Ayyukan Manzanni 4:1-37
4 Yayin da su biyun suke magana da mutanen, sai firistoci da shugaban masu gadin haikali da Sadukiyawa suka zo suka same su.
2 Suna fushi domin manzannin suna koyar da mutanen kuma suna shela a fili yadda aka ta da Yesu.
3 Sai suka kama su, suka kulle su har sai washegari, domin yamma ta riga ta yi.
4 Amma, da yawa daga cikin mutanen da suka saurari jawabinsu sun ba da gaskiya, kuma adadin maza da suka ba da gaskiya ya kai wajen dubu biyar.
5 Washegari, shugabanninsu, da dattawa, da kuma marubuta suka taru a Urushalima,
6 tare da Anas babban firist, da Kayafas, da Yohanna, da Alekzanda da kuma dukan dangin babban firist ɗin.
7 Sai suka sa Bitrus da Yohanna suka tsaya a tsakiyarsu, kuma suka fara yi musu tambaya suna cewa: “Da wane iko ne, ko kuma a cikin sunan wane ne kuka yi wannan abin?”
8 Sai Bitrus cike da ruhu mai tsarki ya ce musu:
“Ku shugabannin mutane da kuma dattawa,
9 idan kuna mana bincike yau game da alherin da aka yi ma wani gurgu, kuma kuna so ku san wanda ya warkar da mutumin nan,
10 bari dukanku da kuma dukan mutanen Israꞌila su san cewa a cikin sunan Yesu Kristi mutumin Nazaret, wanda kuka kashe a kan gungume, amma Allah ya ta da shi daga mutuwa, ta wurinsa ne wannan mutumin da ke tsaye a gabanku ya sami cikakkiyar lafiya.
11 Wannan shi ne ‘dutsen da ku magina kuka ɗauka cewa ba shi da amfani, amma ya zama dutse* mafi amfani a ginin.’
12 Ƙari ga haka, ban da shi babu wanda zai iya ceton mu, domin babu wani suna a ƙarƙashin sama da aka bayar a tsakanin mutane wanda ta wurinsa ne za mu iya samun ceto.”
13 Da suka ga yadda Bitrus da Yohanna suka yi magana babu tsoro, kuma suka gano cewa su marasa ilimi* ne da kuma talakawa, sun yi mamaki sosai. Sai suka soma gane cewa mutanen nan suna tare da Yesu a dā.
14 Yayin da suke ganin mutumin da aka warkar yana tsaye tare da manzannin, sai suka rasa abin da za su ce.
15 Sai suka umurce su su fita daga wurin taro na Sanhedrin,* kuma suka soma shawara da juna,
16 suna cewa: “Mene ne za mu yi da mutanen nan? Domin an yi abin ban mamaki ta wurinsu, kuma dukan mazaunan Urushalima sun san da hakan, ba za mu iya yin mūsun sa ba.
17 Don kada wannan abin ya ƙara yaɗuwa a tsakanin mutane, mu ja musu kunne, kuma mu gaya musu cewa kada su ƙara yi wa kowa magana cikin wannan sunan.”
18 Sai suka kira su kuma suka umurce su cewa kada su ƙara ce kome, ko su koyar da mutane cikin sunan Yesu.
19 Amma, Bitrus da Yohanna sun amsa musu suka ce: “Ku yi tunani da kanku ko zai dace a gaban Allah mu saurare ku maimakon mu saurari Allah.
20 Mu kam, ba za mu iya yin shuru a kan abin da muka ji, kuma muka gani ba.”
21 Bayan da suka ƙara ja musu kunne, sai suka sake su, domin ba su ga wani dalilin da zai sa su hukunta su ba, kuma dukan mutanen suna ɗaukaka Allah domin abin da ya faru.
22 Ƙari ga haka, mutumin nan da aka warkar ta wurin alꞌajibi, ya fi shekara arbaꞌin.
23 Bayan da aka sake su, sai suka je wurin mutanensu kuma suka gaya musu abin da manyan firistoci da dattawa suka faɗa musu.
24 Da suka ji hakan, sai suka ɗaga muryoyinsu ga Allah da nufi ɗaya, suna cewa:
“Ubangiji Mai Iko Duka, kai ne ka yi sama, da ƙasa, da kuma teku da dukan abubuwa da ke cikinsu,
25 ta wurin ruhu mai tsarki ka yi magana ta bakin bawanka, wato kakanmu Dauda, cewa: ‘Me ya sa alꞌummai suka ta da hayaniya, kuma mutane suna tunanin banza?
26 Sarakunan duniya sun yi shirin yaƙi, shugabanninsu kuma sun haɗa kai, suna gāba da Jehobah* da kuma wanda ya zaɓa.’*
27 A gaskiya, Hirudus,* da Buntus Bilatus, da mutanen alꞌummai, da Israꞌilawa sun haɗa kai a birnin nan sun yi gāba da bawanka Yesu wanda ka zaɓa,
28 don su yi abin da ka faɗa zai faru bisa ga ikonka da kuma nufinka.
29 Yanzu kuma, Ya Jehobah,* ka dubi yadda suke ƙoƙarin tsoratar da mu, ka taimaka wa bayinka su ci-gaba da faɗin kalmarka da ƙarfin zuciya,
30 kuma ka miƙa hannunka na warkarwa, ka kuma sa alamu, da abubuwan ban mamaki su faru ta wurin sunan bawanka mai tsarki Yesu.”
31 Bayan da suka yi adduꞌa da dukan zuciyarsu, sai wurin da suka taru ya girgiza, kuma aka cika dukansu da ruhu mai tsarki, suka yi ta faɗin kalmar Allah babu tsoro.
32 Ƙari ga haka, taron jamaꞌa da suka ba da gaskiya suna da haɗin kai a zuciyarsu da kuma tunaninsu, kuma babu wani a cikinsu da yake ganin abubuwan da yake da su nasa ne, amma dukansu suna raba abubuwan da suke da su tare.
33 Kuma da iko mai girma, manzannin sun ci-gaba da ba da shaida game da tashin Ubangiji Yesu daga mutuwa. Kuma dukansu sun sami alheri mai yawa.
34 Har ba wanda ya rasa wani abu a cikinsu, domin dukan masu gonaki da gidaje sun sayar da su kuma suka kawo kuɗin,
35 suna ajiye a gaban manzannin kuma ana rarraba wa kowa bisa ga bukatarsa.
36 Sai Yusufu wanda manzannin suke kiran sa da suna, Barnabas (idan aka fassara sunan, yana nufin, “Ɗan Taꞌaziyya”), shi Balawi ne da ya fito daga Saifrus,
37 yana da fili, sai ya sayar da filin ya kawo kuɗin ya ajiye a gaban manzannin.
Hasiya
^ Akan saka wannan dutsen a kwana, inda bango 2 suke haɗuwa.
^ Wannan yana nufin cewa ba su je makarantar da malaman addinai suke zuwa ba. Ba wai ba su iya karatu da rubutu ba ne.
^ Sanhedrin shi ne Kotun Ƙolin Yahudawa. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ko kuma “Kristi.”
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.