Ta Hannun Luka 19:1-48
19 Sai Yesu ya shiga Jeriko kuma yana wucewa cikin garin.
2 Akwai wani mutum da ke wurin, mai suna Zakka; shi shugaban masu karɓan haraji ne, kuma yana da arziki.
3 Ya yi ta ƙoƙari ya ga ko wane ne Yesun nan, amma bai iya ba, domin shi gajere ne, kuma mutane sun yi yawa.
4 Don haka, ya gudu ya je gaba, ya hau kan wani itace* don ya ga Yesu, domin Yesu ya kusan wucewa ta hanyar.
5 Da Yesu ya kai wurin, sai ya ɗaga ido ya ce masa: “Zakka, ka sauko da sauri, domin yau zan sauka a gidanka.”
6 Sai ya sauko da sauri, kuma ya marabci Yesu a gidansa hannu bibbiyu.
7 Da suka ga haka, sai dukansu suka soma gunaguni, suna cewa: “Ya sauka a gidan mai zunubi.”
8 Amma Zakka ya tashi ya ce wa Ubangiji: “Ubangiji, zan ba wa talakawa rabin dukiyata, kuma duk abin da na ƙwace daga wurin wani, zan mayar masa ninki huɗu.”
9 Da jin haka, sai Yesu ya ce masa: “A yau, ceto ya zo gidan nan, domin shi ma ɗan Ibrahim ne.
10 Ɗan mutum ya zo ne domin ya nemi, kuma ya ceci abin da ya ɓata.”
11 Yayin da suke saurarar abubuwan nan, ya sake ba su wani misali, domin ya yi kusa da Urushalima kuma suna tsammanin Mulkin Allah zai bayyana nan da nan.
12 Sai ya ce: “Wani mutum da ya fito daga gidan sarauta, ya yi tafiya zuwa wata ƙasa mai nisa domin a naɗa shi sarki kuma ya dawo.
13 Sai ya kira goma daga cikin bayinsa, ya ba su kuɗin mina* guda goma kuma ya ce musu, ‘Ku yi kasuwanci da shi har sai na dawo.’
14 Amma ꞌyan garinsa sun tsane shi kuma suka aika wakilai, su je su ce masa, ‘Ba ma so ka zama sarkinmu.’
15 “Saꞌad da ya dawo gida bayan da aka naɗa shi sarki, sai ya kira bayinsa waɗanda ya ba su kuɗi don ya san ribar nawa ne suka samu daga kasuwancin da suka yi.
16 Sai na farkon ya zo ya ce, ‘Ubangiji, na samu ribar mina goma daga mina ɗaya da ka ba ni.’
17 Sai mutumin ya ce masa, ‘Sannu da ƙoƙari, bawan kirki! Ka nuna cewa za a iya yarda da kai a ƙaramin abu, ka yi iko a kan birane goma.’
18 Sai na biyun ya zo ya ce, ‘Ubangiji, na samu ribar mina biyar daga mina ɗaya da ka ba ni.’
19 Sai mutumin ya ce wa bawan, ‘Kai ma ka yi iko a kan birane biyar.’
20 Amma wani bawa a cikinsu ya zo ya ce, ‘Ubangiji, ga kuɗinka da na ɓoye a cikin kaya.
21 Dalilin shi ne, na ji tsoron ka, domin kai mutum ne mai zafin rai; ga son na banza a wurinka, kuma kana girbin abin da ba ka shuka ba.’
22 Sai ya ce wa bawan, ‘Kai mugun bawa ne, zan hukunta ka don abin da ka faɗa da bakinka. Ka san cewa ni mai zafin rai ne, kuma ni mutum ne mai son na banza, da girbin abin da ban shuka ba, ko ba haka ba?
23 To me ya sa ba ka sa kuɗina a banki ba, domin saꞌad da na dawo, in karɓe shi da riba?’
24 “Sai ya ce ma waɗanda suke tsaye kusa, ‘Ku karɓi kuɗin minan daga wurinsa, kuma ku ba ma wanda yake da mina goma.’
25 Amma suka ce masa, ‘Ubangiji, yana da mina goma!’—
26 ‘Ina gaya muku, duk wanda yake da abu, za a ƙara masa, amma duk wanda ba shi da abu, za a ɗauke har ɗan abin da yake da shi.
27 Ƙari ga haka, ku kawo abokan gābana nan, waɗanda ba sa so in zama sarkinsu, kuma ku kakkashe su a gabana.’”
28 Bayan da Yesu ya faɗi abubuwan nan, sai ya ci-gaba da haurawa zuwa Urushalima.
29 Saꞌad da ya kai kusa da Baitꞌfaji, da Betani da suke tudun da ake kira Tudun Zaitun, sai ya aiki almajiransa guda biyu,
30 yana cewa: “Ku shiga cikin ƙauyen nan da kuke gani, bayan kun shiga, za ku ga wani ɗan jaki da aka ɗaure, wanda ba a taɓa hawan sa ba. Ku kunce shi ku kawo shi nan.
31 Amma idan wani ya tambaye ku cewa, ‘Me ya sa kuke kunce shi?’ ku ce masa, ‘Ubangiji yana bukatar sa.’”
32 Sai waɗanda ya aika suka tafi, suka samu abubuwa daidai yadda Yesu ya gaya musu.
33 Amma da suke kunce jakin, masu jakin suka ce musu: “Me ya sa kuke kunce ɗan jakin?”
34 Sai almajiran suka ce: “Ubangiji yana bukatar sa.”
35 Sai suka kawo ma Yesu ɗan jakin, suka shimfiɗa mayafinsu a kan ɗan jakin, kuma Yesu ya zauna a kai.
36 Yayin da yake tafiya, suna ta shimfiɗa mayafinsu a kan hanya.
37 Da ya kai kusa da hanyar da ta gangaro daga Tudun Zaitun, sai taron almajiransa suka soma murna da yabon Allah da babbar murya, domin dukan ayyukan ban mamaki da suka gani,
38 suna cewa: “Mai albarka ne wanda yake zuwa a matsayin Sarki cikin sunan Jehobah!* Salama ta kasance a sama, kuma ɗaukaka ta tabbata ga Kai da kake cikin sama!”
39 Amma wasu Farisiyawa da ke cikin jamaꞌar suka ce masa: “Malam, ka tsawata wa almajiranka.”
40 Sai ya amsa ya ce: “Ina gaya muku, idan waɗannan suka yi shuru, duwatsu za su ta da murya.”
41 Da ya yi kusa, kuma ya kalli birnin Urushalima, sai ya yi kuka domin ta,
42 yana cewa: “Da ma a ce yau kin san abin da yake kawo zaman lafiya, amma yanzu an ɓoye abubuwan nan don kada ki gani da idanunki.
43 Domin kwanaki na zuwa da abokan gābanki, za su kewaye ki da sanduna masu tsini, kuma za su kawo miki hari ta kowane gefe.
44 Za su buga ki da yaranki a ƙasa, kuma ba dutse ko ɗaya da za a bari a kan wani dutse a cikinki. Domin ba ki gane lokacin da aka zo a yi miki shariꞌa* ba.”
45 Sai Yesu ya shiga cikin haikali, kuma ya soma koran waɗanda suke sayar da abubuwa,
46 yana ce musu: “A rubuce yake cewa, ‘Za a ce da gidana, gidan adduꞌa,’ amma kun mai da shi wurin ɓuyan ɓarayi.”
47 Ya ci-gaba da yin koyarwa a haikali kowace rana. Amma manyan firistoci da marubuta, da shugabannin jamaꞌa suna neman su kashe shi.
48 Amma ba su sami hanyar da za su kashe shi ba, domin mutanen sun ci-gaba da kasancewa tare da shi don su saurare shi.
Hasiya
^ Ana kiran wannan itacen, itacen sycamore.
^ Kuɗin Girka wanda ake kiran mina, yana da nauyin giram 340. Albashin wajen wata uku ke nan, kuma mina ɗaya drakma 100 ne.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ A yaren Girka, “bincike.”