Ta Hannun Markus 12:1-44
12 Sai ya soma koyar da su ta wurin misalai, yana cewa: “Akwai wani mutum da ya shuka inabi a gonarsa, kuma ya kewaye gonar da katanga, ya tona wurin matse ꞌyaꞌyan inabi a ciki. Ƙari ga haka, ya gina hasumiyar tsaro a ciki, sai ya sa wasu manoma su kula da shi, shi kuwa ya yi tafiya zuwa wata ƙasa.
2 Da lokacin girbi ya yi, sai ya aiki bawansa zuwa wurin manoman don ya karɓo masa wasu daga cikin amfanin gonar.
3 Sai manoman suka kama bawan, suka yi masa dūka kuma suka sallame shi hannu wofi.
4 Sai ya sake aika wani bawa zuwa wurin manoman, manoman suka buge shi a kai kuma sun wulaƙanta shi.
5 Ya sake tura wani bawa, kuma manoman sun kashe shi. Ya sake aika waɗansu da yawa, amma manoman sun dūki wasu, sun kuma kashe wasu.
6 A ƙarshe, sai ya aika ɗansa da yake ƙauna. Yana cewa, ‘Za su daraja ɗana.’
7 Amma manoman suka gaya wa juna cewa, ‘Wannan shi ne zai gāji gonar. Ku zo mu kashe shi don gādonsa ya zama namu.’
8 Sai suka kama shi, suka kashe shi kuma suka jefa shi a bayan gonar inabin.
9 Mene ne mai gonar zai yi? Zai zo ya kakkashe manoman kuma ya ba da gonar inabin ga wasu manoma dabam.
10 Ba ku taɓa karanta nassin nan ba, da ya ce: ‘Dutsen da magina suka ƙi, shi ne ya zama dutse* mafi amfani a ginin.
11 Wannan daga wurin Jehobah* ne, abin mamaki kuwa a idanunmu’?”
12 Da jin hakan, sun so su kama shi da ƙarfi domin sun san cewa ya yi misalin ne game da su, amma sun ji tsoron jamaꞌa. Sai suka bar shi suka tafi.
13 Bayan haka, sai suka aiki wasu Farisiyawa da rukunin mutane da ke goyan bayan Hirudus* don su sa shi ya faɗi abin da zai sa su kama shi.
14 Da suka isa, sai suka ce masa: “Malam, mun san cewa kai mai gaskiya ne, kuma ba ka neman farin jini a gaban kowa, domin ba siffar mutane ne kake dubawa ba. Amma kana koyar da hanyar Allah a cikin gaskiya. Ya dace ne mutum ya biya haraji ga Kaisar ko bai dace ba?
15 Ya kamata mu biya ne? Ko kuma bai kamata ba?” Da Yesu ya gane munafuncinsu, sai ya ce musu: “Me ya sa kuke gwada ni? Ku kawo mini dinari* in gani.”
16 Sai suka kawo masa dinari ɗaya, sai ya ce musu: “Hoton nan da sunan nan na waye ne?” Suka ce masa: “Na Kaisar ne.”
17 Sai Yesu ya ce musu: “Ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, amma ku ba Allah abin da yake na Allah.” Abin da ya fada ya burge su kuma ya ba su mamaki sosai.
18 Sai Sadukiyawa waɗanda suka ce babu tashin matattu, suka zo suka tambaye shi cewa:
19 “Malam, Musa ya gaya mana cewa, idan mutum ya mutu ya bar matarsa kuma bai haifi yaro ba, dole ɗanꞌuwansa ya auri matar domin ya haifa wa ɗanꞌuwansa ꞌyaꞌya.
20 Akwai ꞌyanꞌuwa maza guda bakwai. Na farkon ya yi aure, kuma ya mutu ba tare da ya haifi ꞌyaꞌya ba.
21 Sai na biyun ya aure ta, kuma ya mutu ba tare da ya haifi ꞌyaꞌya ba. Haka ma da na ukun.
22 Kuma dukan ꞌyanꞌuwan guda bakwai sun mutu ba tare da sun haifi ꞌyaꞌya ba. Sai a ƙarshe, matar ma ta mutu.
23 To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Domin dukansu bakwai sun aure ta.”
24 Yesu ya ce musu: “Wannan ne ya sa kuke kuskure, saboda ba ku fahimci Nassosi ko ikon Allah ba.
25 Domin idan sun tashi daga mutuwa, maza ba za su yi aure ba, kuma mata ba za a aurar da su ba, amma za su zama kamar malaꞌiku a sama.
26 Game da tashin matattu, ba ku karanta a littafin Musa, a labarin itacen ƙaya cewa Allah ya ce masa: ‘Ni ne Allah na Ibrahim, da na Ishaku, da na Yakubu’ ba?
27 Shi ba Allah na matattu ba ne, amma Allah na masu rai ne. Kun yi babban kuskure.”
28 Ɗaya daga cikin marubutan da ya zo ya ji suna gardama, ya lura cewa Yesu ya ba su amsa mai kyau, sai ya tambaye Yesu cewa: “Wace doka ce ta farko?”*
29 Yesu ya amsa masa ya ce: “Ta farko ita ce, ‘Ka saurara, Ya Israꞌila, Jehobah* Allahnmu, Jehobah* ɗaya ne,
30 kuma dole ne ka ƙaunaci Jehobah* Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan tunaninka, da kuma dukan ƙarfinka.’
31 Ta biyu kuma ita ce, ‘Dole ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ Babu wata doka da ta kai waɗannan dokokin.”
32 Marubucin ya ce masa: “Malam, ka yi magana mai kyau, bisa gaskiya, ‘Shi Ɗaya ne, kuma babu wani sai shi’;
33 kuma mutum ya ƙaunace shi da dukan zuciyarsa, da dukan fahimtarsa, da dukan ƙarfinsa, da kuma ƙaunar maƙwabci kamar kanmu, ya fi kowace irin hadaya ta ƙonawa da sauran hadayu.”
34 Da Yesu ya ga cewa mutumin ya amsa da kyau, sai ya ce masa: “Ba ka yi nisa da Mulkin Allah ba.” Amma babu wanda ya yi ƙarfin hali ya sake yi masa tambaya.
35 Da Yesu ya ci-gaba da koyarwa a haikalin, sai ya ce: “Me ya sa marubuta suka ce Kristi ɗan Dauda ne?
36 Ta wurin ikon ruhu mai tsarki, Dauda da kansa ya ce, ‘Jehobah* ya ce wa Ubangijina: “Ka zauna a hannun damana har sai na sa abokan gābanka a ƙarƙashin ƙafafunka.”’
37 Dauda da kansa ya kira shi Ubangiji, to ta yaya ya zama ɗan Dauda?”
Kuma jamaꞌar da ke sauraron sa, suna jin daɗin abin da yake faɗa.
38 A cikin koyarwarsa, ya ce: “Ku yi hankali da marubuta waɗanda suke son sa dogayen riguna suna yawo kuma suna so mutane su riƙa gaishe su a kasuwanni.
39 Ƙari ga haka, suna son kujerun gaba* a majamiꞌu da wurin zaman manya a biki.
40 Suna kwashe kaya na matan da mazajensu suka mutu, suna yin dogayen adduꞌoꞌi don a gan su. Hukuncin da za a yi musu, zai fi na sauran mutane tsanani.”
41 Sai ya zauna ya fuskanci wurin saka gudummawa, kuma yana ganin yadda jamaꞌar suke zuba kuɗi a wurin saka gudummawar, kuma masu arziki da yawa suna zuba tsabar kuɗi da yawa.
42 Sai ga wata matalauciya da mijinta ya mutu ta zo. Ta zuba ƙananan tsabar kuɗi guda biyu da ba su da daraja sosai.*
43 Sai Yesu ya kira almajiransa kuma ya ce musu: “A gaskiya ina gaya muku, kuɗin da matalauciyar nan da mijinta ya mutu ta saka, ya fi na sauran mutanen.
44 Domin dukansu sun bayar ne daga abubuwa masu yawa da suke da su, amma ita kuwa, daga cikin talaucinta, ta ba da dukan abin da take da shi, wato dukan abin da take dogara da shi.”
Hasiya
^ Akan saka wannan dutse a kwana, inda bango 2 suke haɗuwa.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Dinari ɗaya ya yi daidai da kuɗin da ake biyan lebura na aikin yini ɗaya.
^ Ko kuma “mafi muhimmanci.”
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ko kuma “kujeru mafi kyau.”
^ A yaren Girka, “lefta guda biyu, wato kwadrans ɗaya.”