Ta Hannun Markus 14:1-72
-
Firistoci sun ƙulla su kashe Yesu (1, 2)
-
An zuba wa Yesu mān ƙamshi (3-9)
-
Yahuda ya ci amanar Yesu (10, 11)
-
Bikin Ƙetarewa na ƙarshe (12-21)
-
Yesu ya kafa Abincin Yamma na Ubangiji (22-26)
-
Yesu ya ce Bitrus zai yi mūsun sanin sa (27-31)
-
Yesu ya yi adduꞌa a Getsemani (32-42)
-
An kama Yesu (43-52)
-
An yi masa shariꞌa a gaban membobin Sanhedrin (53-65)
-
Bitrus ya yi mūsun sanin Yesu (66-72)
14 Saura kwana biyu a yi Bikin Ƙetarewa da kuma Bikin Burodi Marar Yisti. Kuma manyan firistoci da marubuta suna neman yadda za su kama Yesu da wayo kuma su kashe shi.
2 Amma suna cewa: “Kada mu kama shi a lokacin bikin, domin wataƙila mutane za su ta da hayaniya.”
3 Saꞌad da Yesu yake Betani yana cin abinci a gidan Siman, wanda a dā kuturu ne, sai wata mata ta zo da kwalba,* ɗauke da mān ƙamshi mai tsada sosai, wanda aka yi da nad* zalla. Ta buɗe kwalbar, kuma ta soma zuba mān a kan Yesu.
4 Da wasu suka ga haka, sai suka yi fushi kuma suka soma ce wa junansu: “Me ya sa aka yi ɓarna da mān ƙamshin nan haka?
5 Ai, da za a iya sayar da mān nan fiye da dinari* ɗari uku, a ba wa talakawa kuɗin!” Kuma sun yi fushi sosai* don abin da ta yi.
6 Amma Yesu ya ce: “Ku bar ta mana. Me ya sa kuke damun ta? Abu mai kyau ne ta yi mini.
7 Domin a kullum kuna tare da talakawa, kuma za ku iya yi musu alheri a duk lokacin da kuke so, amma ni ba zan kasance da ku kullum ba.
8 Ta yi abin da za ta iya yi; ta zuba mān ƙamshin nan a jikina don ta shirya jikina kafin a binne ni.
9 A gaskiya ina gaya muku, a duk inda za a yi shelar labari mai daɗi a dukan duniya, za a riƙa faɗin abin da matar nan ta yi don tunawa da ita.”
10 Sai Yahuda Iskariyoti, ɗaya daga cikin almajiransa goma sha biyu, ya je wurin manyan firistoci don ya ci amanar Yesu ta wurin ba da shi ga manyan firistocin.
11 Da suka ji hakan, sun yi farin ciki sosai kuma sun yi alkawarin ba shi kuɗin azurfa. Sai ya soma neman damar da zai ci amanar Yesu.
12 A ranar farko ta Bikin Burodi Marar Yisti, wato ranar da akan miƙa hadaya ta Bikin Ƙetarewa, sai almajiran Yesu suka ce masa: “Ina kake so mu je mu shirya maka ka ci abincin Bikin Ƙetarewa?”
13 Sai ya aika almajiransa biyu kuma ya ce musu: “Ku shiga cikin gari, wani mutum da ke ɗauke da tulun ruwa zai same ku. Ku bi shi.
14 Kuma duk gidan da ya shiga, ku ce wa maigidan, ‘Malam ya ce: “Ina ɗakin da zan ci abincin Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina?”’
15 Zai nuna muku wani babban ɗaki da ke saman gidan, wanda aka gyara kuma yana nan a shirye. A wurin ne za ku shirya mana bikin.”
16 Sai almajiran suka tafi, suka shiga cikin gari, kuma suka sami abubuwa yadda Yesu ya gaya musu. Suka kuma shirya Bikin Ƙetarewan.
17 Da yamma ta yi, sai ya zo tare da almajiransa goma sha biyu.
18 Yayin da suka zauna suna cin abinci a teburi, Yesu ya ce: “A gaskiya ina gaya muku, ɗaya daga cikinku wanda yake cin abinci tare da ni, zai ci amanata.”
19 Sai almajiran suka damu kuma suka soma tambayar sa ɗaya bayan ɗaya cewa: “Ni ne?”
20 Ya ce musu: “Ɗaya daga cikinku goma sha biyu ne, wanda yake cin abinci tare da ni a kwano ɗaya.
21 Ɗan mutum zai mutu kamar yadda aka rubuta game da shi, amma kaiton wanda ta wurin shi ne za a ci amanar Ɗan mutum, zai fi wa mutumin nan da ma ba a haife shi ba.”
22 Yayin da suka ci-gaba da cin abinci, sai ya ɗauki burodi, bayan ya yi godiya ga Allah, ya kakkarya, ya kuma ba su yana cewa: “Ku karɓa; wannan yana wakiltar jikina.”
23 Ya kuma ɗauki kofi, ya yi godiya, sai ya ba su, kuma dukansu sun sha daga ciki.
24 Sai ya ce musu: “Wannan yana wakiltar ‘jinina na alkawari,’ wanda za a zubar a madadin mutane da yawa.
25 A gaskiya ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai dai a ranar da zan sake shan wani sabo a Mulkin Allah.”
26 A ƙarshe, bayan da suka rera waƙoƙin yabo, sai suka fita suka tafi Tudun Zaitun.
27 Sai Yesu ya ce musu: “Dukanku za ku yi tuntuɓe, domin a rubuce yake cewa: ‘Zan bugi makiyayin, kuma tumakin za su watse.’
28 Amma bayan da aka ta da ni daga mutuwa, zan je Galili in jira ku.”
29 Sai Bitrus ya ce masa: “Ko sauran sun yi tuntuɓe, ni kam ba zan yi tuntuɓe ba.”
30 Da jin haka, sai Yesu ya ce masa: “A gaskiya ina gaya maka, a yau ɗin nan, da daren nan ma, kafin zakara ya yi cara sau biyu, za ka yi mūsun sani na sau uku.”
31 Amma Bitrus ya ci-gaba da cewa: “Ko da zan mutu tare da kai ne, ba zan taɓa yin mūsun sanin ka ba.” Sauran almajiran Yesu ma sun soma faɗin hakan.
32 Sai suka kai wani wurin da ake kira Getsemani, kuma Yesu ya ce wa almajiransa: “Ku zauna a nan bari in je in yi adduꞌa.”
33 Ya tafi da Bitrus, da Yaƙub, da Yohanna, sai ya soma damuwa sosai kuma ya soma matuƙar baƙin ciki.
34 Sai ya ce musu: “Damuwar da take raina, za ta iya kashe ni. Ku zauna a nan kuma ku ci-gaba da yin tsaro.”
35 Da ya je gaba kaɗan, sai ya faɗi a ƙasa, kuma ya soma adduꞌa yana cewa idan zai yiwu, a ɗauke masa wannan lokacin wahala.
36 Sai ya ce: “Abba,* Uba, duk abu mai yiwuwa ne a wurinka; ka ɗauke mini wannan kofi. Duk da haka, bari abin da kake so ya faru, ba abin da nake so ba.”
37 Da ya dawo wurin almajiransa, sai ya same su suna barci, sai ya ce wa Bitrus: “Siman kana barci? Ba za ka iya yin tsaro na awa ɗaya ba?
38 Ku ci-gaba da yin tsaro da adduꞌa, domin kada ku faɗi cikin jarraba. A gaskiya, zuciyar tana da niyya sosai, amma jikin ba ƙarfi.”
39 Ya sake komawa ya yi adduꞌa, kuma ya maimaita abin da ya faɗa da farko.
40 Ya sake dawowa, ya same su suna barci, domin idanunsu sun yi nauyi sosai, sun ma rasa amsar da za su ba shi.
41 Sai ya sake dawo wurinsu a karo na uku kuma ya ce musu: “A lokaci kamar haka kuna barci kuna hutawa! Ya isa! Ga shi! Lokaci ya yi da za a ci amanar Ɗan mutum kuma a ba da shi a hannun masu zunubi.
42 Ku tashi, mu tafi. Don mai cin amanata ya yi kusa.”
43 Yayin da yake kan magana, nan da nan, sai ga Yahuda, ɗaya daga cikin almajiransa goma sha biyu, ya zo tare da jamaꞌa riƙe da takubba da sanduna. Manyan firistoci da marubuta da dattawa ne suka turo su.
44 Wanda zai ci amanarsa ya riga ya ba su alama cewa: “Duk wanda na sumbace shi, shi ne mutumin; ku kama shi, ku tafi da shi, kuma kada ku yarda ya gudu.”
45 Sai Yahuda ya je wurin Yesu kai tsaye, ya ce masa, “Malam!”* kuma ya sumbace shi.
46 Sai suka kama shi, kuma suka riƙe shi.
47 Amma ɗaya daga cikin waɗanda suke tsaye a wurin ya zare takobinsa, ya sari bawan babban firist kuma ya yanke masa kunne.
48 Amma Yesu ya ce musu: “Shin kun fito ne ku kama ni da takubba da sanduna, sai ka ce ɗan fashi?
49 A kullum, ina tare da ku a haikali ina koyarwa, amma ba ku kama ni ba. Duk da haka, abubuwan nan sun faru ne don a cika Nassosi.”
50 Sai dukan almajiran suka bar shi suka gudu.
51 Amma akwai wani matashi da ya saka mayafin lilin kawai a jikinsa, ya soma bin Yesu a baya, kuma sun yi ƙoƙarin kama shi,
52 Sai ya bar mayafinsa a hannunsu, ya gudu tsirara.*
53 Sun kai Yesu wurin babban firist, sai dukan manyan firistoci da dattawa da marubuta suka taru.
54 Amma Bitrus ya ci-gaba da bin shi daga nesa, har zuwa farfajiyar gidan babban firist. Ya zauna tare da masu hidima a gidan yana jin ɗumin wuta.
55 Manyan firistoci da dukan membobin Sanhedrin* suna neman waɗanda za su ba da shaida a kan Yesu da zai ba su damar kashe shi, amma ba su samu ko ɗaya ba.
56 Duk da cewa mutane da yawa sun ba da shaidar ƙarya a kansa, amma shaidar da suka bayar ba ta jitu ba.
57 Ƙari ga haka, wasu kuma suna tashiwa suna ba da shaidar ƙarya a kansa suna cewa:
58 “Mun ji shi yana cewa, ‘Zan rusar da haikalin nan da aka gina da hannu, kuma a cikin kwana uku zan gina wanda ba a yi da hannu ba.’”
59 Amma duk da haka, shaidar da suka bayar ba ta jitu ba.
60 Sai babban firist ya tashi a tsakaninsu, ya tambaye Yesu ya ce: “Ba za ka ce kome ba? Ba ka ji abin da mutanen nan suke faɗa a kanka ba?”
61 Amma Yesu ya yi shuru, bai ce kome ba. Sai babban firist ya sake soma tambayar sa, ya ce masa: “Kai ne Kristi Ɗan Mai Albarka?”
62 Sai Yesu ya ce: “Ni ne; kuma za ku ga Ɗan mutum yana zaune a hannun dama mai iko kuma yana zuwa a cikin gajimaren sama.”
63 Da jin haka, sai babban firist ya yage mayafinsa ya ce: “Wace shaida kuma muke bukata?
64 Kun dai ji saɓon. To, mene ne raꞌayinku?” Sai dukansu suka yanke hukunci cewa ya kamata a kashe shi.
65 Sai wasu suka soma tofa masa miyau, suka rufe fuskarsa, kuma suka yi ta masa naushi suna cewa: “Idan kai annabi ne, ka gaya mana, wa ya mare ka?” Sai waɗanda suke gadin wurin suka mammare shi, kuma suka tafi da shi.
66 Yayin da Bitrus yake zaune a farfajiyar gidan, sai ɗaya daga cikin ꞌyan matan da suke yi wa babban firist hidima, ta zo wurin.
67 Da ta ga Bitrus yana jin ɗumin wuta, sai ta kalle shi kuma ta ce: “Kai ma kana tare da wannan Yesu mutumin Nazaret.”
68 Amma ya yi mūsun hakan, yana cewa: “Ban san mutumin nan ba, kuma ban san abin da kike magana a kai ba.” Sai ya fita waje zuwa ƙofar gidan.*
69 Yarinyar ta sake ganin sa a wurin kuma ta soma gaya ma waɗanda suke tsaye a wurin cewa: “Wannan ɗaya daga cikinsu ne.”
70 Sai ya sake yin mūsun hakan. Bayan ɗan lokaci, waɗanda suke tsaye a wurin sun soma gaya wa Bitrus cewa: “Babu shakka, kai ma ɗaya daga cikinsu ne, domin kai mutumin Galili ne.”
71 Sai ya soma zagi da rantsuwa yana cewa: “Ban san mutumin nan da kuke maganarsa ba!”
72 Nan da nan zakara ya yi cara a karo na biyu, kuma Bitrus ya tuna abin da Yesu ya ce masa: “Kafin zakara ya yi cara sau biyu, za ka yi mūsun sani na sau uku.” Sai ya kasa kame kansa, kuma ya fashe da kuka.
Hasiya
^ A yaren Girka, “kwalbar alabasta.” Wata ƙaramar kwalba ce da asali aka yi da dutse da ake samuwa kusa da yankin Alabastron a Masar.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Dinari ɗaya ya yi daidai da kuɗin da ake biyan lebura na aikin yini ɗaya.
^ Ko kuma “sun tsawata mata sosai.”
^ Kalmar Ibrananci ko kuma yaren Aramaik da ke nufin “Ya Uba!”
^ A yaren Girka, “Rabbai.”
^ Ko kuma “da gajeren wando.”
^ Sanhedrin shi ne Kotun Ƙolin Yahudawa. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ko kuma “zaure.”