Ayyukan Manzanni 5:1-42
5 Akwai wani mutum mai suna Hananiya, shi da matarsa Safira sun sayar da wasu abubuwan da suke da su.
2 Amma ya ɓoye wasu daga cikin kuɗin da sanin matarsa, kuma ya kawo sauran kuɗin ya ajiye a gaban manzannin.
3 Sai Bitrus ya ce masa: “Hananiya, me ya sa ka bar Shaiɗan ya ba ka ƙarfin zuciyar yin ƙarya ga ruhu mai tsarki, kuma ka ɓoye wasu daga cikin kuɗin filin da ka sayar?
4 Kafin ka sayar da filin, ba naka ba ne? Bayan da ka sayar da filin, kuɗin ba naka ba ne? Me ya sa ka yi tunanin yin irin wannan abin a zuciyarka? Ai, ba mutum ka yi wa ƙarya ba, Allah ne ka yi wa.”
5 Da Hananiya ya ji haka, sai ya faɗi ya mutu. Kuma tsoro ya kama dukan mutanen da suka ji labarin.
6 Sai samari suka tashi suka nannaɗe jikinsa da yadi kuma suka fitar da shi waje suka binne shi.
7 Bayan wajen awa uku sai matarsa ta shigo, ba ta san abin da ya faru ba.
8 Bitrus ya ce mata: “Ki gaya mini, wannan ne dukan kuɗin da kuka sayar da filin?” Sai ta ce: “E, dukan kuɗin ke nan.”
9 Bitrus ya ce mata: “Me ya sa ku biyu kuka haɗa baki don ku gwada ruhun Jehobah?* Ga mutanen da suka binne maigidanki a ƙofa, za su ɗauke ki su fitar da ke.”
10 Nan take sai ta faɗi a gabansa ta mutu. Da samarin suka shigo, sai suka same ta a mace, kuma suka fitar da ita suka binne ta a gefen maigidanta.
11 Sai tsoro ya kama kowa a ikilisiyar da dukan waɗanda suka ji labarin abubuwan nan da suka faru.
12 Ƙari ga haka, manzannin sun ci-gaba da yin alamu da abubuwan ban mamaki da yawa a tsakanin mutanen, kuma dukansu sukan taru a Rumfar Sulemanu.
13 A gaskiya, sauran mutanen suna jin tsoron yin tarayya da su, duk da haka mutane da yawa suna faɗin abubuwa masu kyau game da su.
14 Ƙari ga haka, masu ba da gaskiya ga Ubangiji sun ci-gaba da ƙaruwa, da maza da mata masu yawan gaske.
15 Har ma mutane suna fitar da marasa lafiya a kan tituna kuma su kwantar da su a ƙananan gadaje da tabarma. Domin saꞌad da Bitrus yake wucewa, inuwarsa ta bi kan wasunsu.
16 Sai mutane da yawa suna ta zuwa daga garuruwa da ke kewayen Urushalima, suna kawo marasa lafiya da waɗanda aljannu suke damunsu. Kuma aka warkar da kowannensu.
17 Amma shugaban firistoci ya tashi da dukan waɗanda suke tare da shi, wato ꞌyan ƙungiyar Sadukiyawa, domin suna kishin manzannin sosai.
18 Kuma suka kama manzannin, suka saka su a kurkuku.
19 Amma da dare, malaꞌikan Jehobah* ya buɗe ƙofofin kurkukun, ya fitar da su kuma ya ce musu:
20 “Ku je ku tsaya a cikin haikali, kuma ku ci-gaba da gaya wa mutane dukan saƙon nan na rai.”
21 Da suka ji hakan, sai suka shiga haikalin da wayewar gari kuma suka soma koyarwa.
Saꞌad da shugaban firistocin da waɗanda suke tare da shi suka taru, sai suka kira dukan membobin Sanhedrin* da dukan taron dattawa na ꞌyaꞌyan Israꞌila. Kuma suka aika saƙo zuwa kurkuku cewa a kawo manzannin gabansu.
22 Amma da masu tsaron suka isa kurkukun, ba su sami kowa ba. Sai suka dawo suka ba da labarin,
23 suna cewa: “Mun sami kurkukun a kulle da kyau, masu gadin kuma suna gadin ƙofofin, amma da muka buɗe, ba mu ga kowa a ciki ba.”
24 Da shugaban masu gadin haikalin da manyan firistocin suka ji hakan, sai suka rikice sosai, suna tunanin abin da wannan zai jawo.
25 Amma wani ya zo ya gaya musu cewa: “Ga shi, mutanen da kuka saka a kurkuku suna haikali, suna tsaye suna koyar da mutane.”
26 Sai shugaban masu gadin da jamiꞌansa suka je suka kawo su. Amma ba su kama su da ƙarfi da yaji ba domin suna tsoro kada mutane su jejjefe su da duwatsu.
27 Sai suka kawo su a gaban membobin Sanhedrin.* Kuma shugaban firistoci ya yi musu magana
28 ya ce: “Mun ja muku kunne sosai kada ku ƙara koyarwa cikin sunan nan, amma ga shi kun cika Urushalima da koyarwarku, kuma niyyarku ita ce ku sa alhakin jinin mutumin nan a kanmu.”
29 Amma Bitrus da sauran manzannin suka amsa musu suka ce: “Dole ne mu yi wa Allah biyayya a matsayin sarki maimakon mutane.
30 Allahn kakanninmu ya ta da Yesu wanda kuka kashe ta wurin rataye shi a kan gungume.*
31 Allah ya ɗaukaka wannan zuwa matsayin Shugaba da kuma Mai Ceto a hannun damansa, domin ya buɗe wa mutanen Israꞌila hanyar tuba kuma a gafarta zunubansu.
32 Mu shaidu ne ga waɗannan abubuwa, haka ma ruhu mai tsarki, wanda Allah ya ba wa masu yi masa biyayya a matsayin sarki.”
33 Da suka ji haka, sai suka yi fushi sosai kuma suka so su kashe su.
34 Amma wani Bafarisi mai suna Gamaliyel ya tashi a tsakanin membobin Sanhedrin,* shi mai koyar da Doka* ne da dukan mutane suke daraja sosai. Sai ya ba da umurni cewa a fitar da su waje na ɗan lokaci.
35 Sai ya ce musu: “Mutanen Israꞌila, ku yi hankali fa da abin da kuke so ku yi wa mutanen nan.
36 Alal misali, kafin kwanakin nan, Tudas ya taso kuma yana cewa shi wani mutum ne mai muhimmanci, kuma mutane da yawa, wajen ɗari huɗu suka zama mabiyansa. Amma aka kashe shi kuma mabiyansa suka watse, hakan ya kawo ƙarshensu.
37 Bayan wannan, Yahuda wani mutumin Galili ya taso a kwanakin da ake ƙirga mutane* kuma ya sa mutane sun zama mabiyansa. Shi ma ya hallaka, kuma dukan masu bin sa suka watse.
38 Don haka ina gaya muku, ku fita daga harkar mutanen nan, ku bar su kawai, idan abin da suke ƙulla ko aikinsu na mutum ne, zai zo ga ƙarshe;
39 amma idan daga wurin Allah ne, ba za ku iya kawar da su ba. Idan ba haka ba, za ku zama masu faɗa da Allah.”
40 Da jin haka, sai suka bi shawararsa, kuma suka kira manzannin suka yi musu bulala. Sai suka ja musu kunne su daina yin magana cikin sunan Yesu, kuma suka sake su.
41 Sai manzannin suka fita daga gaban membobin Sanhedrin* suna farin ciki, domin sun cancanci a wulaƙanta su saboda sunan Yesu.
42 Kuma a kowace rana a haikali da gida-gida, sun ci-gaba da koyarwa da shelar labari mai daɗi game da Kristi, Yesu.
Hasiya
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Sanhedrin shi ne Kotun Ƙolin Yahudawa. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Sanhedrin shi ne Kotun Ƙolin Yahudawa. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ko kuma “itace.”
^ Sanhedrin shi ne Kotun Ƙolin Yahudawa. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ko kuma “Dokar Musa.”
^ Ko kuma “ƙidaya.”
^ Sanhedrin shi ne Kotun Ƙolin Yahudawa. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.