a sake musu Barabbas, amma a kashe Yesu.
21 Sai gwamnan ya ce musu: “Wane ne a cikin su biyun nan kuke so in sake muku?” Sai suka ce: “Barabbas.”
22 Bilatus ya ce musu: “Mene ne kuke so in yi da Yesu, wanda ake ce da shi Kristi?” Sai dukansu suka ce: “A rataye shi a kan gungume!”*
23 Ya ce musu: “Me ya sa? Wane laifi ne ya yi?” Har ila suka ci-gaba da ihu, suna cewa: “A rataye shi a kan gungume!”
24 Da Bilatus ya ga ba abin da zai iya yi, kuma mutanen suna ƙoƙarin ta da hankali, sai Bilatus ya ɗebi ruwa, ya wanke hannayensa a gaban jamaꞌar, yana cewa: “Alhakin jinin mutumin nan ba ya kaina, a kanku yake.”
25 Sai dukan mutanen suka ce: “Bari alhakin jininsa ya zo kanmu da kuma kan yaranmu.”
26 Saꞌan nan ya sa an sake musu Barabbas. Bayan ya sa aka yi wa Yesu bulala, sai ya ba da shi don a kashe shi a kan gungume.
27 Daga nan sojojin gwamna suka kai Yesu gidan gwamna kuma suka tara dukan sojoji kewaye da shi.
28 Sun tuɓe masa kaya, sai suka saka masa jan mayafi,
29 sai suka yi wani rawanin ƙaya suka saka masa a kai. Suka sa ya riƙe sanda a hannunsa na dama. Sai suka durƙusa a gabansa, suka yi masa baꞌa suna cewa: “Ranka ya daɗe,* Sarkin Yahudawa!”
30 Kuma suka tofa masa miyau, suka ɗauki sandar, suka soma buga masa a kai.
31 A ƙarshe, bayan sun gama yi masa baꞌa, sai suka tuɓe masa jan mayafin, kuma suka saka masa kayansa, sai suka tafi da shi don su rataye shi a kan gungume.
32 Yayin da suke tafiya, sai suka haɗu da wani mutumin Sayirin mai suna Siman. Suka tilasta wa mutumin nan ya ɗauki gungumen azabar* Yesu.
33 Saꞌad da suka kai wurin da ake kira Golgota, wato, Wurin Ƙoƙon Kai,
34 sai suka ba shi ruwan inabi da aka haɗa da wani abu mai ɗaci domin ya sha; amma da ya ɗanɗana sai ya ƙi sha.
35 Bayan da suka rataye shi a kan gungume, sai suka jefa ƙuriꞌa don su raba mayafinsa,
36 kuma suka zauna a wurin suna gadin sa.
37 A saman gungumen, sun rubuta laifin da aka ce ya yi, cewa: “Wannan shi ne Yesu, Sarkin Yahudawa.”
38 An rataye ɓarayi biyu tare da shi, ɗaya a hannun hagunsa, ɗaya kuma a hannun damansa.
39 Mutanen da suke wucewa suna ta zagin sa, suna kaɗa kansu
40 kuma suna cewa: “Kai da za ka rushe haikali kuma ka gina shi cikin kwana uku, ka ceci kanka! Idan kai ɗan Allah ne, ka sauko mana daga gungumen azabar!”*
41 Hakan nan ma, manyan firistoci, da marubuta, da kuma dattawa suka soma yi masa baꞌa suna cewa:
42 “Ya ceci wasu; amma ya kasa ceton kansa! Idan shi ne Sarkin Israꞌila, bari ya sauko daga kan gungumen azabar,* za mu yarda da shi.
43 Ya dogara ga Allah; bari Allah ya cece shi yanzu idan Ya amince da shi, domin ya ce, ‘Ni Ɗan Allah ne.’”
44 Har ɓarayin da aka rataye su tare da shi ma, suna yi masa baƙar magana.
45 Daga wajen ƙarfe sha biyu na rana,* sai duhu ya rufe koꞌina a ƙasar har zuwa ƙarfe uku na yamma.*
46 A wajen ƙarfe uku na yamma, Yesu ya yi magana da babbar murya, yana cewa: “Eli, Eli, lama sabaktani?” wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”
47 Saꞌad da wasu daga cikin mutanen da suke tsaye a wajen suka ji hakan, sai suka ce: “Mutumin nan yana kiran Iliya.”
48 Sai nan da nan, wani ya yi gudu, ya je ya ɗauki soso ya jiƙa shi a cikin ruwan inabi da ya yi tsami, ya soka shi a sanda, ya miƙa masa ya sha.
49 Amma sauran suka ce: “Ku bar shi! Bari mu ga ko Iliya zai zo ya cece shi.”
50 Yesu ya sake yin ihu da babbar murya, sai ya mutu.*
51 Sai labulen da ke haikali ya rabu kashi biyu daga sama zuwa ƙasa. Aka yi girgizar ƙasa, kuma duwatsu sun tsage.
52 Kaburbura sun buɗu kuma tsarkaka da yawa da suka mutu, sun tashi.
53 (Mutanen da suka fito daga kaburburan, sun shiga cikin birni mai tsarki bayan da Yesu ya tashi daga mutuwa), kuma mutane da yawa sun gan su.
54 Saꞌad da jamiꞌin sojan da sauran sojojin da suke gadin Yesu tare da shi suka ga girgizar ƙasar da abubuwan da ke faruwa, sun ji tsoro sosai kuma suka ce: “Ba shakka, wannan Ɗan Allah ne.”
55 Kuma mata da yawa da suka bi Yesu daga Galili don su yi masa hidima, sun tsaya daga nesa suna kallon abin da yake faruwa.
56 A cikinsu akwai Maryamu Magdalin, da Maryamu mamar Yaƙub da Joses, da mamar ꞌyaꞌyan Zabadi.
57 Da yamma ta yi kusa, wani mutum mai arziki daga Arimatiya mai suna Yusufu wanda shi ma ya zama almajirin Yesu, ya zo.
58 Wannan mutumin ya je wurin Bilatus kuma ya roƙa a ba shi gawar Yesu. Sai Bilatus ya ba da izini a ba shi.
59 Yusufu ya ɗauki gawar Yesu, ya naɗe shi da yadin lilin mai tsabta,
60 ya kwantar da shi a cikin sabon kabarinsa, wanda ya tona a cikin dutse. Sai ya tura wani babban dutse ya rufe bakin kabarin, ya tafi.
61 Amma Maryamu Magdalin da ɗayan Maryamun, sun ci-gaba da zama a gaban kabarin.
62 Washegari, wato bayan Ranar Shiri,* sai manyan firistoci da Farisiyawa suka taru a gaban Bilatus,
63 suka ce: “Ranka ya daɗe, mun tuna abin da mayaudarin nan ya faɗa tun yana da rai, ya ce, ‘Bayan kwana uku za a tashe ni.’
64 Saboda haka, ka sa a yi gadin kabarin da kyau har zuwa rana ta uku, don kada almajiransa su zo su sace shi kuma su ce wa mutane, ‘An ta da shi daga mutuwa!’ Idan hakan ya faru, yaudara na ƙarshen zai fi na farkon.”
65 Bilatus ya ce musu: “Ku ɗebi sojoji, ku je ku yi gadin shi duk yadda za ku iya.”
66 Sai suka je suka rufe dutsen da ya tare bakin kabarin sosai kuma suka sa sojoji su yi gadin shi.
Hasiya
^ A yaren Girka, “filin maginan tukwane.” Mai yiwuwa fili ne da maginan tukwane suke yin sanaꞌarsu.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ko kuma “A kashe shi a kan gungume!”
^ Ko kuma “gaisuwa.”
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ A yaren Girka, “Wajen awa ta 6.”
^ A yaren Girka, “Wajen awa ta 9.”
^ A yaren Girka, “saki ransa.”
^ Rana ce kafin Ranar Assabaci, da Yahudawa suke shirye-shirye don Assabaci.