Zuwa ga Filibiyawa 4:1-23
4 Saboda haka, ꞌyanꞌuwana waɗanda nake ƙauna kuma nake marmarin gani, dalilin farin cikina da kuma rawanina, ku tsaya daram a wannan hanyar cikin Ubangiji, ya ku waɗanda nake ƙauna.
2 Ina roƙon Yudiya kuma ina roƙon Sintiki su zama da raꞌayi ɗaya cikin Ubangiji.
3 Hakika, ina kuma roƙon ka a matsayin abokin aikina na gaske, ka ci-gaba da taimaka wa matan nan waɗanda suka yi aiki da ƙwazo tare da ni saboda labari mai daɗi, tare da Kilemen da sauran abokan aikina waɗanda sunayensu suna cikin littafin rai.
4 Kullum ku yi farin ciki cikin Ubangiji. Ina ƙara cewa, Ku Yi Farin Ciki!
5 Bari dukan mutane su san ku a matsayin masu sanin yakamata.* Ubangiji ya kusan zuwa.
6 Kada ku damu a kan kowane abu, amma a cikin kowane abu, ku gaya wa Allah abubuwan da ke damun ku ta wurin adduꞌa da roƙe-roƙe sosai tare da godiya;
7 kuma salamar Allah wadda ta fi dukan ganewar ɗanꞌadam, za ta kāre zukatanku da tunaninku ta wurin Kristi Yesu.
8 A ƙarshe, ꞌyanꞌuwana, ku ci-gaba da yin tunani a kan dukan abubuwan da suke na gaske, da dukan abubuwan da suke da muhimmanci,* da dukan abubuwan da suke na adalci, da dukan abubuwan da suke da tsabta, da dukan abubuwan da suke jawo ƙauna, da dukan abubuwan da ake magana mai kyau a kansu, da dukan abubuwan da suke da kyau a gaban Allah, da kuma dukan abubuwan da suka cancanci yabo.
9 Ku ci-gaba da aikata abubuwan da kuka koya, kuka karɓa, kuka ji, kuma kuka gani daga wurina, kuma Allah na salama zai kasance tare da ku.
10 Ina farin ciki sosai cikin Ubangiji don yanzu kun sake nuna cewa kun damu da ni. Ko da yake kun damu da ni, amma ba ku sami zarafin nuna hakan ba.
11 Ba wai ina faɗan hakan domin ina bukatar wani abu ba ne, gama na koyi yadda zan kasance da gamsuwa ko da wane irin yanayi ne nake ciki.
12 Na san yadda zan yi rayuwa da abubuwa kaɗan da kuma yadda zan yi rayuwa da abubuwa da yawa. A cikin dukan abubuwa da kuma dukan yanayoyi, na koyi sirrin zama mai gamsuwa saꞌad da na ƙoshi ko kuma ina jin yunwa, ko da ina da abubuwa da yawa ko ba ni da shi.
13 Gama a cikin dukan abubuwa ina samun iko ta wurin wanda yake ba ni ƙarfi.
14 Duk da haka, kun kyauta da kuka ci-gaba da taimaka mini yayin da nake shan wahala.
15 Ku ma Filibiyawa kun san cewa a lokacin da kuka fara koya game da labari mai daɗi, saꞌad da na bar Makidoniya, babu ikilisiyar da ta taimaka mini a batun bayarwa da karɓa sai ku kaɗai;
16 gama saꞌad da nake Tasalonika, kun aika mini taimako don ku biya bukatuna, ba sau ɗaya ba amma har sau biyu.
17 Ba wai ina neman wata kyauta daga wurinku ba ne, amma ina so ku yi ayyuka masu kyau ne don ku sami ƙarin lada.*
18 Ina da kome da nake bukata, har ma fiye da hakan. Ina da isasshen abubuwan da nake bukata bayan da na karɓo abin da kuka aika mini ta wurin Abaforiditus. Kyautar na kama da turare mai ƙamshi, hadaya ce da Allah zai karɓa kuma ya ji daɗin ta.
19 A sakamakon haka, Allahna zai biya dukan bukatunku bisa ga arzikinsa mai ɗaukaka ta wurin Kristi Yesu.
20 Yanzu, bari ɗaukaka ta tabbata ga Allahnmu wanda kuma shi ne Ubanmu har abadan abadin. Amin.
21 Ku miƙa gaisuwata ga kowane tsarkaka da ke da haɗin kai da Kristi Yesu. ꞌYanꞌuwan da suke tare da ni suna aika muku gaisuwarsu.
22 Dukan tsarkaka, musamman ma waɗanda suke gidan Kaisar, sun aika muku gaisuwarsu.
23 Bari alherin Ubangiji Yesu Kristi ya kasance da ku don halin kirki* da kuka nuna.

