Ta Farko Zuwa ga Yohanna 5:1-21
5 Duk wanda ya ba da gaskiya cewa Yesu shi ne Kristi, shi ɗan Allah ne, kuma duk wanda yake ƙaunar mahaifi, yana kuma ƙaunar ꞌyaꞌyan mahaifin.
2 Ta haka ne za mu san cewa muna ƙaunar ꞌyaꞌyan Allah, idan muna ƙaunar Allah kuma muna bin dokokinsa.
3 Gama ga abin da ƙaunar Allah take nufi, cewa mu bi dokokinsa; kuma dokokinsa ba su da wuyan bi,*
4 domin duk wanda shi ɗan Allah ne, ya yi nasara da duniya. Kuma bangaskiyarmu ce ta sa muka yi nasara da duniya.
5 Wane ne zai iya yin nasara da duniya? Shin ba wanda ya ba da gaskiya cewa Yesu ne Ɗan Allah ba?
6 Shi ne wanda ya zo ta wurin ruwa da kuma jini, wato Yesu Kristi, ba ta wurin ruwa kawai ba, amma ta wurin ruwa da kuma jini. Ruhun kuma yana ba da shaida, domin ruhun gaskiya ne.
7 Gama akwai abubuwa uku da ke ba da shaida:
8 ruhun, da ruwan, da jinin; abubuwa ukun nan kuma manufarsu ɗaya ce.
9 Idan muka karɓi shaidar mutane, ai shaidar Allah ta fi girma. Domin wannan ita ce shaidar da Allah ya bayar, wato, shaidar da ya bayar game da Ɗansa.
10 Mutumin da yake ba da gaskiya ga Ɗan Allah yana da shaidar nan a zuciyarsa. Wanda ba ya ba da gaskiya ga Allah, ya mai da Allah maƙaryaci, domin bai ba da gaskiya ga shaidar da Allah ya bayar game da Ɗansa ba.
11 Wannan ita ce shaidar, cewa Allah ya ba mu rai na har abada, kuma ta wurin Ɗansa ne yake ba da wannan rai.
12 Wanda yake da haɗin kai da Ɗan yana da wannan rai; amma duk wanda ba shi da haɗin kai da Ɗan Allah, ba shi da wannan rai.
13 Na rubuta muku abubuwan nan ne domin ku sani cewa kuna da rai na har abada, ku da kuka ba da gaskiya ga sunan Ɗan Allah.
14 Kuma muna da wannan tabbacin game da Allah, cewa ko da mene ne muka roƙa da ya yi daidai da nufinsa, yana saurarar mu.
15 Kuma idan mun san cewa zai saurare mu idan muka roƙe shi kowane abu, mun san cewa za mu samu abubuwan da muka roƙa, tun da yake mun roƙe shi abubuwan.
16 Idan wani ya ga ɗanꞌuwansa yana yin zunubi wanda ba zai kai ga mutuwa ba, zai yi masa adduꞌa kuma Allah zai ba shi rai, wato, ga waɗanda ba sa yin zunubin da zai kai ga mutuwa. Akwai zunubin da zai kai ga mutuwa. Ba irin wannan zunubin ne na ce masa ya yi adduꞌa a kai ba.
17 Dukan rashin adalci zunubi ne, duk da haka, akwai zunubin da ba ya kai ga mutuwa.
18 Mun san cewa duk wanda shi ɗan Allah ne ba ya ci-gaba da yin zunubi, amma wanda shi ɗan Allah* ne yana lura da shi, kuma mugun nan ba zai iya riƙe shi ba.
19 Mun san cewa mu na Allah ne, amma dukan duniya tana ƙarƙashin ikon mugun nan.
20 Ƙari ga haka, mun san cewa Ɗan Allah ya zo, kuma ya ba mu ganewa don mu iya sanin wanda shi ne gaskiya. Kuma muna da haɗin kai da wanda shi ne gaskiya, ta wurin Ɗansa Yesu Kristi. Wannan shi ne Allah na gaskiya da kuma rai na har abada.
21 Ya ku ƙananan yara, ku kiyaye kanku daga gumaka.

