Ta Hannun Matiyu 10:1-42
10 Sai Yesu ya kira almajiransa goma sha biyu kuma ya ba su iko a kan ruhohi masu ƙazanta don su iya fitar da su, kuma su iya warkar da kowane irin cuta da kowane irin rashin lafiya.
2 Ga sunayen manzanninsa goma sha biyun: Na farko Siman, wanda ake ce da shi Bitrus, da ɗanꞌuwansa Andarawus, da Yaƙub ɗan Zabadi da ɗanꞌuwansa Yohanna,
3 da Filibus, da Batalomi, da Tomas, da Matiyu mai karɓan haraji, da Yaƙub ɗan Alfiyus, da Taddiyus,
4 da Siman Mai Ƙwazo,* da kuma Yahuda Iskariyoti, wanda ya ci amanar Yesu daga baya.
5 Waɗannan manzanni goma sha biyu ne Yesu ya aika, kuma ya ba su waɗannan umurnai: “Kada ku bi hanyar mutanen alꞌummai kuma kada ku shiga garin Samariyawa;
6 sai dai ku ci-gaba da zuwa gidajen waɗanda suke kamar tumakin da suka ɓata a Israꞌila.
7 Yayin da kuke tafiya, ku yi waꞌazi kuna cewa: ‘Mulkin sama ya yi kusa.’
8 Ku warkar da marasa lafiya, ku ta da matattu, ku warkar da kutare, ku fitar da aljanu. Kyauta aka ba ku, ku kuma bayar kyauta.
9 Kada ku saka zinariya ko azurfa ko tagulla a jakar kuɗinku.
10 Kada kuma ku ɗauki jakar abinci ko riga biyu ko takalma ko sanda domin tafiyarku, ai, maꞌaikaci ya cancanci ya sami abinci.
11 “A duk gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mutumin da ya cancanci ziyarar da kuka kai, kuma ku zauna a wurin har sai lokacin da za ku tashi.
12 Saꞌad da kuka shiga gidan, ku ce, ‘salama a gare ku.’
13 Idan mutanen gidan sun cancanci ziyararku, bari su sami salamar da kuka yi musu fatan ta. Amma idan ba su cancanci ziyararku ba, bari fatan salama da kuka yi musu ta komo kanku.
14 A duk inda wani ya ƙi karɓan ku, ko ya ƙi saurarar saƙonku, yayin da kuke barin gidan ko kuma garin, ku kakkaɓe ƙurar da ke ƙafafunku.
15 A gaskiya ina gaya muku, a Ranar Shariꞌa zai yi wa ƙasar Sodom da Gomora sauƙi su jimre fiye da garin.
16 “Ga shi kuwa, ina aikan ku kamar tumaki a tsakanin ƙyarketai.* Saboda haka, ku nuna cewa ku masu wayo ne kamar macizai, marasa ɓarna kuma kamar kurciyoyi.
17 Ku yi hankali da mutane, domin za su kai ku kotuna kuma za su yi muku bulala a majamiꞌunsu.
18 Za a kai ku gaban gwamnoni da sarakuna saboda ni, don ku gaya musu da kuma alꞌummai abin da kuka yi imani da shi.
19 Amma, saꞌad da aka kai ku gabansu, kada ku damu a kan abin da za ku faɗa ko yadda za ku faɗe shi, Allah zai gaya muku abin da za ku faɗa a lokacin;
20 domin ba ku ne kawai kuke magana ba, amma ruhun Ubanku ne yake magana ta wurinku.
21 Ƙari ga haka, ɗanꞌuwa zai ba da ɗanꞌuwansa a kashe shi, uba kuma zai ba da ɗansa, yara kuma za su yi wa iyayensu tawaye kuma hakan zai kai ga mutuwar iyayen.
22 Kuma dukan mutane za su tsane ku saboda sunana, amma duk wanda ya jimre har zuwa ƙarshe za a cece shi.
23 Idan sun tsananta muku a wannan gari, ku gudu zuwa wani gari; a gaskiya ina gaya muku kafin ku gama zagaya dukan garuruwan Israꞌila, Ɗan mutum zai dawo.
24 “Babu ɗalibin da ya fi malaminsa, ko kuma bawa da ya fi maigidansa.
25 Idan ɗalibin ya zama kamar malaminsa, kuma bawan kamar maigidansa, hakan ma ya isa. Idan mutane sun kira maigida Belzebub,* to me za su kira mutanen gidansa?
26 Saboda haka, kada ku ji tsoron su, don babu abin da aka rufe da ba za a buɗe ba kuma babu asirin da ba za a tona ba.
27 Abin da na gaya muku a duhu, ku faɗe shi a cikin haske, abin da na gaya muku a kunne, ku yi shelarsa daga saman gidaje.
28 Kuma kada ku ji tsoron waɗanda za su kashe jiki, amma ba za su iya kashe rai* ba. A maimakon haka, ku ji tsoron wanda zai iya hallaka rai da jiki a Gehenna.*
29 Ana sayan ƙananan tsuntsaye* guda biyu da tsabar kuɗi ɗaya da ba shi da daraja, ko ba haka ba? Duk da haka, babu ɗayansu wanda zai faɗi a ƙasa ba tare da sanin Ubanku ba.
30 Ai, ko gashin kanku ma ya san adadinsu.
31 Saboda haka, kada ku ji tsoro; kuna da daraja fiye da ƙananan tsuntsaye da yawa.
32 “Duk wanda ya faɗa a gaban mutane cewa ya san ni, ni ma zan faɗa a gaban Ubana da ke sama cewa na san shi.
33 Amma duk wanda ya yi mūsun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi mūsun sanin sa a gaban Ubana da ke sama.
34 Kada ku yi tsammani na zo ne domin in kawo salama a duniya; ban zo domin in kawo salama ba, sai dai takobi.
35 Na zo ne don in raba kan iyali, ɗa zai yi gāba da babansa, ꞌya za ta yi gāba da mamarta, matar ɗa kuma za ta yi gāba da mamar mijinta.
36 Hakika, mutanen gidan mutum ne za su zama abokan gābansa.
37 Duk wanda yake ƙaunar babansa ko mamarsa fiye da ni, bai isa ya zama almajirina ba; kuma duk wanda yake ƙaunar ɗansa ko ꞌyarsa fiye da ni, bai isa ya zama almajirina ba.
38 Kuma duk wanda bai ɗauki gungumen azabarsa* ya bi ni ba, bai isa ya zama almajirina ba.
39 Duk wanda ya yi ƙoƙarin kāre ransa zai rasa shi, kuma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, zai sake rayuwa.
40 “Duk wanda ya karɓe ku, ya karɓe ni, kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi Wanda ya aiko ni ma.
41 Duk wanda ya karɓi annabi saboda shi annabi ne, zai sami ladan annabi, duk wanda ya karɓi mai adalci saboda shi mai adalci ne, zai sami ladan mai adalci.
42 Kuma duk wanda ya ba wa ɗaya daga cikin mafi ƙanƙantan nan ko da kofi ɗaya ne na ruwan sanyi saboda shi almajirina ne, a gaskiya ina gaya muku cewa, ba zai taɓa rasa ladansa ba.”
Hasiya
^ Wasu juyin Littafi Mai Tsarki sun ce, “mutumin Kanꞌana.” Amma a asalin yaren da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, da alama kalmar na nufin “mai ƙwazo.”
^ Wata dabbar daji da take kama da kare.
^ Sunan da ake kiran Shaiɗan wanda shi ne yarima, ko kuma sarkin aljanu.
^ Ko kuma “begen yin rayuwa a nan gaba.”
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ko kuma “gwara.”
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.