Ta Hannun Luka 12:1-59

  • Yistin Farisiyawa (1-3)

  • Ku ji tsoron Allah, ba mutane ba (4-7)

  • Mutumin da ya ce ya san Kristi (8-12)

  • Misalin mai arziki marar wayo (13-21)

  • Ku daina yawan damuwa (22-34)

    • Ƙaramin garke (32)

  • Yin tsaro (35-40)

  • Bawa mai aminci da kuma bawa marar aminci (41-48)

  • Ba salama ba, amma rashin haɗin kai (49-53)

  • Muhimmancin gane abin da yake faruwa a lokacin nan (54-56)

  • Yadda za a sasanta (57-59)

12  Ana nan sai dubban mutane suka taru, har suna tattaka juna, sai Yesu ya fara magana da almajiransa, ya ce: “Ku yi hankali da yistin Farisiyawa, wato munafuncinsu. 2  Domin babu abin da aka rufe da kyau da ba za a buɗe ba, kuma babu asirin da ba za a tona ba. 3  Saboda haka, duk abin da kuka faɗa a duhu, za a ji shi a cikin haske, kuma duk abin da kuka gaya ma wani a kunne, za a yi shelarsa daga saman gidaje. 4  Ƙari ga haka, ina gaya muku abokaina, kada ku ji tsoron waɗanda za su iya kashe jiki kuma bayan hakan ba za su iya yin wani abu ba. 5  Amma zan nuna muku wanda za ku ji tsoron sa: Ku ji tsoron wanda bayan ya kashe ku, yana da iko ya jefa ku cikin Gehenna.* Hakika ina gaya muku, ku ji tsoron Wannan. 6  Ana sayan ƙananan tsuntsaye* guda biyar da tsabar kuɗi biyu da ba su da daraja, ko ba haka ba? Duk da haka, Allah ba ya manta* da ko ɗayansu. 7  Kuma ko gashin kanku ma an san adadinsu. Kada ku ji tsoro; don kuna da daraja fiye da ƙananan tsuntsaye da yawa. 8  “Ina gaya muku, duk wanda ya faɗa a gaban mutane cewa ya san ni, Ɗan mutum ma zai faɗa a gaban malaꞌikun Allah cewa ya san shi. 9  Amma duk wanda ya yi mūsun sani na a gaban mutane, za a yi mūsun sanin sa a gaban malaꞌikun Allah. 10  Duk wanda ya yi wa Ɗan mutum baƙar magana, za a gafarta masa, amma duk wanda ya yi maganar saɓo game da ruhu mai tsarki, ba za a gafarta masa ba. 11  Saꞌad da suka kai ku a gaban taron jamaꞌa,* da jamiꞌan gwamnati, da hukumomi, kada ku damu a kan abin da za ku faɗa ko yadda za ku faɗe shi don ku kāre kanku, ko kuma wasu abubuwan da za ku faɗa, 12  domin ruhu mai tsarki zai koya muku abubuwan da za ku faɗa a wannan lokacin.” 13  Sai wani mutum daga cikin jamaꞌar ya ce wa Yesu: “Malam, ka gaya wa ɗanꞌuwana ya ba ni rabona na gādon da aka bar mana.” 14  Sai ya tambaye mutumin ya ce: “Abokina, wa ya naɗa ni alƙali ko kuma mai raba muku gādo?” 15  Sai Yesu ya ce musu: “Ku lura sosai, kuma ku guji kowace irin haɗama, domin ko da mutum yana da dukiya da yawa, ba za su ba shi rai ba.” 16  Don haka, sai ya ba su wani misali cewa: “Gonar wani mutum mai arziki ta ba da amfani sosai. 17  Sai ya fara tunani a ransa yana cewa, ‘Me zan yi yanzu da ba ni da wurin da zan tara amfanin gonata?’ 18  Sai ya ce, ‘Na san abin da zan yi: Zan rusa waɗannan rumbunana, in kuma gina waɗansu manya, a wurin zan tattara dukan amfanin gonata da dukan kayana, 19  kuma zan ce wa kaina: “Kana da abubuwa masu kyau da yawa da za su ishe ka shekaru masu yawa; don haka, ka huta, ka ci, ka sha, kuma ka ji daɗinka.”’ 20  Amma Allah ya ce masa, ‘Kai marar tunani, da daren nan ne za ka mutu. Don haka, abubuwan nan da ka tara, za su zama na waye?’ 21  Haka zai faru da duk wanda ya tara wa kansa dukiya amma a gaban Allah bai da arziki.” 22  Sai Yesu ya ce wa almajiransa: “Shi ya sa nake gaya muku cewa, ku daina yawan damuwa a kan yadda za ku rayu, game da abin da za ku ci ko a kan abin da za ku saka a jiki. 23  Domin rai ya fi abinci kuma jiki ya fi abin da za ku saka. 24  Ku lura da hankaki: Ba sa shuka iri, ko girbi, ko kuma tarawa a rumbuna, duk da haka, Allah yana ciyar da su. Shin ba ku fi tsuntsaye daraja sosai ba? 25  Wane ne a cikinku ta yawan damuwa zai iya ƙara ko minti ɗaya* ga tsawon rayuwarsa? 26  Saboda haka, idan ba za ku iya yin irin wannan ƙaramin abu ba, me ya sa za ku riƙa yawan damuwa game da sauran abubuwan? 27  Ku yi tunani a kan yadda furanni suke girma: Ba sa aiki, ko yin saƙa, duk da haka, ina gaya muku, ko Sulemanu da dukan darajarsa bai taɓa yin ado kamar ɗaya daga cikin furannin nan ba. 28  Idan har Allah zai yi wa furannin daji ado kamar haka, waɗanda a yau suna nan, gobe su bushe kuma a jefa su cikin wuta, ba kwa ganin Allah zai tanada muku abin sakawa fiye da su ba, ku masu ƙarancin bangaskiya? 29  Saboda haka, ku daina damuwa a kan abin da za ku ci, da abin da za ku sha, kuma ku daina yawan damuwa; 30  domin dukan abubuwan nan ne mutanen duniya suke nema da dukan zuciya, amma Ubanku ya san kuna bukatar abubuwan nan. 31  A maimakon haka, ku ci-gaba da sa Mulkinsa farko a rayuwarku, kuma zai ƙara muku abubuwan nan. 32  “Ya ku ƙaramin garke, kada ku ji tsoro domin Ubanku ya amince ya ba ku Mulkin. 33  Ku sayar da abubuwan da kuke da su, kuma ku ba wa talakawa kyauta.* Ku samo jakar kuɗi da ba za ta tsufa ba, wato abubuwa masu kyau da ba za su taɓa ƙarewa ba a sama, wurin da ɓarawo ba zai iya sacewa ba, kuma ƙwari ba za su iya cinye su ba. 34  Domin inda dukiyarku take, wurin ne zukatanku za su kasance. 35  “Ku saka rigarku, ku zauna a shirye* kuma ku kunna fitilunku, 36  ku zama kamar mutanen da suke jiran maigidansu ya dawo daga bikin aure, saboda in ya dawo kuma ya ƙwanƙwasa ƙofa, za ku buɗe masa nan da nan. 37  Waɗannan bayin za su yi farin ciki saꞌad da maigidansu ya dawo kuma ya ga cewa ba su yi barci ba! Hakika ina gaya muku cewa, zai saka rigar masu hidima kuma ya ce ma waɗannan bayin su zauna don ya yi musu hidima. 38  Kuma waɗannan bayin za su yi farin ciki idan ya dawo tsakanin ƙarfe tara na dare zuwa tsakar dare, ko ma tsakar dare zuwa ƙarfe uku na asuba, kuma ya same su a shirye! 39  Amma ku sani cewa, da a ce maigida ya san lokacin da ɓarawo zai zo, da ba zai bari a shiga gidansa ba. 40  Haka ku ma, ku kasance a shirye, domin Ɗan mutum zai zo a lokacin da ba ku yi tsammani ba.” 41  Sai Bitrus ya ce: “Ubangiji, wannan misalin a kan mu ne kawai ka yi, ko kuwa ya shafi kowa?” 42  Sai Ubangiji ya ce: “Wane ne bawan nan mai aminci, wanda yake da hikima, wanda maigidansa ya naɗa shi ya lura da dukan bayin da ke gidansa don ya riƙa ba wa bayin abinci a daidai lokaci? 43  Bawan nan zai yi farin ciki idan maigidansa ya dawo, kuma ya same shi yana yin abin da ya ce ya yi! 44  A gaskiya ina gaya muku, zai ba shi hakkin kula da dukan mallakarsa. 45  Amma idan bawan ya yi tunani a zuciyarsa cewa, ‘Maigidana yana jinkirin dawowa,’ sai ya soma dūkan sauran bayin maza da mata, yana ci da sha da kuma buguwa, 46  maigidan wannan bawan zai dawo a ranar da bawan bai yi tsammani ba kuma a lokacin da bai sani ba. Maigidansa zai yi masa hukunci mafi tsanani kuma ya haɗa shi wuri ɗaya da marasa bangaskiya. 47  Sai kuma bawan da ya fahimci abin da maigidansa yake so ya yi amma bai yi shiri ko ya yi abin da aka ce ya yi ba, za a yi masa bulala da yawa. 48  Wanda kuma bai fahimci abin da maigidansa yake so ya yi ba, amma ya yi abin da ya isa a yi masa bulala, za a yi masa bulala kaɗan. Hakika, duk wanda aka ba shi abu mai yawa, za a bukaci abu mai yawa daga wurinsa. Kuma wanda aka ba shi hakkin kula da abubuwa da yawa, za a bukaci ƙarin abubuwa daga wurinsa. 49  “Na zo ne in kunna wuta a duniya, idan wutar ta riga ta kamu, fatan me kuma zan yi? 50  Hakika, ina da wata baftisma da za a yi mini, kuma hankalina ba zai kwanta ba har sai an gama! 51  Kuna tsammani na zo in kawo salama a duniya ne? A ina! ina gaya muku, ba salama na kawo ba, sai dai rashin haɗin kai. 52  Daga yanzu, mutane biyar a gida ɗaya ba za su kasance da haɗin kai ba. Uku za su yi gāba da biyu, biyu kuma su yi gāba da uku. 53  Ba za su kasance da haɗin kai ba, baba zai yi gāba da ɗa, ɗa kuma zai yi gāba da baba, mama za ta yi gāba da ꞌya, ꞌya kuma za ta yi gāba da mamarta, mamar miji za ta yi gāba da matar ɗanta, matar ɗan za ta yi gāba da mamar mijinta.” 54  Yesu ya kuma ce wa jamaꞌar: “Saꞌad da kuka ga hadari yana haɗuwa ta yamma, kukan ce, ‘Za a yi ruwan sama sosai,’ kuma hakan yakan faru. 55  Idan kuma kuka ji iska tana hurowa daga kudu, kukan ce, ‘Za a yi zafi sosai,’ kuma hakan yakan faru. 56  Munafukai, kuna iya gane yanayin duniya da kuma sararin sama amma me ya sa ba ku iya gane maꞌanar abubuwan da suke faruwa a yanzu ba? 57  Me ya sa ku da kanku ba kwa iya sanin abin da ya dace ku yi? 58  Alal misali, idan wani ya kai ƙarar ka kuma kai da shi kuna kan hanya zuwa wurin wani mai mulki, ka yi ƙoƙari ka sasanta da shi tun kuna hanya, domin kada ya kai ka gaban alƙali, alƙali ya haɗa ka da jamiꞌin kotu, jamiꞌin kotun kuma ya jefa ka a kurkuku. 59  A gaskiya ina gaya maka cewa, kafin a fitar da kai daga kurkukun, sai ka biya dukan kuɗin* da kake da shi.”

Hasiya

Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Ko kuma “gwara.”
Ko kuma “watsi.”
Yana kuma iya nufin, “majamiꞌu.”
Ko kuma “kubit ɗaya.”
Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
A yaren Girka, “ku sha ɗamara.”
Ko kuma “ƙwandala mafi ƙanƙanta.”