Ta Hannun Markus 13:1-37

  • ALAMUN ƘARSHEN ZAMANI (1-37)

    • Yaƙe-yaƙe, girgizar ƙasa, da ƙarancin abinci (8)

    • Za a yi waꞌazin labari mai daɗi (10)

    • Ƙunci mai girma (19)

    • Zuwan Ɗan mutum (26)

    • Misalin itacen ɓaure (28-31)

    • Ku zauna da shiri (32-37)

13  Saꞌad da Yesu yake barin haikalin, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa: “Malam, duba, duwatsu da gine-ginen nan masu ban mamaki!” 2  Amma Yesu ya ce masa: “Ka ga waɗannan manyan gine-ginen? Za a rushe su gabaki-ɗaya, kuma ba dutse ko ɗaya da za a bari a kan wani dutse da ba za a rushe shi ba.” 3  Da Yesu yake zaune a Tudun Zaitun kuma ya fuskanci haikali, sai Bitrus, da Yaƙub, da Yohanna, da Andarawus, suka same shi shi kaɗai kuma suka tambaye shi cewa: 4  “Ka gaya mana, yaushe ne abubuwan nan za su faru, da alamar da za ta nuna cewa ƙarshen abubuwan nan ya iso?” 5  Sai Yesu ya soma gaya musu cewa: “Ku mai da hankali don kada wani ya ruɗe ku. 6  Mutane da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne shi,’* kuma za su ruɗi mutane da yawa. 7  Ƙari ga haka, idan kun ji ana yaƙe-yaƙe, da labaran yaƙe-yaƙe, kada hankalinku ya tashi; domin dole ne abubuwan nan su faru, amma ƙarshen bai zo ba tukuna. 8  “Alꞌumma za ta yaƙi alꞌumma, mulki kuma ya yaƙi mulki. Za a yi girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam, kuma za a yi ƙarancin abinci. Abubuwan nan su ne somawar azaba. 9  “Amma ku, ku kula da kanku. Mutane za su kai ku kotuna, za a yi muku dūka a majamiꞌu, kuma za ku tsaya a gaban gwamnoni da sarakuna saboda ni, domin shaida a gare su. 10  Ƙari ga haka, dole a yi waꞌazin labari mai daɗi a dukan ƙasashe tukuna. 11  Saꞌad da suke tafiya da ku don su kai ku gaban hukumomi, kada ku damu a kan abin da za ku faɗa; amma duk abin da aka gaya muku a daidai wannan lokacin, ku faɗe shi, domin ba ku ne kuke magana ba, amma ruhu mai tsarki ne yake magana ta wurinku. 12  Ƙari ga haka, ɗanꞌuwa zai ba da ɗanꞌuwansa a kashe shi, uba kuma zai ba da ɗansa, yara kuma za su yi wa iyayensu tawaye kuma hakan ya kai ga mutuwar iyayen. 13  Kuma dukan mutane za su tsane ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jimre har zuwa ƙarshe za a cece shi. 14  “Ƙari ga haka, idan kun ga abin ƙyamar nan da ke jawo hallaka yana tsaye a wurin da bai kamata ya tsaya ba (sai mai karatu ya yi ƙoƙari ya fahimta), bari waɗanda suke Yahudiya su soma guduwa zuwa tuddai. 15  Kada wanda yake saman gida ya sauko ko ya shiga cikin gida ya ɗauki wani abu daga gidansa. 16  Kuma kada wanda yake gona ya koma ga abubuwan da ya bari a baya don ya ɗauki mayafinsa. 17  Kaiton mata masu ciki da masu shayarwa a lokacin! 18  Ku ci-gaba da adduꞌa kada gudun nan ya zo muku a lokacin sanyi; 19  domin lokacin zai zama lokacin ƙunci, irin wanda ba a taɓa yi ba tun Allah ya fara halitta zuwa lokacin, kuma ba za a sake yin irin sa ba. 20  Da ba don Jehobah* ya rage kwanakin ba, da ba wanda zai tsira. Amma saboda waɗanda ya zaɓa, ya rage kwanakin. 21  “Saꞌan nan, idan wani ya ce muku, ‘Ga Kristi a nan,’ ko kuma, ‘Ga shi can,’ kada ku yarda. 22  Don Kristin ƙarya da annabawan ƙarya za su taso, su yi alamu da abubuwan ban mamaki don su ruɗi mutane, har da waɗanda aka zaɓa in zai yiwu. 23  Ku dai, ku yi tsaro, na riga na gaya muku dukan abubuwa kafin su faru. 24  “Bayan kwanakin ƙuncin, rana za ta yi duhu, wata kuma ba zai ba da haskensa ba. 25  Taurari za su faffaɗo daga sama, kuma abubuwan da ke sama za su girgiza. 26  Saꞌan nan za su ga Ɗan mutum yana zuwa a cikin gajimare tare da iko da ɗaukaka sosai. 27  Zai aiko malaꞌikunsa su tattara waɗanda ya zaɓa daga gabas, da yamma, da kudu, da kuma arewa. Daga iyakar duniya zuwa iyakar sama. 28  “Ku koyi wani abu daga misalin nan na itacen ɓaure: Da zarar kun ga ya soma fitar da ƙananan rassa da kuma ganye, kun san cewa damina ta kusa. 29  Haka ku ma, idan kun ga abubuwan nan suna faruwa, ku san cewa yana dab da bakin ƙofa. 30  A gaskiya ina gaya muku, wannan tsarar ba za ta shuɗe ba, har sai dukan waɗannan abubuwan sun faru. 31  Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba. 32  “Ba wanda ya san ranar, ko ƙarfe nawa ne wannan zai faru, ko malaꞌikun da suke sama, ko kuma Ɗan, ba su sani ba, sai dai Uban. 33  Ku ci-gaba da lura, ku ci-gaba da zama da shiri, domin ba ku san lokacin da Allah ya zaɓa ba. 34  Yana nan kamar mutumin da ya yi tafiya zuwa wata ƙasa, kuma ya ba wa bayinsa hakkin kula da gidansa, ya ba wa kowa aikin da zai yi, kuma ya umurci mai tsaron ƙofa ya zauna a shirye. 35  Don haka, ku ci-gaba da yin tsaro, don ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba, ko zai dawo da yamma, ko da tsakar dare, ko kafin asuba,* ko kuma da safe, 36  domin kada ya zo ba labari, ya same ku kuna barci. 37  Amma, abin da nake gaya muku, ina gaya wa kowa ne: Ku zauna da shiri.”

Hasiya

Ko kuma “Kristi.”
Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
A yaren Girka, “lokacin da zakara yake cara.”