Ayyukan Manzanni 20:1-38
20 Da rikicin ya kwanta, sai Bulus ya aika a kira almajiran, bayan ya ƙarfafa su kuma ya yi musu ban kwana, sai ya soma tafiya zuwa Makidoniya.
2 Bayan da ya bi ta yankunan kuma ya furta kalmomi da yawa na ƙarfafa ga waɗanda suke wurin, sai ya isa Girka.
3 Ya zauna a wurin har na watanni uku, amma da yake Yahudawan suna shirya masa mugunta saꞌad da yake shirin shiga jirgin ruwa zuwa Siriya, sai ya yanke shawarar komawa ta Makidoniya.
4 Waɗanda suka raka shi su ne, Sufata ɗan Farus na Biriya, da Aristarkus, da Sakundus daga Tasalonika, da Gayus daga Darbe, da Timoti, daga yankin Asiya kuma akwai Tikikus, da Tarofimus.
5 Waɗannan mutanen sun sha gaba kuma suna jiran mu a Toruwas.
6 Sai muka tashi daga Filibi a jirgin ruwa bayan Bikin Burodi Marar Yisti, a cikin kwana biyar mun isa wurinsu a Toruwas, kuma mun yi kwanaki bakwai a wurin.
7 A ranar farko ta mako, saꞌad da muka taru don mu ci abinci, sai Bulus ya soma yi musu jawabi da yake zai tafi washegari; kuma ya yi ta yin jawabi har zuwa tsakar dare.
8 Akwai fitilu da yawa a wurin da muka taru a ɗakin da ke sama.
9 Da Bulus ya ci-gaba da magana, sai barci mai zurfi ya kama wani saurayi mai suna Yutikus da ke zaune a kan wundo. Da yake barcin, sai ya faɗo daga hawa na uku. Da suka sauko wurinsa sai suka ga ya mutu.
10 Amma Bulus ya sauko ƙasa, ya kwanta a kansa kuma ya rungume shi, sai ya ce: “Ku daina damuwa, don yana da rai.”
11 Sai Bulus ya haura sama ya ɗauki abincin* ya soma ci. Ya ci-gaba da yin magana har gari ya waye, sai ya tafi.
12 Sai suka ɗauki yaron da rai, kuma hakan ya taꞌazantar da su ba kaɗan ba.
13 Mu kuwa muka yi gaba zuwa inda jirgin ruwan yake, muka tafi Assos, amma Bulus ya yanke shawarar takawa da ƙafa. Dā ma mun shirya za mu ɗauki Bulus a wurin kamar yadda ya gaya mana.
14 Da ya same mu a Assos, sai muka ɗauke shi a jirgin ruwan muka tafi Mitilin.
15 Washegari muka bar wurin da jirgin ruwa, muka isa kusa da Kiyos. Kwana ɗaya bayan haka, sai muka ɗan tsaya a Samos, washegarin kuma muka isa Miletus.
16 Bulus ya yanke shawarar wuce Afisa da jirgin ruwa don kada ya ɓata lokaci a yankin Asiya, gama yana sauri ya isa Urushalima a Ranar Bikin Fentikos idan zai yiwu.
17 Amma daga Miletus, Bulus ya aika saƙo zuwa Afisa cewa a kira dattawan ikilisiyar.
18 Da suka zo wurinsa, sai ya ce musu: “Kun san irin halayen da na nuna tun daga ranar farko da na shiga yankin Asiya,
19 na yi wa Ubangiji hidima da dukan sauƙin kai tare da hawaye da tsanantawa da na sha, domin ƙulle-ƙullen da Yahudawa suka yi mini.
20 Duk da haka, ban fasa gaya muku abubuwan da za su amfane ku, da koyar da ku a fili da kuma gida-gida ba.
21 Amma na yi waꞌazi sosai ga Yahudawa da kuma mutanen Girka, cewa su tuba ga Allah kuma su ba da gaskiya ga Ubangijinmu Yesu.
22 Amma yanzu ta wurin ja-gorancin ruhu,* za ni Urushalima duk da cewa ban san abin da zai faru da ni a wurin ba,
23 Na dai san cewa a kowane birni, ruhu mai tsarki ya ci-gaba da gaya mini cewa kurkuku da tsanantawa suna jira na.
24 Duk da haka, ban ɗauki raina da wani muhimmanci ba, idan dai zan kammala tserena, da kuma hidimar da na karɓa daga wurin Ubangiji Yesu, cewa in ba da shaida sosai a kan labari mai daɗi na alherin Allah.
25 “Yanzu na san cewa, ba ko ɗaya daga cikinku da na yi ma waꞌazin Mulkin Allah da zai sake ganina.
26 Saboda haka, a yau na kira ku ku shaida cewa babu alhakin jinin kowa a kaina,
27 gama ban ɓoye muku wani abu ba, amma na gaya muku dukan nufin Allah.
28 Ku lura da kanku da kuma dukan tumakin da ruhu mai tsarki ya naɗa ku ku zama masu kula a tsakaninsu, don ku yi kiwon* ikilisiyar Allah da ya saya da jinin Ɗansa.
29 Na san cewa bayan na tafi, wasu mugayen ƙyarketai* za su shigo a tsakaninku kuma ba za su bi da tumakin da tausayi ba.
30 Ko a cikinku ma, mutane za su taso su yi ta maganganun ƙarya don su sa almajiran Yesu su soma bin su.
31 “Saboda haka, ku zauna da shiri, ku tuna cewa shekara uku, dare da rana, ban taɓa fasa yi wa kowannenku gargaɗi ba, har da hawaye.
32 To yanzu, na miƙa ku ga hannun Allah, kuma bari kalmar alherinsa ta kiyaye ku, kalmar kuwa za ta ƙarfafa ku kuma za ta sa ku samu gādo a tsakanin dukan tsarkaka.
33 Ban taɓa kwaɗayin azurfa, ko zinariya, ko tufafin wani ba.
34 Ku da kanku kun san cewa hannayen nan nawa, sun biya mini bukatuna da kuma bukatun waɗanda suke tare da ni.
35 A cikin dukan abubuwa, na nuna muku ta wurin ayyukana, yadda ya kamata ku taimaka wa marasa ƙarfi, kuma dole ku tuna da abin da Ubangiji Yesu ya faɗa cewa: ‘Bayarwa tana sa farin ciki fiye da karɓa.’”
36 Bayan ya faɗi abubuwan nan, sai ya durƙusa tare da dukansu kuma ya yi adduꞌa.
37 A gaskiya, dukansu sun yi kuka sosai, suka rungumi Bulus kuma suka sumbace shi.
38 Abin da ya fi sa su baƙin ciki shi ne maganarsa da ya ce ba za su ƙara ganin fuskarsa ba. Sai suka raka shi zuwa jirgin ruwa.
Hasiya
^ A yaren Girka, “ya karya burodi.”
^ Ko kuma “ruhu mai tsarki ya tilasta mini.”
^ Ko kuma “kula da.”
^ Wasu dabbobin daji da suke kama da karnuka.