Ta Hannun Markus 16:1-8
-
An ta da Yesu (1-8)
16 Bayan Ranar Assabaci, Maryamu Magdalin, da Maryamu mamar Yaƙub, da Salomi sun sayo kayan ƙamshi don su shafa wa jikin Yesu.
2 Da sassafe a ranar farko ta mako, da fitowar rana, sai suka zo kabarin.*
3 Suna ce wa juna: “Wane ne zai tura mana dutsen da aka rufe kabarin da shi?”
4 Amma da suka ɗaga idanu, sai suka ga cewa an riga an ture dutsen, duk da cewa yana da girma sosai.
5 Da suka shiga kabarin, sai suka ga wani saurayi yana zaune a hannun dama, sanye da farin riga, kuma suka yi mamaki sosai.
6 Sai ya ce musu: “Kada ku yi mamaki. Kuna neman Yesu mutumin Nazaret wanda aka kashe a kan gungume. An tashe shi. Kuma ba ya nan. Ga wurin da suka kwantar da shi dā ma.
7 Ku je ku gaya wa almajiransa da kuma Bitrus cewa, ‘Za shi Galili ya jira ku. Za ku gan shi a wurin, kamar yadda ya riga ya gaya muku.’”
8 Da suka fita daga kabarin, sai suka soma guduwa, suna rawar jiki kuma cike da mamaki. Ba su faɗa ma kowa wani abu ba domin suna jin tsoro.*
Hasiya
^ Ko kuma “kabarin tunasarwan.”
^ Rubuce-rubucen farko da aka yi a yaren Girka da mutane suka yarda da su, sun nuna cewa labari mai daɗi da Markus ya rubuta ya ƙare da kalmomin da ke aya ta 8. Ka duba sashen Wasu Bayanai na A3.

