Ayyukan Manzanni 26:1-32

  • Bulus ya kāre kansa a gaban Agirifa (1-11)

  • Bulus ya bayyana yadda ya zama Kirista (12-23)

  • Abin da Festus da Agirifa suka gaya wa Bulus (24-32)

26  Sai Agirifa ya ce wa Bulus: “An ba ka izini ka kāre kanka.” Kuma Bulus ya miƙa hannunsa ya soma magana yana cewa: 2  “Ya Sarki Agirifa, ina farin ciki cewa a gabanka ne zan kāre kaina a yau daga dukan zargi da Yahudawa suke mini, 3  musamman ma don kana da ƙwarewa a kan dukan alꞌadun Yahudawa da kuma abubuwan da suke gardama a kai. Saboda haka, ina roƙon ka, ka yi haƙuri ka saurare ni. 4  “Hakika, dukan Yahudawa sun san irin rayuwar da na yi tun ina matashi a tsakanin mutanena* da kuma a Urushalima. 5  Yahudawan sun san ni sosai a dā, idan a shirye suke su faɗi gaskiya, za su faɗi cewa na yi rayuwata a matsayin Bafarisi, kuma a addininmu, Farisiyawa sun fi sauran Yahudawa nace wa bin Doka.* 6  Amma yanzu ana yi mini shariꞌa domin ina da bege cewa alkawarin da Allah ya yi wa kakanninmu zai cika; 7  wannan alkawari ne da kabilu goma sha biyu namu suke begen ganin cikarsa ta wurin bauta wa Allah da dukan zuciyarsu dare da rana. Domin wannan begen ne Yahudawa suke zargi na, Ya Sarki. 8  “Me ya sa yake muku wuya ku yarda cewa Allah zai iya ta da waɗanda suka mutu? 9  Ni ma a dā ina ganin ya dace in yi duk abin da zan iya don in yi gāba da sunan Yesu mutumin Nazaret. 10  Abin da na yi ke nan a Urushalima har na kulle tsarkaka da yawa a cikin kurkuku, domin na sami izini daga manyan firistoci; kuma a lokacin da ake so a kashe su, na goyi bayan hakan. 11  Na tsananta musu sau da yawa a dukan majamiꞌu, don in sa su dole su bar imaninsu; kuma tun da yake ina fushi da su sosai, har na je wasu birane don in tsananta musu. 12  “Yayin da nake tafiya zuwa Damaskus don in yi hakan da izini da kuma umurnin da na samu daga manyan firistoci, 13  da tsakar rana, Ya Sarki, saꞌad da nake kan hanya sai na ga wani haske daga sama fiye da hasken rana, yana haskakawa kewaye da ni da abokan tafiyata. 14  Kuma saꞌad da dukanmu muka faɗi a ƙasa, sai na ji wata murya ta yi mini magana a Ibrananci tana cewa: ‘Shawulu, Shawulu, me ya sa kake tsananta mini? Kana ba kanka wahala ne da kake gāba* da ni.’ 15  Amma na ce: ‘Wane ne kai Ubangiji?’ Sai Ubangiji ya ce mini: ‘Ni ne Yesu, wanda kake tsananta wa. 16  Amma ka tashi ka tsaya. Na bayyana a gare ka don in zaɓe ka ka zama bawana, kuma ka ba da shaidar abubuwan da ka gani da kuma abubuwan da zan sa ka gani game da ni. 17  Kuma zan cece ka daga mutanen nan da kuma alꞌummai da zan aike ka wurinsu 18  domin ka buɗe idanunsu kuma ka juyo su daga duhu zuwa haske, daga ikon Shaiɗan zuwa wurin Allah, domin a iya gafarta zunubansu kuma su sami gādo tare da waɗanda aka tsarkake su ta wurin bangaskiyarsu a gare ni.’ 19  “Saboda haka, Ya Sarki Agirifa, ban yi rashin biyayya ga wahayin nan daga sama ba, 20  amma na yi waꞌazi da farko ga waɗanda suke Damaskus, saꞌan nan ga waɗanda suke Urushalima, da dukan yankunan Yahudiya, da kuma ga alꞌummai ma, na yi ta gaya musu cewa ya kamata su tuba kuma su juyo ga Allah ta wurin yin ayyukan da za su nuna cewa sun tuba. 21  Abin da ya sa Yahudawa suka kama ni a haikali ke nan kuma suka yi ƙoƙari su kashe ni. 22  Amma, domin Allah ya taimaka mini, na ci-gaba da ba da shaida har wa yau ga yaro da babba, kuma babu abin da nake koyarwa ban da abubuwan da Annabawa da kuma Musa suka ce za su faru— 23  wato Kristi zai sha wahala, kuma tun da yake shi ne mutum na farko da za a ta da daga mutuwa, zai yi shelar haske ga waɗannan mutane da kuma alꞌummai.” 24  Yayin da Bulus yake faɗan abubuwan nan don ya kāre kansa, sai Festus ya ɗaga murya ya ce: “Bulus ka haukace fa! Yawan ilimi ya sa ka haukace!” 25  Amma Bulus ya ce: “Ban haukace ba, Ya Mai Girma Festus, abin da nake faɗa gaskiya ne kuma ina cikin hankalina. 26  A gaskiya, sarkin da nake masa magana a sake ya san abubuwan nan; ina da tabbaci cewa ya san dukan abubuwan nan, domin babu ɗayansu da aka yi a ɓoye. 27  Ya Sarki Agirifa, ka gaskata da abin da annabawa suka rubuta? Na san cewa ka gaskata da abin da suka rubuta.” 28  Amma Agirifa ya ce wa Bulus: “A cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, za ka rinjaye ni in zama Kirista.” 29  Sai Bulus ya ce: “Ko a cikin ƙanƙanin lokaci ko a dogon lokaci, ina adduꞌa cewa Allah ya sa ba kai kaɗai ba, har ma dukan waɗanda suke sauraro na a yau su zama kamar yadda nake, amma ba na so a saka musu sarƙoƙi kamar ni.” 30  Sai sarkin ya tashi har da gwamna da Banis da mutanen da suke zaune tare da su. 31  Yayin da suke barin wurin, sai suka soma gaya wa juna cewa: “Abin da mutumin nan yake yi bai isa a kashe shi ko a ɗaure shi a kurkuku ba.” 32  Sai Agirifa ya ce wa Festus: “Da mutumin nan bai ɗaukaka ƙara zuwa wurin Kaisar ba, da an sake shi.”

Hasiya

Ko kuma “alꞌummata.”
Ko kuma “Dokar Musa.”
A yaren Girka, “yayin da kake buga sanda.” Wannan sanda ce mai tsinin baki. Da irin wannan sandar ne ake wa dabbobi ja-gora.