Ayyukan Manzanni 9:1-43

  • Shawulu a hanya zuwa Damaskus (1-9)

  • An aika Hananiya ya je ya taimaka wa Shawulu (10-19a)

  • Shawulu ya yi waꞌazi game da Yesu a Damaskus (19b-25)

  • Shawulu ya ziyarci Urushalima (26-31)

  • Bitrus ya warkar da Aniyas (32-35)

  • An ta da Dokas daga mutuwa (36-43)

9  Amma Shawulu ya ci-gaba da tsoratar da kuma kashe almajiran Ubangiji, sai ya je wurin shugaban firistoci 2  kuma ya roƙe shi ya ba shi wasiƙu zuwa ga majamiꞌun da ke Damaskus, don idan ya ga masu bin Hanyar Ubangiji, maza ko mata, ya ɗaure su ya kawo Urushalima. 3  Yayin da yake cikin tafiya, kuma ya yi kusa da Damaskus, nan take, sai wani haske daga sama ya haska kewaye da shi, 4  sai ya faɗi ƙasa kuma ya ji wata murya ta ce masa: “Shawulu, Shawulu, me ya sa kake tsananta mini?” 5  Sai ya yi tambaya ya ce: “Wane ne kai, Ubangiji?” Sai ya ce: “Ni ne Yesu, wanda kake tsananta masa. 6  Amma ka tashi, ka shiga cikin birnin, kuma za a gaya maka abin da ya kamata ka yi.” 7  Mutanen da suke tafiya tare da shi sun tsaya kawai, ba su iya ce kome ba. Hakika, sun ji murya, amma ba su ga kowa ba. 8  Sai Shawulu ya tashi daga ƙasa, ko da yake idanunsa a buɗe suke ba ya ganin kome. Sai suka riƙe hannunsa, kuma suka kawo shi cikin Damaskus. 9  Ya yi kwana uku bai ga kome ba, kuma bai ci ba, bai sha ba. 10  Akwai wani almajiri mai suna Hananiya a Damaskus, sai Ubangiji ya yi magana da shi ta wahayi, ya ce: “Hananiya!” Sai ya ce: “Ga ni nan, Ubangiji.” 11  Sai Ubangiji ya ce masa: “Ka tashi, ka tafi titin nan da ake kira Miƙaƙƙe, kuma ka nemi wani mutum mai suna Shawulu, daga Tarsus, a gidan Yahuda. Ga shi! yana yin adduꞌa, 12  kuma a cikin wahayi, ya ga wani mutum mai suna Hananiya ya zo ya sa hannayensa a kansa domin ya soma gani.” 13  Amma Hananiya ya amsa ya ce: “Ubangiji, na ji daga wurin mutane da yawa game da mutumin nan, da dukan tsanantawa da ya yi wa mutanenka masu tsarki a Urushalima. 14  Kuma ko a nan ma, manyan firistoci sun ba shi izinin kama duk wanda yake kira ga sunanka.” 15  Amma Ubangiji ya ce masa: “Ka je! domin na zaɓi mutumin nan* ya yi shelar sunana ga alꞌummai, da sarakuna, da kuma ꞌyaꞌyan Israꞌila. 16  Zan nuna masa dalla-dalla dukan wahalolin da zai sha saboda sunana.” 17  Sai Hananiya ya tafi kuma ya shiga gidan, ya sa hannayensa a kan Shawulu kuma ya ce: “Ɗanꞌuwana Shawulu, Ubangiji Yesu, wanda ya bayyana a gare ka a hanyar da ka biyo saꞌad da kake zuwa ne ya aiko ni, domin ka soma gani, kuma a cika ka da ruhu mai tsarki.” 18  Nan da nan, sai wani abu kamar ɓawo ya faɗi daga idanun Shawulu, kuma ya soma gani. Sai ya tashi, kuma aka yi masa baftisma. 19  Sai ya ci abinci ya samu ƙarfi. Ya zauna da almajiran a Damaskus na ꞌyan kwanaki, 20  kuma nan da nan, ya soma waꞌazi game da Yesu a cikin majamiꞌu, yana cewa wannan shi ne Ɗan Allah. 21  Amma dukan waɗanda suka ji shi sun yi mamaki, kuma suna cewa: “Ba wannan ne ya tsananta ma dukan waɗanda suke kira ga sunan nan a Urushalima ba? Ba ya zo nan ne domin ya kama su, kuma ya kai su* wurin manyan firistoci ba?” 22  Shawulu ya ci-gaba da samun ƙarin ƙarfi kuma ya ba Yahudawan da ke zama a Damaskus mamaki sosai, yayin da yake ba su tabbacin da ya nuna cewa Yesu shi ne Kristi. 23  Bayan kwanaki da yawa, sai Yahudawan suka haɗa kai, kuma suka ƙulla yadda za su kashe shi. 24  Amma Shawulu ya ji game da shirin da suke yi. Suna kuma zuba ido a kan ƙofofin garin dare da rana don su kashe shi. 25  Don haka, da dare, almajiransa suka ɗauke shi, suka saka shi a kwando, kuma suka saukar da shi ta wani wundo* da ke katangar birnin. 26  Da ya isa Urushalima, ya yi ƙoƙari ya shiga cikin almajiran, amma dukansu suna tsoron sa domin ba su yarda cewa shi almajiri ba ne. 27  Sai Barnabas ya zo ya taimaka masa, ya kai shi wurin manzannin, sai ya bayyana musu dalla-dalla yadda Shawulu ya ga Ubangiji a hanya, da yadda Ubangiji ya yi magana da shi, da kuma yadda ya yi magana game da sunan Yesu da ƙarfin hali a Damaskus. 28  Sai ya kasance tare da su, kuma yana shiga da fita a cikin Urushalima, yana magana da ƙarfin hali a cikin sunan Ubangiji. 29  Yana magana da kuma gardama da Yahudawan da ke yin yaren Girka, amma sun yi ta ƙoƙarin kashe shi. 30  Saꞌad da ꞌyanꞌuwan suka ji hakan, sai suka ɗauke shi suka kawo shi Kaisariya, kuma suka aika shi Tarsus. 31  Saꞌan nan, ikilisiyoyin da ke dukan yankunan Yahudiya, da Galili, da Samariya, suka shiga lokacin salama, kuma suka ci-gaba da yin ƙarfi. Ƙari ga haka, yayin da suke ci-gaba da nuna cewa suna tsoron Jehobah* kuma suna samun ƙarfafa daga ruhu mai tsarki, sun ci-gaba da ƙaruwa. 32  Yayin da Bitrus yake tafiya zuwa wurare dabam-dabam a yankin, sai ya zo wurin tsarkaka da suke zama a Lidda. 33  A nan, ya haɗu da wani mutum mai suna Aniyas, wanda ya yi shekaru takwas yana kwance a gadonsa, domin jikinsa ya shanye. 34  Sai Bitrus ya ce masa: “Aniyas, Yesu Kristi ya warkar da kai. Ka tashi ka gyara gadonka.” Nan da nan sai ya tashi. 35  Saꞌad da waɗanda suke zama a Lidda da kuma Sharon suka gan shi, sai suka juyo ga Ubangiji. 36  Akwai wata almajira a Joffa, mai suna Tabita, idan aka fassara sunanta, yana nufin “Dokas.”* Tana yin ayyukan kirki sosai da kuma ba da kyauta ga talakawa. 37  Amma a kwanakin, ta yi rashin lafiya kuma ta mutu. Sai suka yi mata wanka, kuma suka kwantar da ita a ɗakin da ke saman gidan. 38  Da yake Lidda yana kusa da Joffa, da almajiran suka ji cewa Bitrus yana birnin, sai suka aika mutane guda biyu su roƙe shi cewa: “Don Allah ka zo wurinmu da sauri.” 39  Da jin hakan, sai Bitrus ya tashi kuma ya bi su. Da ya isa, sun kai shi cikin ɗakin da ke saman gidan. Sai dukan mata da mazajensu suka mutu suka zo wurinsa, suna kuka, suna kuma nuna masa riguna da mayafin da Dokas ta yi musu saꞌad da take da rai. 40  Sai Bitrus ya fitar da kowa waje, kuma ya durƙusa ya yi adduꞌa. Da ya juya zuwa inda gawar take, ya ce: “Tabita, ki tashi!” Sai ta buɗe idanunta. Da ta ga Bitrus, sai ta tashi, ta zauna. 41  Sai ya miƙa mata hannunsa, ya ɗaga ta, sai ya kira tsarkaka da matan da mazajensu suka mutu, kuma ya miƙa musu ita da rai. 42  Labarin nan ya yaɗu a dukan Joffa, kuma mutane da yawa sun ba da gaskiya ga Ubangiji. 43  Sai ya ci-gaba da zama a Joffa na ꞌyan kwanaki a gidan wani mai aikin fatar dabbobi, mai suna Siman.

Hasiya

A yaren Girka, “mutumin nan yana kamar tulun ƙasa da na zaɓa.”
A yaren Girka, “kai su a ɗaure.”
Ko kuma “taga.”
Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Dokas a yaren Girka da Tabita a yaren Aramaik, duk suna nufin wani irin dabbar daji da ke kamar “Barewa.”