Ta Hannun Matiyu 12:1-50

  • Yesu “Ubangiji ne na Assabaci” (1-8)

  • An warkar da mutumin da hannunsa ya shanye (9-14)

  • Ƙaunataccen bawan Allah (15-21)

  • Fitar da aljanu ta wurin ruhu mai tsarki (22-30)

  • Zunubin da ba a gafarta wa mutum (31, 32)

  • Gane itace ta wurin ꞌyaꞌyansa (33-37)

  • Alamar Yunana (38-42)

  • Saꞌad da ruhu mai ƙazanta ya dawo (43-45)

  • Mamar Yesu da kuma ꞌyanꞌuwansa (46-50)

12  A Ranar Assabaci, Yesu ya bi ta gonakin alkama. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara tsinka alkama suna ci. 2  Da Farisiyawa suka ga haka, sai suka ce masa: “Duba! Almajiranka suna yin abin da Doka* ta hana yi a Ranar Assabaci.” 3  Sai ya ce musu: “Shin ba ku karanta abin da Dauda ya yi saꞌad da shi da mutanen da ke tare da shi suke jin yunwa ba? 4  Yadda ya shiga gidan Allah, kuma suka ci burodin da ake miƙa wa Allah, wanda bai kamata shi da waɗanda suke tare da shi su ci ba, sai firistoci kaɗai? 5  Ko kuma ba ku karanta a cikin Doka cewa a Ranar Assabaci, firistoci suna yin aiki a haikali, duk da haka, ba su taka Doka ba? 6  Amma ina gaya muku, wanda ya fi haikali yana nan. 7  Da kun san abin da furucin nan yake nufi, ‘Jinƙai nake so ba hadaya ba,’ da ba ku ga laifin marasa laifi ba. 8  Domin Ɗan mutum Ubangiji ne na Assabaci.” 9  Bayan da ya bar wurin, sai ya shiga cikin majamiꞌarsu. 10  Akwai wani mutum a wurin da hannunsa ya shanye! Sai suka tambayi Yesu suka ce, “Ya dace ne a warkar da mutum a Ranar Assabaci?” Sun yi wannan tambayar ne domin su kama shi da laifi. 11  Sai ya ce musu: “Idan wani a cikinku yana da tunkiya, sai tunkiyar ta faɗa a cikin rami a Ranar Assabaci, shin akwai wani a cikinku da ba zai shiga ramin ya fitar da tunkiyar ba? 12  Ai, mutum ya fi tunkiya daraja sosai! Saboda haka, ya dace mutum ya yi aikin alheri a Ranar Assabaci.” 13  Sai Yesu ya ce wa mutumin: “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙa hannun, kuma hannun ya warke ya zama kamar ɗayan hannun. 14  Amma Farisiyawan suka fita kuma suka ƙulla yadda za su kashe shi. 15  Saꞌad da Yesu ya gane haka, sai ya bar wurin. Mutane da yawa suka bi shi, ya kuma warkar da dukansu, 16  amma ya ja musu kunne kada su gaya wa mutane ko wane ne shi, 17  domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya wanda ya ce: 18  “Ga bawana wanda na zaɓa, shi ne nake ƙauna, wanda yake sa ni farin ciki sosai! Zan ba shi ruhuna, kuma zai sa dukan mutane su san yadda za su yi abubuwan da suka dace. 19  Ba zai yi gardama ko ya ta da murya ba, kuma ba wanda zai ji muryarsa a kan manyan tituna. 20  Ba zai karya karan da ya kusan karyewa ba, ba zai kashe fitilar da ta kusan mutuwa ba, har sai ya tabbata cewa ya kawo adalci. 21  Hakika, alꞌummai za su sa rai gare shi.”* 22  Sai aka kawo masa wani mutum da ke da aljani, mutumin kuwa makaho ne kuma bebe ne, sai ya warkar da shi kuma mutumin ya soma magana da kuma gani. 23  Sai dukan mutanen suka yi mamaki kuma suka soma cewa: “Anya! Wannan ba Ɗan Dauda ba kuwa?” 24  Da Farisiyawa suka ji haka, sai suka ce: “Wannan mutumin ba ya fitar da aljanu sai dai da ikon Belzebub,* shugaban aljanu.” 25  Da yake Yesu ya san abin da suke tunani, sai ya ce musu: “Duk mulkin da mutanensa sun rabu kashi biyu kuma suna faɗa da juna zai hallaka, kuma duk birni ko gidan da mutanensa sun rabu kashi biyu kuma suna faɗa da juna ba zai tsaya ba. 26  Haka ma, idan Shaiɗan yana korin Shaiɗan, ya rabu kashi biyu ke nan. To, yaya mulkinsa zai tsaya? 27  Ƙari ga haka, idan ina fitar da aljanu da ikon Belzebub, da wane iko ne ꞌyaꞌyanku suke fitar da su? Shi ya sa su ne za su yi muku shariꞌa. 28  Amma idan da ruhun Allah ne nake fitar da aljanun, hakan na nufin cewa Mulkin Allah ya zo kuma ba ku sani ba. 29  Ko kuma, ta yaya mutum zai iya shiga gidan wani mutum mai ƙarfi ya kwashe kayansa? Ai, sai dai ya ɗaure mutumin tukuna, ta haka ne zai iya kwashe kayan gidansa. 30  Duk wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni, kuma duk wanda ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi. 31  “Saboda haka, ina gaya muku cewa, za a gafarta wa mutane kowane irin zunubi ko maganar saɓo da suka yi, amma duk wanda ya yi maganar saɓo game da ruhu mai tsarki, ba za a gafarta masa ba. 32  Alal misali, duk wanda ya yi wa Ɗan mutum baƙar magana, za a gafarta masa. Amma duk wanda ya yi baƙar magana game da ruhu mai tsarki, ba za a gafarta masa ba ko a zamanin nan ne, ko kuma a zamani mai zuwa. 33  “Idan kun sa itace ya yi kyau, zai ba da ꞌyaꞌya masu kyau. Idan kun sa itace ya lalace, zai ba da ꞌyaꞌya marasa kyau. Ana gane itace mai kyau ta wurin ꞌyaꞌyansa. 34  ꞌYaꞌyan macizai masu dafi, ta yaya za ku faɗi abubuwa masu kyau, da yake ku mugaye ne? Ai, abin da ya cika zuciya, shi yake fitowa a baki. 35  Mutumin kirki yakan fitar da abubuwa masu kyau daga ajiyarsa na kirki, amma mugun mutum yakan fitar da mugayen abubuwa daga ajiyarsa na mugunta. 36  Ina gaya muku, a Ranar Shariꞌa mutane za su ba da lissafin abubuwa marasa kyau da suka faɗa, 37  domin abubuwan da kuka faɗa ne za su sa Allah ya ɗauke ku a matsayin masu adalci ko kuma ya hukunta ku.” 38  Sai wasu marubuta da Farisiyawa suka amsa masa suka ce: “Malam, muna so ka nuna mana wata alama mu gani.” 39  Sai Yesu ya amsa ya ce musu: “Mutanen zamanin nan mugaye ne kuma marasa aminci, sun ci-gaba da neman a nuna musu alama, amma ba za a nuna musu alama ba, sai dai alamar annabi Yunana. 40  Kamar yadda Yunana ya yi kwanaki uku dare da rana a cikin babban kifi, haka ma Ɗan mutum zai yi kwanaki uku dare da rana a cikin kabari. 41  A ranar shariꞌa, mutanen Nineba za su tashi tare da mutanen zamanin nan, su nuna wa mutanen zamanin nan cewa ba su yi daidai ba, domin su sun tuba saboda waꞌazin Yunana. Ga shi kuwa wanda ya fi Yunana yana nan. 42  A ranar shariꞌa, sarauniyar kudu* za ta tashi tare da mutanen zamanin nan, ta nuna wa mutanen zamanin nan cewa ba su yi daidai ba. Domin ta fito daga wuri mai nisa sosai ta ji koyarwar Sulemanu. Ga shi kuwa wanda ya fi Sulemanu yana nan. 43  “Saꞌad da ruhu mai ƙazanta ya fito daga jikin mutum, yakan yi ta yawo a wuraren da babu ruwa domin ya sami wurin hutawa, kuma idan bai samu ba, 44  sai ya ce, ‘Zan koma gidana na dā inda na fito.’ Idan ya isa gidan, sai ya ga ba kowa, an share shi da kyau kuma an yi masa ado. 45  Sai ya koma ya kwaso waɗansu ruhohi masu ƙazanta guda bakwai, waɗanda suka fi shi mugunta. Bayan da suka shiga ciki sai suka zauna a wurin. A ƙarshe, yanayin mutumin zai yi muni sosai fiye da dā. Haka ma zai faru da wannan mugun zamanin.” 46  Saꞌad da yake kan magana da jamaꞌar, mamarsa da ꞌyanꞌuwansa suna tsaye a waje kuma suna so su yi magana da shi. 47  Sai wani ya ce masa: “Ga mamarka da ꞌyanꞌuwanka suna tsaye a waje kuma suna so su yi magana da kai.” 48  Sai ya ce wa mutumin nan da ya yi masa magana: “Wace ce mamata, kuma su wane ne ꞌyanꞌuwana?” 49  Sai ya nuna almajiransa da hannunsa, ya ce: “Ga mamata da kuma ꞌyanꞌuwana a nan! 50  Domin duk wanda ya yi nufin Ubana wanda yake sama, shi ne ɗanꞌuwana, da ꞌyarꞌuwata, da kuma mamata.”

Hasiya

Ko kuma “Dokar Musa.”
A yaren Girka, “a cikin sunansa.”
Sunan da ake kiran Shaiɗan.
Wato, Sarauniya Sheba.