Ta Hannun Markus 3:1-35
3 Ya sake shiga wata majamiꞌa, kuma ya ga wani mutum a wurin da hannunsa ya shanye.
2 Sai suka soma kallon sa don su ga ko zai warkar da mutumin a Ranar Assabaci, don su zarge shi.
3 Sai ya ce wa mutumin da hannunsa ya shanye: “Ka tashi, ka zo tsakiya.”
4 Sai Yesu ya ce musu: “Ya dace a yi alheri ko kuma mugunta a Ranar Assabaci? A ceci rai ko kuma a yi kisa?” Amma sun yi shuru.
5 Bayan da Yesu ya kalli dukansu cikin fushi, yana kuma baƙin ciki sosai domin taurin zuciyarsu, sai ya ce wa mutumin: “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙa hannun, kuma hannun ya warke.
6 Sai Farisiyawa suka fita, kuma nan da nan suka haɗu da rukunin mutanen da ke goyon bayan Hirudus,* kuma suka soma ƙulle-ƙulle a kan Yesu domin su kashe shi.
7 Sai Yesu da almajiransa suka bar wurin zuwa teku, kuma mutane da yawa daga Galili da kuma Yahudiya sun bi shi.
8 Har ma mutane da yawa daga Urushalima, da Idumiya, da kuma ƙetaren Kogin Jodan, da yankin Taya da Sidon sun zo wurinsa saꞌad da suka ji abubuwa da yawa da yake yi.
9 Sai ya gaya wa almajiransa su shirya masa ƙaramin jirgin ruwa ya shiga don kada jamaꞌar su matse shi.
10 Domin ya warkar da mutane da yawa, dukan waɗanda suke da cututtuka masu tsanani suna ta zuwa kusa da inda yake domin su taɓa shi.
11 Har da ruhohi masu ƙazanta ma, a duk lokacin da suka gan shi, sai su faɗi a gabansa suna ihu cewa: “Kai ne Ɗan Allah.”
12 Amma sau da yawa, yakan ja musu kunne kada su gaya wa mutane ko wane ne shi.
13 Sai Yesu ya hau tudu ya kira waɗanda yake so, kuma suka zo wurinsa.
14 Sai ya zaɓi* almajirai goma sha biyu, waɗanda ya kira su manzanni, su ne waɗanda za su riƙa bin sa, kuma su ne waɗanda zai aika zuwa waꞌazi,
15 su ne zai ba wa ikon fitar da aljanu.
16 Kuma waɗannan manzanni goma sha biyu da ya zaɓa* su ne Siman, wanda kuma ya ba wa suna Bitrus,
17 da Yaƙub ɗan Zabadi, da Yohanna ɗanꞌuwan Yaƙub (ya kuma ba su suna Buwarnajis, wanda yake nufin “ꞌYaꞌyan Tsawa”),
18 da Andarawus, da Filibus, da Bartalomi, da Matiyu, da Toma, da Yaƙub ɗan Alfiyus, da Taddiyus, da Siman Mai Ƙwazo,*
19 da kuma Yahuda Iskariyoti, wanda ya ci amanar Yesu daga baya.
Sai ya shiga wani gida.
20 Jamaꞌa suka sake taruwa, hakan ya sa ba su ma iya cin abinci ba.
21 Saꞌad da ꞌyanꞌuwansa suka ji game da hakan, sai suka zo su kama shi domin suna cewa: “Ai ya haukace.”
22 Ƙari ga haka, marubuta da suka zo daga Urushalima suna cewa: “Yana da Belzebub,* kuma da ikon shugaban aljanu ne yake fitar da aljanu.”
23 Bayan ya kira su, sai ya yi musu magana da misalai, ya ce: “Ta yaya Shaiɗan zai fitar da Shaiɗan?
24 Idan mulki ya rabu kashi biyu kuma babu haɗin kai, ba zai tsaya ba;
25 idan gida ya rabu kashi biyu kuma babu haɗin kai, gidan ba zai tsaya ba.
26 Haka ma, idan Shaiɗan ya tayar ma kansa, kuma ya rabu kashi biyu, ba zai tsaya ba amma zai hallaka.
27 Hakika, babu wanda zai iya shiga gidan wani mutum mai ƙarfi ya saci kayansa, sai dai ya ɗaure mutumin tukuna. Ta haka ne zai iya kwashe kayan gidansa.
28 A gaskiya ina gaya muku, za a gafarta wa mutane ko da mene ne suka yi, ko da wane irin zunubai da kuma maganar saɓo ne suka yi.
29 Amma duk wanda ya yi maganar saɓo game da ruhu mai tsarki, ba za a gafarta masa ba har abada. Yana da alhakin zunubi har abada.”
30 Ya faɗi hakan ne domin suna cewa: “Yana da ruhu mai ƙazanta.”
31 Sai mamarsa da ꞌyanꞌuwansa suka zo, suka tsaya a waje, kuma suka aiki wani ya kira shi.
32 Sai jamaꞌar da suke zaune kewaye da shi suka ce masa: “Ga mamarka da ꞌyanꞌuwanka a waje suna so su yi magana da kai.”
33 Sai ya amsa musu ya ce: “Wace ce mamata da kuma ꞌyanꞌuwana?”
34 Sai ya kalli waɗanda suke zaune kewaye da shi kuma ya ce: “Ga mamata da kuma ꞌyanꞌuwana!
35 Duk wanda ya yi nufin Allah, shi ne ɗanꞌuwana, da ꞌyarꞌuwata, da kuma mamata.”
Hasiya
^ Wannan shi ne Hirudus mai suna Antifas. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ko kuma “naɗa.”
^ Ko kuma “naɗa.”
^ Wasu juyin Littafi Mai Tsarki sun ce, “mutumin Kanꞌana.” Amma a asalin yaren da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, da alama kalmar na nufin “mai ƙwazo.”
^ Sunan da ake kiran Shaiɗan. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.