Ta Hannun Matiyu 15:1-39

  • Yesu ya fallasa alꞌadun ꞌyanꞌadam (1-9)

  • Abin da ke ƙazantar da mutum daga zuciya ne (10-20)

  • Bangaskiya mai ƙarfi da ꞌyar Finikiya ta nuna (21-28)

  • Yesu ya warkar da cututtuka da yawa (29-31)

  • Yesu ya ciyar da maza dubu huɗu (32-39)

15  Sai Farisiyawa da marubuta daga Urushalima suka zo wurin Yesu suna cewa: 2  “Me ya sa almajiranka ba sa bin alꞌadun kakanninmu? Alal misali, ba sa wanke hannayensu* kafin su ci abinci.” 3  Yesu ya amsa musu ya ce: “Me ya sa kuke taka dokokin Allah saboda alꞌadunku? 4  Alal misali, Allah ya ce, ‘Ka girmama babanka da mamarka,’ kuma ‘A kashe duk wanda ya zagi* babansa ko mamarsa.’ 5  Amma kukan ce, ‘Duk wanda ya ce wa babansa ko mamarsa: “Duk abin da nake da shi da zai amfane ku, na keɓe wa Allah,” 6  ba dole ba ne ya girmama babansa.’ Kun mayar da kalmar Allah banza saboda alꞌadunku. 7  Ku munafukai, ya dace da Ishaya ya yi annabci a kanku cewa: 8  ‘Mutanen nan fa, da baki ne kawai suke girmama ni, amma zukatansu ba sa tare da ni. 9  A banza ne suke bauta mini, domin suna koyar da dokokin mutane a matsayin kalmar Allah.’” 10  Yesu ya kira jamaꞌar kuma ya ce musu: “Ku saurara don ku gane abin da nake faɗa: 11  Ba abin da yake shiga bakin mutum ne yake ƙazantar da shi a gaban Allah ba, sai dai abin da yake fitowa daga bakinsa.” 12  Sai almajiransa suka zo suka ce masa: “Ka san cewa Farisiyawa sun yi fushi da suka ji maganarka?” 13  Sai ya amsa ya ce musu: “Duk shukin da ba Ubana na sama ba ne ya shuka, za a tuge shi. 14  Bar su kawai. Su makafi ne masu yi wa makafi ja-goranci. Idan makaho ya yi wa makaho ja-goranci, ai, dukansu za su faɗi cikin rami.” 15  Bitrus ya amsa masa cewa: “Ka bayyana mana misalin nan.” 16  Sai ya ce: “Har ila ku ma ba ku fahimta ba? 17  Ba ku san cewa duk abin da ya bi ta baki zai shiga cikin ciki ba, saꞌan nan ya fita daga jiki ya shiga bayan gida ba? 18  Amma abin da yake fitowa daga baki daga zuciya ne yake fitowa, kuma abubuwan nan ne suke ƙazantar da mutum a gaban Allah. 19  Alal misali, daga zuciya ne mugayen tunani suke fitowa, kamar: kisa, da zina, da lalata,* da sata, da shaidar ƙarya, da kuma saɓo. 20  Abubuwan nan ne suke ƙazantar da mutum; amma cin abinci ba tare da wanke hannaye ba, ba ya ƙazantar da mutum.” 21  Da Yesu ya bar wajen, sai ya shiga yankin Taya da Sidon. 22  Sai ga wata mata ꞌyar Finikiya,* ta zo ta same shi tana kuka ta ce masa: “Ka ji tausayi na, ya Ubangiji, Ɗan Dauda. ꞌYata tana fama da aljani da ke ba ta wahala sosai.” 23  Amma bai ce mata kome ba. Sai almajiransa suka zo suka roƙe shi, suna cewa: “Ka sallame ta domin tana ta bin mu da kuka.” 24  Ya amsa ya ce: “Ba a aiko ni wurin kowa ba, sai wurin jamaꞌar Israꞌila da suke kamar tumakin da suka ɓata.” 25  Amma matar ta zo ta durƙusa a gabansa kuma ta ce: “Ubangiji, ka taimake ni!” 26  Sai ya amsa ya ce: “Ba zai dace a ɗauki abincin yara a ba yaran karnuka ba.” 27  Sai ta ce: “Gaskiya ne Ubangiji, amma yaran karnuka sukan ci burbuɗi da suke faɗowa daga teburin masu gida.” 28  Sai Yesu ya ce mata: “Uwargida, kina da bangaskiya sosai; bari ya faru miki yadda kika ba da gaskiya.” Nan take ꞌyarta ta warke. 29  Da Yesu ya bar wurin, ya zo kusa da Tekun Galili, bayan da ya hau kan tudu, sai ya zauna a wurin. 30  Sai jamaꞌa da yawa suka zo wurinsa, suka kawo masa guragu, da waɗanda suka rasa wani ɓangaren jikinsu,* da makafi, da bebaye da waɗansu da yawa, suka kwantar da su a gabansa, sai ya warkar da su. 31  Sai jamaꞌar suka yi mamaki sosai da suka ga bebaye suna magana, da yadda aka warkar da waɗanda suka rasa wani ɓangaren jikinsu, da yadda guragu suke tafiya, da yadda makafi suke gani kuma suka ɗaukaka Allah na Israꞌila. 32  Sai Yesu ya kira almajiransa yana cewa: “Ina jin tausayin jamaꞌar nan, domin sun riga sun yi kwana uku tare da ni kuma ba su ci kome ba. Ba na so in sallame su da yunwa,* domin za su iya suma a hanya.” 33  Amma almajiransa suka ce masa: “A ina ne za mu sami isasshen burodin da za mu ciyar da jamaꞌar nan a wannan wurin da babu kowa?” 34  Sai Yesu ya ce musu: “Burodi guda nawa ne kuke da su?” Suka ce masa: “Burodi guda bakwai da ƙananan kifaye kaɗan.” 35  Bayan da ya sa jamaꞌar su zauna a ƙasa, 36  sai ya ɗauki burodi bakwai ɗin da kifayen, bayan ya yi godiya, sai ya soma rarraba wa almajiransa, almajiran kuwa suka ba wa jamaꞌar. 37  Kuma dukansu suka ci, suka ƙoshi. Almajiran kuwa suka tattara abincin da ya rage, kuma ya cika manyan kwanduna bakwai. 38  Waɗanda suka ci abincin kuma, sun kai maza dubu huɗu, ban da mata da yara. 39  Bayan da ya sallami jamaꞌar sai ya shiga cikin jirgin ruwa kuma ya zo yankin Magadan.

Hasiya

Wato, wanke hannu irin na alꞌadar Yahudawa.
Ko kuma “ya yi baƙar magana ga.”
A yaren Girka, por·neiʹa. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Ko kuma “Kanꞌana.” Mazaunan Finikiya sun fito daga Kanꞌana.
Ko kuma “masu dungu.”
Ko kuma “azumi.”