Ta Farko Zuwa ga Timoti 3:1-16
3 Zancen nan gaskiya ne cewa: Idan mutum yana yin iya ƙoƙarinsa don ya zama mai kula,* yana marmarin yin aiki mai kyau ne.
2 Saboda haka, dole ne mai kulan ya zama marar laifi, mijin mace ɗaya, mai kamun kai, mai sanin yakamata, mai yin abubuwa cikin tsari, mai karɓan baƙi, mai iya koyarwa,
3 ba mai buguwa ba, ba mai faɗa ba, ba mai nacewa a kan raꞌayinsa ba, ba mai son gardama ba, ba mai son kuɗi ba,
4 ya zama wanda yake yi wa iyalinsa ja-goranci a hanya mai kyau, yana da yara da suke biyayya da kuma nuna ban-girma a kowace hanya
5 (gama idan mutum bai san yadda zai yi wa iyalinsa ja-goranci ba, ta yaya zai iya kula da ikilisiyar Allah?),
6 ba sabon tuba ba, domin kada ya soma girman kai kuma ya faɗa cikin hukuncin da aka yanke ma Ibilis.
7 Ƙari ga haka, dole ne kuma mutanen waje su ba da shaida mai kyau a kansa domin kada ya jawo wa kansa kunya kuma ya faɗa cikin tarkon Ibilis.
8 Haka ma, bayi masu hidima su zama waɗanda ba sa wasa,* ba sa baki biyu,* ba sa yawan shan ruwan inabi, ba sa kwaɗayin samun ƙazamar riba,
9 suna riƙe da sirri mai tsarki, wato bangaskiya, tare da lamiri mai tsabta.
10 Ƙari ga haka, a gwada su tukuna don a ga ko sun cancanta; bayan haka, sai a bar su su yi hidima, muddin ba wanda zai zarge su da yin wani abu.
11 Mata ma su zama masu hankali, marasa ɓata sunan wasu, masu kamun kai, masu aminci a dukan abubuwa.
12 Bayi masu hidima su zama masu mata ɗaya, suna yi wa yaransu da kuma iyalinsu ja-goranci a hanya mai kyau.
13 Gama mazajen da suke hidima a hanya mai kyau suna samar ma kansu suna mai kyau da kuma ꞌyanci sosai na yin magana game da bangaskiyarsu ga Kristi Yesu.
14 Ina rubuta maka waɗannan abubuwan ko da yake ina sa ran zuwa wurinka nan ba da daɗewa ba,
15 amma idan ban iya zuwa da wuri ba, hakan zai taimaka maka ka san yadda za ka bi da kanka a iyalin Allah, wanda shi ne ikilisiyar Allah mai rai, kuma ikilisiyar ce ginshiƙi da tushen gaskiya.
16 A gaskiya, sirri mai tsarkin nan game da yadda za a yi ibada da dukan zuciya yana da muhimmanci sosai cewa: ‘An bayyana shi a cikin jiki, da ya koma cikin ruhu, Allah ya ce da shi mai adalci, ya bayyana ga malaꞌiku, an yi waꞌazi game da shi a tsakanin alꞌummai, kuma an ba da gaskiya gare shi a duniya, an marabce shi a sama da ɗaukaka.’

