Ta Hannun Markus 7:1-37

  • Yesu ya fallasa alꞌadun ꞌyanꞌadam (1-13)

  • Abin da ke ƙazantar da mutum daga zuciya ne (14-23)

  • Bangaskiyar ꞌYar Finikiya da ke ƙasar Siriya (24-30)

  • Yesu ya warkar da wani kurma (31-37)

7  Sai Farisiyawa da wasu marubuta da suka zo daga Urushalima suka taru kusa da shi. 2  Kuma suka ga wasu almajiransa suna cin abinci da hannaye marasa tsabta, wato, ba su wanke hannayensu ba.* 3  (Domin Farisiyawa da dukan Yahudawa ba sa cin abinci ba tare da sun wanke hannunsu har zuwa gwiwar hannu ba. Suna yin hakan ne bisa ga alꞌadar kakanninsu. 4  Kuma idan suka dawo daga kasuwa, ba sa cin abinci sai sun yi wanka. Akwai kuma wasu alꞌadu da yawa da suka gāda kuma suka manne musu, kamar na nitsar da* kofi, da tuluna, da kuma kwanukan tagulla cikin ruwa.) 5  Sai Farisiyawan da marubutan suka tambaye shi suka ce: “Me ya sa almajiranka ba sa bin alꞌadun kakanninmu, kuma suna cin abinci da hannaye marasa tsabta?” 6  Sai ya ce musu: “Ya dace da Ishaya ya yi annabci a kanku munafukai, kamar yadda ya rubuta, ‘Mutanen nan fa, da baki kawai suke girmama ni, amma zukatansu ba sa tare da ni. 7  A banza ne suke bauta mini, domin suna koyar da dokokin mutane a matsayin kalmar Allah.’ 8  Kun bar dokokin Allah, amma kun manne wa alꞌadun mutane.” 9  Ƙari ga haka, ya ce musu: “Kuna ƙin bin dokokin Allah da wayo don ku bi alꞌadunku. 10  Alal misali, Musa ya ce, ‘Ka girmama babanka da mamarka,’ kuma ‘A kashe duk wanda ya zagi* babansa ko mamarsa.’ 11  Amma kukan ce, ‘Idan wani ya ce wa babansa ko mamarsa: “Duk abin da nake da shi da zai amfane ku, kyauta* ne da na keɓe wa Allah.”’ 12  Ba kwa barin sa ya yi wani abu ga babansa ko mamarsa. 13  Saboda haka, kun mai da kalmar Allah banza saboda alꞌadunku da kuke koya wa mutane. Kuma kuna yin abubuwa da yawa kamar haka.” 14  Sai ya sake kiran jamaꞌar, kuma ya ce musu: “Ku saurare ni dukanku, don ku gane abin da nake faɗa. 15  Ba abin da ke shiga jikin mutum ne yake ƙazantar da shi a gaban Allah ba; amma abin da ke fita daga jikinsa ne yake ƙazantar da shi a gaban Allah.” 16 * —— 17  Da ya bar jamaꞌar kuma ya shiga cikin wani gida, sai almajiransa suka soma yi masa tambaya game da misalin. 18  Sai ya ce musu: “Ku ma ba ku fahimta ba? Ba ku san cewa babu abin da ke shiga jikin mutum da zai ƙazantar da shi a gaban Allah ba? 19  Da yake ya shiga cikinsa ne ba zuciyarsa ba, kuma daga cikinsa zai wuce zuwa bayan gida.” Ta haka ya faɗa cewa dukan abinci yana da tsabta. 20  Ƙari ga haka, ya ce musu: “Abin da ke fitowa daga jikin mutum ne yake ƙazantar da shi a gaban Allah. 21  Domin daga zuciya ne mugayen tunani suke fitowa, kamar su: lalata,* da sata, da kisa, 22  da zina, da haɗama, da ayyukan mugunta, da yaudara, da halin rashin kunya,* da kishi, da saɓo, da girman kai, da kuma rashin tunani. 23  Daga jikin mutum ne mugayen abubuwan nan suke fitowa kuma su ne suke ƙazantar da mutum a gaban Allah.” 24  Ya tashi daga wurin kuma ya shiga yankin Taya da Sidon. Sai ya shiga wani gida kuma ba ya so kowa ya san haka, duk da haka mutane sun gan shi. 25  Nan da nan, wata mata da ƙaramar ꞌyarta ke da ruhu mai ƙazanta ta ji game da shi, sai ta zo ta faɗi a gabansa. 26  Ita ꞌYar Girka ce, amma an haife ta a Finikiya da ke ƙasar Siriya. Sai ta yi ta roƙan Yesu ya fitar da aljani da ke jikin ꞌyarta. 27  Amma ya ce mata: “Bari yaran su ƙoshi tukuna, domin ba zai dace a ɗauki abincin yara a ba yaran karnuka ba.” 28  Sai ta amsa masa ta ce: “Gaskiya ne, Ubangiji, ko yaran karnukan ma da ke ƙarƙashin teburi suna cin burbuɗi da ke faɗowa daga abincin yara.” 29  Sai Yesu ya ce mata: “Saboda abin da kika faɗa, ki tafi gida; aljanin ya rabu da ꞌyarki.” 30  Sai ta koma gida ta sami ꞌyarta a kwance a kan gado. Aljanin kuwa ya rabu da ita. 31  Da Yesu ya dawo daga yankin Taya, sai ya bi ta Sidon zuwa tekun Galili, kuma ya bi ta yankin Dikafolis.* 32  A wurin, sai aka kawo masa wani kurma da ba ya iya yin magana sosai, kuma suka roƙe shi ya sa hannunsa a kan mutumin. 33  Sai Yesu ya ja mutumin gefe, inda babu kowa. Ya sa yatsunsa a kunnuwan mutumin, kuma bayan ya tofa miyau, sai ya taɓa harshen mutumin. 34  Yesu ya kalli sama, kuma ya yi baƙin ciki sosai, sai ya ce wa mutumin: “Effata,” wato, “Ka buɗu.” 35  Da hakan, sai kunnuwansa sun buɗu kuma ya soma magana da kyau. 36  Yesu ya ja musu kunne kada su gaya ma kowa. Amma da Yesu yana gaya musu haka, su kuma suna ƙara yaɗa labarin. 37  Mutanen sun cika da mamaki kuma suka ce: “Ya yi kome da kyau. Har ma ya sa kurame suna ji, bebaye kuma suna magana.”

Hasiya

Wato, wanke hannu irin na alꞌadar Yahudawa.
A yaren Girka, “baftisma.”
Ko kuma “yi baƙar magana ga.”
A yaren Girka, ana kiran irin wannan kyautar, Koban.
Wannan ayar tana cikin wasu juyin Littafi Mai Tsarki, amma ayar ba ta cikin asalin rubuce-rubucen da aka yi a yaren Girka. Don haka, da alama ba ta cikin Kalmar Allah.
A yaren Girka, por·neiʹa. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Ko kuma “Yanki Mai Birane 10.”