Ta Hannun Luka 11:1-54

  • Yadda za a yi adduꞌa (1-13)

    • Adduꞌar da Yesu ya koyar (2-4)

  • An fitar da aljanu da yatsar Allah (14-23)

  • Yadda ruhu mai ƙazanta ke dawowa (24-26)

  • Farin ciki na gaske (27, 28)

  • Alamar Yunana (29-32)

  • Fitilar jiki (33-36)

  • Kaiton munafukai (37-54)

11  Akwai lokacin da Yesu yake adduꞌa a wani wuri, da ya gama, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya gaya masa cewa: “Ubangiji, ka koya mana yadda za mu yi adduꞌa, kamar yadda Yohanna ya koya wa almajiransa.” 2  Sai ya ce musu: “A duk lokacin da za ku yi adduꞌa, ku ce: ‘Ya Uba, a tsarkake sunanka. Mulkinka ya zo. 3  Ka ba mu abincinmu kowace rana, daidai da bukatunmu na kullum. 4  Ka yafe mana zunubanmu, domin mu ma mun gafarta ma dukan waɗanda muke bin su bashi; kuma kada ka kai mu cikin jarraba.’” 5  Sai ya ce musu: “A ce waninku yana da aboki kuma ya je wurin abokin da tsakar dare, ya ce masa, ‘Aboki, ka ba ni aron burodi guda uku, 6  domin wani abokina da ya dawo daga tafiya, ya sauka a wurina yanzu-yanzu, kuma ba ni da wani abin da zan ba shi.’ 7  Amma mutumin ya amsa masa daga cikin ɗaki ya ce: ‘Ka daina damu na. Na riga na kulle ƙofa, kuma ni da yarana mun kwanta, ba zan iya tashi in ba ka kome ba.’ 8  Ina gaya muku, ko da mutumin ba ya so ya tashi ya ba shi wani abu domin shi abokinsa ne, da yake ya ci-gaba da nacewa, mutumin zai tashi ya ba shi duk wani abin da yake bukata. 9  Saboda haka ina ce muku, ku ci-gaba da roƙo, za a ba ku; ku ci-gaba da nema, za ku samu, ku ci-gaba da ƙwanƙwasawa, za a buɗe muku. 10  Domin duk wanda yake roƙo, za a ba shi, duk wanda yake nema, zai samu, kuma duk wanda yake ƙwanƙwasawa, za a buɗe masa. 11  Hakika, wane baba ne a cikinku, wanda idan ɗansa ya roƙe shi kifi, zai ba shi maciji maimakon kifi? 12  Ko kuma idan ya roƙi ƙwai, sai ya miƙa masa kunama? 13  Don haka, idan ku da kuke mugaye, kun san yadda za ku ba wa yaranku abubuwa masu kyau, ba kwa ganin Uba wanda yake sama zai fi ba da ruhu mai tsarki ga waɗanda suke roƙon sa?” 14  Bayan haka, ya fitar da wani aljani da ya hana wani mutum yin magana. Bayan aljanin ya fita daga jikin mutumin, sai mutumin ya soma magana, kuma jamaꞌar suka yi mamaki sosai. 15  Amma wasu sun ce: “Yana fitar da aljanu ne ta wurin Belzebub* shugaban aljanu.” 16  Amma kuma wasu don suna so su gwada shi, sai suka soma ce masa ya nuna musu wata alama daga sama. 17  Da yake Yesu ya san abin da suke tunani, sai ya ce musu: “Duk mulkin da mutanensa sun rabu kashi biyu kuma suna faɗa da juna zai hallaka, kuma duk gidan da mutanensa sun rabu kashi biyu kuma suna faɗa da juna ba zai tsaya ba. 18  Haka ma, idan Shaiɗan ya rabu kashi biyu kuma yana faɗa da kansa, ta yaya mulkinsa zai tsaya? Domin kun ce ina fitar da aljanu da ikon Belzebub. 19  Idan ina fitar da aljanu da ikon Belzebub, da wane iko ne ꞌyaꞌyanku suke fitar da su? Shi ya sa su ne za su yi muku shariꞌa. 20  Amma idan da yatsar Allah ne nake fitar da aljanun, hakan na nufin cewa Mulkin Allah ya zo kuma ba ku sani ba. 21  Idan mutum mai ƙarfi yana gadin fadarsa da makami, ba za a iya saci kayansa ba. 22  Amma saꞌad da wanda ya fi shi ƙarfi ya kawo masa hari, kuma ya yi nasara a kansa, mutumin zai kwashe dukan makamansa da yake dogara da su, kuma zai rarraba wa mutane abubuwan da ya kwashe daga wurinsa. 23  Duk wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni, kuma duk wanda ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi. 24  “Saꞌad da ruhu mai ƙazanta ya fito daga jikin mutum, yakan yi ta yawo a wuraren da babu ruwa domin ya sami wurin hutawa, kuma idan bai samu ba, sai ya ce, ‘Zan koma gidana na dā inda na fito.’ 25  Idan ya isa, sai ya ga an share gidan da kyau kuma an yi masa ado. 26  Sai ya koma ya kwaso waɗansu ruhohi masu ƙazanta guda bakwai, waɗanda suka fi shi mugunta. Bayan da suka shiga ciki sai suka zauna a wurin. A ƙarshe, yanayin mutumin zai yi muni sosai fiye da na dā.” 27  Yayin da yake faɗin abubuwan nan, sai wata mata daga jamaꞌar ta ta da murya ta ce: “Mai farin ciki ce wadda ta haife ka ta kuma shayar da kai!” 28  Amma ya ce mata: “Aꞌa, a maimakon haka, masu farin ciki ne waɗanda suke jin kalmar Allah, kuma suke aikata ta!” 29  Da jamaꞌa suna ƙaruwa, sai ya ce: “Mutanen zamanin nan mugaye ne; suna neman a nuna musu alama, amma ba za a nuna musu alama ba, sai dai alamar Yunana. 30  Kamar yadda Yunana ya zama alama ga mutanen Nineba, haka ma Ɗan mutum zai zama ga mutanen zamanin nan. 31  A ranar shariꞌa, sarauniyar kudu* za ta tashi tare da mutanen zamanin nan ta nuna wa mutanen zamanin nan cewa ba su yi daidai ba. Domin ta fito daga wuri mai nisa sosai ta ji koyarwar Sulemanu. Ga shi kuwa wanda ya fi Sulemanu yana nan. 32  A ranar shariꞌa, mutanen Nineba za su tashi tare da mutanen zamanin nan, su nuna wa mutanen zamanin nan cewa ba su yi daidai ba, domin su sun tuba saboda waꞌazin Yunana. Ga shi kuwa wanda ya fi Yunana yana nan. 33  Bayan mutum ya kunna fitila, ba ya ɓoye ta ko kuma ya rufe ta,* amma yakan ajiye ta a kan sandar riƙe fitila, domin waɗanda suka shigo su ga hasken. 34  Ido ne fitilar jiki. Idan ba kwa yin rawan ido, jikinku zai kasance da haske; amma idan kuna rawan ido,* jikinku zai yi duhu. 35  Saboda haka, ku mai da hankali fa, kada ya zama cewa hasken da ke jikinku duhu ne. 36  Ƙari ga haka, idan dukan jikinku haske ne, kuma babu wani ɓangarensa da akwai duhu, dukan jikinku zai haskaka kamar yadda fitila take ba ku haske.” 37  Bayan da Yesu ya gama magana, sai wani Bafarisi ya ce wa Yesu ya zo su ci abinci tare. Sai ya shiga ya zauna yana cin abinci a teburi. 38  Amma Bafarisin ya yi mamaki saꞌad da ya ga cewa Yesu bai fara da wanke hannu* kafin ya soma cin abinci ba. 39  Amma Ubangiji ya ce masa: “Ku Farisiyawa kukan wanke bayan kofi da na kwano, amma zuciyarku na cike da haɗama da kuma mugunta. 40  Marasa tunani! Wanda ya yi bayan, ai shi ne ya yi cikin ma, ko ba haka ba? 41  Amma bari kyautar da kuke ba wa talakawa* ya zama abin da ya fito daga zuciyarku, kuma kome game da ku zai zama da tsabta. 42  Kaiton ku, Farisiyawa, domin kuna ba da kashi goma na mint da na rue* da wasu kayan lambu! Amma kun yi watsi da adalci, da kuma nuna wa Allah ƙauna. Yana da muhimmanci ku yi abubuwa na farkon, amma ba wai ku yi watsi da sauran abubuwan nan ba. 43  Kaiton ku, Farisiyawa, domin kuna son kujerun gaba* a majamiꞌu, kuma kuna so mutane su riƙa gaishe ku a kasuwanni! 44  Kaiton ku, domin kuna kama da kaburburan da ba a iya ganewa da kyau, waɗanda mutane suke tafiya a kai don rashin sani!” 45  Sai ɗaya daga cikin waɗanda suka san Doka* ya amsa ya ce wa Yesu: “Malam, mu ma kana zagin mu ta wurin abubuwan nan da kake faɗa.” 46  Sai ya ce: “Kaiton ku, ku ma waɗanda kuka san Doka, domin kuna ɗaura wa mutane kaya masu nauyi da suke da wuyar ɗaukawa, amma ku da kanku ba kwa so ku taɓa kayan da yatsunku! 47  “Kaiton ku, domin kuna gina kaburburan annabawa, amma kakanninku ne suka kashe su! 48  Hakika, kun nuna cewa ku shaidu ne ga abubuwan da kakanninku suka yi, duk da haka, kun amince da abin da suka yi, domin sun kashe annabawan, ku kuma kuna gina kaburburansu. 49  Shi ya sa Allah ma ya nuna irin hikimar da yake da ita saꞌad da ya ce: ‘Zan aika musu annabawa da kuma manzanni, za su kashe waɗansu, kuma za su tsananta ma waɗansu, 50  domin alhakin jinin dukan annabawan da aka kashe tun daga farkon duniya* ya kasance a kan mutanen zamanin nan. 51  Daga jinin Habila har zuwa jinin Zakariya wanda aka kashe tsakanin bagade da kuma gidan.’* Hakika, ina gaya muku, alhakin jinin zai kasance a kan mutanen zamanin nan. 52  “Kaiton ku, ku waɗanda kuka san Doka, domin kun hana mutane sanin Allah. Ku da kanku ba ku shiga Mulkin Allah ba, ba ku kuma bar masu son shiga su shiga ba!” 53  Saꞌad da Yesu ya bar wurin, sai marubuta da kuma Farisiyawa suka soma matsa masa da kuma yi masa tambayoyi da yawa, 54  suna jira su ga ko zai faɗi abin da zai sa su kama shi.

Hasiya

Sunan da ake kiran Shaiɗan.
Wato, Sarauniya Sheba.
Ko kuma “rufe ta da kwando.”
Wato, kishin wasu don abin da suke da shi.
Wato, wanke hannu irin na alꞌadar Yahudawa.
Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Wani ganye ne da ake amfani da shi wurin magani, da kuma sa abinci ya yi ɗanɗano.
Ko kuma “kujeru mafi kyau.”
Ko kuma “Dokar Musa.”
Da alama wannan yana nufin lokacin da Adamu da Hauwaꞌu suka haifi yara.
Ko kuma “haikali.”