Maꞌanar Kalmomi da Ke Littafi Mai Tsarki
A B C D Ɗ F G H I J K Ƙ L M N P R S T W Y Z
A
-
Abikuriya.
Ya kafa sashen koyar da ilimin duniya da ke koyar da mutane cewa su yi iya abin da za su iya yi domin su ji daɗin rayuwa.—A.M 17:18.
-
Abin ƙona turare.
An yi shi ne da zinariya, ko azurfa, ko kuma tagulla, an yi amfani da shi a tentin saduwa da kuma haikali don ƙona turare, an kuma yi amfani da shi don cire gawayi a bagaden hadaya da kuma lagwanin da ya ƙone a sandar riƙe fitila ta zinariya. Ana kuma kiran sa abin riƙe wuta.—Fit 37:23; 2Tr 26:19; Ibr 9:4.
-
Abincin Yamma na Ubangiji.
Abinci ne da ya haɗa da burodi marar yisti da kuma ruwan inabi, waɗanda suke wakiltar jikin Kristi da jininsa. Yana kuma nufin taron tunawa da mutuwar Yesu. Da yake wannan taro ne da Nassi ya umurci Kristoci su ci-gaba da yi, ya dace da ake kiran sa “Abincin Yamma na Ubangiji.”—1Ko 11:20, 23-26.
-
Abubuwan alꞌajibi; Manyan ayyuka.
Ayyuka ne da mutane ba za su iya yi ba, sai dai da taimakon wanda yake da iko fiye da na mutane. A wasu lokuta, ana amfani da kalmonin nan “alamu,” da “abubuwan ban mamaki” a cikin Littafi Mai Tsarki, kuma suna nufin abubuwan alꞌajibi.—Mat 11:20; A.M 4:22; Ibr 2:4.
-
Abyss.
-
Adalci.
A cikin Nassosi, yana nufin abin da Allah yake ganin ya dace da kuma abin bai dace ba.—Far 15:6; M.S 6:25; Zaf 2:3; Mat 6:33.
-
Akaya.
A Nassosin Girkanci na Krista yana yankin Roma da ke kudancin Girka kuma Korinti ne babban birninsa.—A.M 18:12.
-
Akwatin yarjejeniya.
Wannan wani akwati ne da aka yi da itacen akashiya kuma an rufe jikinsa ciki da waje da zinariya. An ajiye shi a Wuri Mafi Tsarki na tentin saduwa, daga baya kuma an ajiye shi a Wuri Mafi Tsarki na haikalin da Sulemanu ya gina. An yi murfin akwatin da zinariya zalla, kuma a kan murfin akwai siffofi guda biyu na malaꞌikun da ake kira cerub da suke fuskantar juna. Muhimman abubuwan da ke cikin akwatin su ne alluna biyu da ke ɗauke da Dokoki Goma.—M.S 31:26; 1Sr 6:19; Ibr 9:4.
-
Alama.
-
Alfa da Omega.
-
Alheri.
Kalmar nan a yaren Girka tana nufin abin da ake amincewa da shi kuma yana da kyau. Ana yawan amfani da ita saꞌad da ake magana game da kyautar da aka bayar da kuma yadda aka ba da kyautar. Idan kuma ana magana game da alherin Allah ne, kalmar tana nufin kyautar da Allah ya bayar da dukan zuciyarsa ba tare da sa rai cewa za a ba shi wani abu ba. Don haka, wannan yana nuna yadda Allah yake ba da kyauta da dukan zuciyarsa da kuma yadda yake nuna wa ꞌyanꞌadam alheri. Ana kuma fassara kalmar yaren Girkan nan zuwa “kyautar da aka bayar cikin alheri.” Idan an ba wa mutum irin kyautar nan, ba wai hakkinsa ba ne ko kuma ya cancanci a ba shi kyautar ba ne. A maimakon haka, wanda ya ba da wannan kyautar mai bayarwa ne sosai.—2Ko 6:1; Afi 1:7.
-
Aljanna.
Wurin hutu mai kyau da ke da furanni da itatuwa da kuma ꞌyaꞌyan itatuwa. Aljanna ta farko ita ce lambun Adnin, kuma Jehobah ne ya yi ta domin mace da namiji na farko. Saꞌad da Yesu yake magana da wani da ya aikata laifi da aka rataye a kan gungumen azaba kusa da shi, Yesu ya nuna cewa duniya za ta zama aljanna. A 2 Korintiyawa 12:4, an yi amfani da kalmar a matsayin aljanna ta alama, kuma a Ruꞌuya ta Yohanna 2:7, an yi amfani da kalmar saꞌad da ake magana game da aljanna ta sama.—2Ko 12:4; R.Y 2:7; Waƙ 4:13; Luk 23:43.
-
Aljanu.
Mugayen ruhohi da ba a iya gani, masu iko sosai fiye da ꞌyanꞌadam. A Farawa 6:2, an kira su “ꞌyaꞌyan Allah” kuma a Yahuda 6, an kira su ‘malaꞌiku.’ Ba a halicce su su zama mugaye ba, amma su malaꞌiku ne da suka mai da kansu abokan gāba na Allah ta wajen yi masa rashin biyayya a zamanin Nuhu da kuma goyon bayan tawaye da Shaiɗan ya yi wa Jehobah.—M.S 32:17; Luk 8:30; A.M 16:16; Yaƙ 2:19.
-
Alkawari.
Wato idan mutum ya gaya wa Allah cewa zai yi wasu abubuwa, ko zai ba da wasu kyaututtuka, ko zai yi wasu hidimomi, ko kuma zai guje ma wasu abubuwa da yin su ba laifi ba ne. Idan mutum ya ce zai yi abubuwan nan, yana da kyau ya yi hakan domin kamar rantsuwa ne ya yi.—Mat 5:33.
-
Almasihu.
A Ibrananci kalmar tana nufin “shafaffe” ko “wanda aka shafe.” Kalmar a yaren Girka shi ne “Kristi.”—Dan 9:25; Yoh 1:41.
-
Amin.
“Ya kasance hakan,” ko kuma “hakika.” An samo ta ne daga kalmar Ibrananci ʼa·manʹ, da ke nufin “kasance da aminci da tabbatacciya.” Ana amfani da “amin” wajen amincewa da rantsuwa, ko adduꞌa, ko kuma wata magana. A littafin Ruꞌuya ta Yohanna, an yi amfani da ita a matsayin laƙabi ga Yesu.—M.S 27:26; 1Tr 16:36; Rom 1:25; R.Y 3:14.
-
Annabci.
Yana nufin saƙo daga wurin Allah ko wahayi ko kuma shelar saƙon. Yana iya nufin yadda Allah yake so mutane su yi rayuwa, ko umurni, ko hukunci, ko kuma shelar wani abin da zai faru a nan gaba.—Mat 13:14; 2Bi 1:20, 21.
-
Annoba.
Duk wata cuta da ke yaɗuwa da sauri kuma za ta iya shafan mutane da yawa har ta kai ga mutuwa.—Luk 21:11.
-
Aramaik.
Wani yaren zamanin dā da ke amfani da harufa irin na Ibrananci. Mutanen Aramaya ne ainihi suke yaren, amma daga baya ya zama yaren da ake yi a fāɗin duniya wajen kasuwanci da sadarwa a daulolin Assiriya da Babila. Ƙari ga haka, yaren hukuma ne a Daular Fasiya. (Ezr 4:7) An rubuta wasu sassan littattafan Ezra, da Irmiya, da kuma Daniyel a yaren Aramaik. An yi amfani da wasu kalmomin Aramaik a Nassosin Girkanci na Krista.—Ezr 4:8–6:18; 7:12-26; Irm 10:11; Dan 2:4b–7:28; Mrk 14:36; A.M 9:36.
-
Ariyofagus.
Wani tudu mai tsayi da ke Atina a arewa maso yammacin Akurofolis. Suna ne kuma da ake kiran rukunin masu shariꞌa (kotu) da ke taro a wurin. Mabiyan Abikuriya da mabiyan Zeno masu koyar da hikimar duniya sun kawo Bulus zuwa Ariyofagus don ya bayyana imaninsa.—A.M 17:19.
-
Armageddon.
An samo kalmar ce daga kalmar Ibranancin nan Har Meghid·dohnʹ, wadda take nufin “Tudun Megiddo.” Kalmar na da alaƙa da “yaƙin da za a yi a babbar rana ta Allah Maɗaukaki.” A ranar, “sarakunan dukan duniya” za su taru don su yi yaƙi da Jehobah. (R.Y 16:14, 16; 19:11-21)—Ka duba ƘUNCI MAI GIRMA.
-
Aselgeia.—
Ka duba HALIN RASHIN KUNYA.
-
Asiya.
A Nassosin Girkanci na Krista, wannan sunan wani yankin Roma ne wanda a yau ya ƙunshi yammacin ƙasar Turkiya, da wasu tsibirai kamar Samos da Batmusa. Babban birninsa shi ne Afisa.—A.M 20:16; R.Y 1:4.
-
Azumi.
Ƙin cin abinci kwata-kwata na ɗan lokaci. Israꞌilawa sukan yi azumi a Ranar Neman Gafara, da lokacin da suke cikin damuwa, da kuma saꞌad da suke neman ja-goranci daga wurin Allah. Yahudawa sukan yi azumi sau huɗu a kowace shekara domin su tuna da wasu munanan abubuwa da suka faru da su a tarihi. Ba dole ba ne Kristoci su yi azumi.—Ezr 8:21; Ish 58:6; Mat 4:2; 9:14; Luk 18:12; A.M 13:2, 3; 27:9.
B
-
Bābā.
A zahiri yana nufin namijin da aka dandaƙe shi. A yawancin lokaci, akan naɗa irin mazajen nan su kula da fādar sarki ko kuma su kula da sarauniya da wasu matan da sarki ya ajiye (ƙwarƙwara). Kalmar kuma tana nufin namijin da ba a dandaƙe shi ba, amma kuma yana ayyuka a fādar sarki. Ana kuma amfani da kalmar a alamance saꞌad da ake magana game da ‘wanda bai yi aure ba domin Mulkin sama,’ wato wanda yake kame kansa domin ya ba da lokaci sosai ga aikin Allah.—Mat 19:12; Est 2:15; A.M 8:27.
-
Babban firist.
A wasu lokuta, ana kiran “shugaban firistoci” da wannan sunan a Nassosin Ibrananci. A Nassosin Girkanci na Krista, da alama sunan na nufin firistoci da ke da babban matsayi a tsakanin firistoci, mai yiwuwa hakan ya haɗa da tsofaffin shugabannin firistoci da kuma shugabannin rukunoni 24 na firistoci.—2Tr 26:20; Ezr 7:5; Mat 2:4; Mrk 8:31.
-
Baftisma.
-
Bagade.
Wani abu da aka gina da laƙa, ko duwatsu, ko bulo, ko kuma katako da aka rufe da ƙarfe. Ana ƙona hadayu ko kuma turaren wuta a kai don bauta. A ɗakin farko na tentin saduwa da kuma na haikali, akwai ƙaramin “bagaden zinariya” da ake ƙona turaren wuta a kai. Da katako aka yi bagaden, kuma aka rufe shi da zinariya. A farfajiya kuma, akwai babban “bagaden da aka yi da tagulla” don miƙa hadayu. Masu bautar ƙarya ma suna amfani da bagade.—Fit 39:38, 39; 1Sr 6:20; Mat 5:23, 24; Luk 1:11; A.M 17:23.
-
Bawa mai hidima.
A yaren Girka, kalmar nan di·aʹko·nos, a yawancin lokaci ana fassara ta zuwa “mai hidima” ko kuma “bawa.” “Bawa mai hidima” yana nufin wanda yake taimaka ma rukunin dattawa a ikilisiya. Dole ne mutum ya yi abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa kafin ya cancanci zama bawa mai hidima.—1Ti 3:8-10, 12.
-
Bayahude.
Sunan da ake kiran mutumin da ya fito daga kabilar Yahuda bayan da kabilu goma na Israꞌila suka ware kansu. (2Sr 16:6) Bayan da suka dawo daga bauta a Babilia, an yi amfani da kalmar don Israꞌilawa da suka fito daga kabilu dabam-dabam waɗanda suka dawo ƙasar Israꞌila. (Ezr 4:12) Daga baya, an yi amfani da wannan kalmar don a bambanta Israꞌilawa daga waɗanda suka fito daga wasu ƙasashe. (Est 3:6) Bulus ya yi amfani da sunan saꞌad da yake so ya taimaka wa mutane su san cewa a ikilisiyar Krista, ƙasar da mutum ya fito ba ta da wani muhimmanci.—Rom 2:28, 29; Gal 3:28.
-
Baꞌal.
Wani allahn mutanen Kanꞌana da ake ganin shi ne mamalakin sararin sama, da mai ba da ruwan sama, da kuma mai sa amfanin gona su yi kyau. Ana kuma kiran wasu ƙananan alloli a yankin “Baꞌal.” Wannan kalmar Ibrananci ne da ke nufin “Mamallaki; Shugaba.”—1Sr 18:21; Rom 11:4.
-
Belzebub.
Sunan da ake kiran Shaiɗan wanda shi ne yarima, ko kuma sarkin aljanu. Mai yiwuwa an samo sunan ne daga Baꞌal-zebub, wato Baꞌal da Filistiyawa suka bauta wa a Ekron.—2Sr 1:3; Mat 12:24.
-
Bikin Bukkoki.
Ana kuma kiran sa Bikin Tentuna, ko kuma Bikin Gama Girbi. Akan yi bikin ne daga ranar 15-21, ga watan Etanim na kalandar Yahudawa. Akan yi bikin ne domin girbin da Israꞌilawa suke yi a ƙarshen lokacin noma, kuma lokaci ne na murna da miƙa godiya ga Jehobah domin yadda ya albarkaci amfanin gonarsu. A kwanakin da za a yi bikin, mutanen sukan zauna a tentuna, ko kuma rumfa, kuma hakan na tuna musu yadda suka fita daga ƙasar Masar. Bikin yana ɗaya daga cikin bukukuwa uku da aka bukaci maza su je Urushalima don su yi.—Fir 23:34; Ezr 3:4; Yoh 7:2.
-
Bikin Burodi Marar Yisti.
Wannan shi ne biki na farko cikin bukukuwa uku da Israꞌilawa suke yi a kowace shekara. Ana soma bikin ne a ranar goma sha biyar ga watan Nisan, wato kwana ɗaya bayan Bikin Ƙetarewa, kuma akan ci-gaba da yin bikin har na kwanaki bakwai. Burodi marar yisti ne kawai ake ci a lokacin bikin, don tunawa da lokacin da Israꞌilawa suka fito daga ƙasar Masar.—Fit 23:15; Mrk 14:1.
-
Bikin Keɓewa.
Ranar da ake tuna yadda aka tsabtace haikali bayan da Antiyokus Efifanes ya ƙazantar da haikalin. Akan soma bikin a ranar 25 ga watan Chislev, kuma akan yi bikin kwanaki takwas.—Yoh 10:22.
-
Bikin Ƙetarewa.
Wani bikin da ake yi kowace shekara a ranar 14 ga watan Abib (daga baya an kira shi Nisan) don tunawa da yadda Jehobah ya ceci Israꞌilawa daga Masar. Ana yin bikin ne ta wurin yanka da kuma gasa ɗan rago (ko kuma akuya), wanda a lokacin akan ci shi da ganyaye masu ɗaci da kuma burodi marar yisti.—Fit 12:27; Yoh 6:4; 1Ko 5:7.
-
Buga hatsi; Wurin buga hatsi.
Wannan yana nufin yadda ake ware hatsi daga kararsa da kuma dusa; wuri ne da ake yin wannan aikin. Ana buga hatsi da sanda, amma idan yana da yawa, ana amfani da kayan aiki na musamman. Akan baza hatsi a wurin buga hatsi, sai dabbobi su ja kayan aikin a kan hatsin. Wurin buga hatsi wuri ne da ke da tsawo wanda iska ke yawan kaɗawa, kuma ya yi lebur sosai.—Fir 26:5; Ish 41:15; Mat 3:12.
-
Bulala.
A Nassosin Girkanci na Krista, yana nufin zana mutum ko kuma yi masa dūka da bulala da ke da ƙulli a bakinsa.—Yoh 19:1.
-
Burodin da ake miƙa wa Allah.
Burodi goma sha biyu da aka kasa su gida biyu, kowane kashi na ɗauke da burodi guda shida. An ajiye su a kan teburi da ke Wuri Mai Tsarki a tentin saduwa da kuma haikali. Ana kuma kiran sa “burodin da aka keɓe.” Akan canja waɗannan burodi da ake keɓe wa Allah da sabbin burodi kowace Ranar Asabaci. Firistoci ne kawai suke cin burodin da aka cire.—2Tr 2:4; Fit 25:30; Fir 24:5-9; Mat 12:4; Ibr 9:2.
C
-
Cerub.
Malaꞌiku ne masu iko sosai kuma suna yin ayyuka na musamman. Su dabam ne da seraf.—Far 3:24; Fit 25:20; Ish 37:16; Ibr 9:5.
D
-
Dattijo.
Yana nufin mutumin da ya manyanta, amma a cikin Nassosi, yana nufin wanda yake da matsayi, da iko, da kuma hakki a cikin alꞌumma. An kuma yi amfani da kalmar a cikin Ruꞌuya ta Yohanna saꞌad da ake magana game da halittu da ke sama. Akan fassara kalmar yaren Girka pre·sbyʹte·ros zuwa “dattijo” saꞌad da take nufin waɗanda suke da hakkin ja-goranci a ikilisiya.—Fit 4:29; K.M 31:23; 1Ti 5:17; R.Y 4:4.
-
Dawo; Dawowa.
A wasu wurare a cikin Nassosin Girkanci na Krista, wannan kalmar na nufin dawowar Yesu, wato daga lokacin da aka naɗa shi sarki a sama har zuwa kwanakin ƙarshe na wannan zamanin. Saꞌad da Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu zai dawo, ba ya nufin cewa zai dawo kuma ya koma nan da nan; a maimakon haka, zai ɗauki dogon lokaci kuma abubuwan da za su faru za su nuna cewa ya dawo.—Mat 24:3.
-
Dikafolis.
Rukunin biranen Girka, wanda asali ya ƙunshi birane goma. (An sami sunan ne daga kalmar yaren Girka deʹka, da ke nufin “goma,” da poʹlis, da ke nufin “birni.”) Shi ne kuma sunan yankin da ke gabas da Tekun Galili da kuma Kogin Jodan, yankin da yawancin biranen suke. Wuraren ne cibiyoyin alꞌadu da kasuwanci na mutanen Girka. Yesu ya bi ta cikin yankin, amma Littafi Mai Tsarki bai ce ya ziyarci ɗaya daga cikin biranen ba.—Mat 4:25; Mrk 5:20.
-
Dinari.
Tsabar kuɗin azurfa na Roma da nauyinsa ya kai wajen giram 3.85 kuma yana ɗauke da zanen siffar Kaisar a gefe ɗaya. Dinari ɗaya ya yi daidai da kuɗin da ake biyan lebura na aikin yini ɗaya. Kuma shi ne tsabar kuɗin haraji da Yahudawa suke ba wa Romawa.—Mat 22:17; Luk 20:24.
-
Doka.
-
Dokar Musa.
-
Drakma.
A Nassosin Girkanci na Krista, kalmar nan tana nufin tsabar kuɗin azurfa na Girka, wanda a lokacin nauyinsa ya kai giram 3.4.—Mat 17:24.
-
Dusa.
Wani abu ne da ake cire daga jikin hatsi saꞌad da ake buga hatsin da kuma tankaɗe shi. Ana amfani da dusa don a kwatanta abin da bai da amfani kuma ba a bukatar sa.—Za 1:4; Mat 3:12.
-
Dutse mafi amfani.
Wannan shi ne dutse da ake saka a kwana na gini, wurin da bango biyu suka haɗu, yana da muhimmanci domin shi yake riƙe su tare. Wanda ya fi muhimmanci shi ne dutsen da ake sakawa a tushen gini; akan zaɓi dutse mai ƙarfi sosai a saka a kwana saꞌad da ake gina manyan gine-gine da kuma katangar birni. An yi amfani da furucin don a kwatanta farkon duniya, an ce Yesu shi ne “dutse mafi amfani a tushen” ikilisiyar Krista, wadda aka kwatanta ta da gida wanda Allah yake amfani da ruhunsa ya gina.—Afi 2:20; Ayu 38:6.
-
Dutsen niƙa.
Wani fefen dutse da aka saka a kan wani dutse da ake amfani da shi wajen niƙa hatsi. A zamanin Littafi Mai Tsarki, a yawanci gidaje, mata suna amfani da dutsen niƙa na hannu. Da yake kowane iyali suna amfani da dutsen niƙa na hannun don su yi burodin da suke bukata a kowace rana, Dokar Musa ta hana ƙwace dutsen niƙa ko ɗan dutsen da ake riƙe a hannu don a yi niƙan da shi a matsayin jingina. Dabbobi ne suke juye manyan dutsen niƙa.—M.S 24:6; Mrk 9:42.
Ɗ
-
Ɗan Dauda.
Furucin da ake yawan kiran Yesu da shi, da ke nuna cewa shi ne zai gāji Mulkin da Allah ya yi wa Dauda alkawari cewa wani daga zuriyarsa ne zai gāda.—Mat 12:23; 21:9.
-
Ɗan fari.
Ainihin abin da yake nufi shi ne ɗa na farko da mutum ya haifa. A zamanin dā, ɗan fari yana da matsayi na musamman a iyali, kuma akan ba shi shugabancin iyali saꞌad da babansa ya mutu. Ban da zama ɗan fari na Jehobah, Yesu ma ɗan fari ne na dukan halittu da kuma na waɗanda aka ta da daga mutuwa.—Far 25:33; Fit 11:5; Kol 1:15; R.Y 1:5.
-
Ɗan mutum.
Furucin nan ya bayyana wajen sau tamanin a cikin littafin Matiyu, da Markus, da Luka, da kuma Yohanna. Yesu ne Ɗan mutum, kuma hakan na nufin cewa haifan sa aka yi a duniya, ba halittar ruhu ne da ya canja siffarsa ya ɗauki siffar ɗanꞌadam ba. Furucin ya kuma nuna cewa Yesu zai cika annabcin da aka rubuta a Daniyel 7:13, 14. A Nassosin Ibrananci, an kira Ezekiyel da Daniyel da wannan furucin, kuma hakan ya nuna bambancin da ke tsakanin su da Wanda ya ba su saƙon.—Eze 3:17; Dan 8:17; Mat 19:28; 20:28.
F
-
Fansa.
Abin da ake bayar don a ceto wani da aka yi garkuwa da shi, ko ake hukunta shi, ko yake shan wahala, ko daga zunubi, ko kuma daga wani abu da ya kamata mutum ya yi. A wasu lokuta, ba kuɗi ake amfani da shi a yi hakan ba. (Ish 43:3) An bukaci fansa a yanayoyi dabam-dabam. Alal misali, dukan ꞌyaꞌyan fari maza, na dabba ko mutum mallakar Jehobah ne, don haka ana bukatar a biya fansa domin a kubutar da su daga yin hidima ta cikakken lokaci ga Jehobah. (Ƙid 3:45, 46; 18:15, 16) Idan ba a ɗaure bijimi da ke da haɗari ba kuma ya kashe mutum, za a bukaci mai bijimin ya biya fansa domin ya ceto kansa daga hukuncin kisa da ya kamata a yi masa. (Fit 21:29, 30) Amma, ba a karɓan fansa daga wurin wanda ya kashe wani da gangan. (Ƙid 35:31) Mafi muhimmanci ma, fansar da Yesu Kristi ya biya domin ya kuɓutar da ꞌyanꞌadam masu biyayya daga zunubi da kuma mutuwa, ita ce fansa da Littafi Mai Tsarki ya fi nanatawa.—Za 49:7, 8; Mat 20:28; Afi 1:7.
-
Fāra.
Wasu irin ƙwari ne da suke tafiya cikin dubbai saꞌad da suke ƙaura. Dokar Musa ta ɗauke su a matsayin abinci mai tsabta. Ana ɗaukan dubban fāra a matsayin annoba domin suna cinye abubuwa saꞌad da suke tafiya, kuma suna jawo hallaka mai girma.—Fit 10:14; Mat 3:4.
-
Farfajiya.
Filin da ke kewaye da katanga a tentin saduwa, kuma bayan an gina haikali, farfajiya ce filin da aka kewaye da katanga a haikalin. Bagaden ƙona hadayu yana farfajiyar da ke tentin saduwa, da kuma farfajiya na ciki da ke haikali. Littafi Mai Tsarki ya kuma ambata farfajiya da ke gidaje da kuma fādar sarakuna.—Fit 8:13; 27:9; 1Sr 7:12; Mat 26:3; Mrk 15:16; R.Y 11:2.
-
Farin turaren wuta.
Ya ƙunshi gam dabam-dabam masu ƙamshi da aka haɗa da balsam da ake ƙonawa a hankali don ya fitar da ƙamshi sosai. An yi amfani da kayan haɗi guda huɗu na musamman don a yi turaren wuta da aka yi amfani da shi a tentin saduwa da kuma haikali. Ana ƙona shi da safe kuma da dare a kan bagaden ƙona turaren wuta da ke Wuri Mai Tsarki. A Ranar Neman Gafara ana ƙona shi a cikin Wuri Mafi Tsarki. Turaren, kwatanci ne na adduꞌoꞌin amintattun bayin Allah, da Allah yake ji. Ba a bukaci Kristoci su ƙona turaren wuta ba.—Fit 30:34, 35; Fir 16:13; R.Y 5:8.
-
Farisiyawa.
Wani rukunin addinin Yahudawa a ƙarni na farko bayan haifuwar Yesu. Ba su fito daga zuriyar firistoci ba, amma suna bin Doka sosai, har ma da bayani mafi ƙanƙanta da ke cikinta. Haka ma suke ƙarfafa mutane su bi alꞌadun da suke faɗa da baki. (Mat 23:23) Sun yi ƙoƙarin hana mutane bin alꞌadun mutanen Girka, kuma da yake su masanan Doka da alꞌadu ne, suna da iko a kan mutane. (Mat 23:2-6) Wasunsu membobin Sanhedrin ne. A lokuta da yawa, sun yi adawa da Yesu a batun Ranar Assabaci, da alꞌadu, da kuma yin tarayya da masu zunubi da kuma masu karɓan haraji. Wasunsu sun zama Kristoci, a cikinsu ma har da Shawulu na Tarsus.—Mat 9:11; 12:14; Mrk 7:5; Luk 6:2; A.M 26:5.
-
Fentikos.
Wannan ne biki na biyu a cikin bukukuwa uku masu muhimmanci da aka umurci dukan Yahudawa maza su yi a Urushlima. Fentikos yana nufin “(Rana) ta Hamsin.” An yi amfani da kalmar a Nassosin Girkanci na Krista saꞌad da ake magana a kan Bikin Girbi ko kuma Bikin Makwanni a Nassosin Ibrananci. Akan yi bikin ne a rana ta hamsin, kuma ana soma ƙirgen ne a rana ta 16 ga watan Nisan.—Fit 23:16; 34:22; A.M 2:1.
-
Firist.
Mutumin da ke wakiltar Allah ga mutanen da yake musu hidima, yana kuma koya musu game da Allah da dokokinsa. Firistoci suna kuma wakiltar mutane a gaban Allah ta wurin miƙa hadayu da kuma yin roƙo a madadinsu. Kafin a kafa Dokar Musa, shugaban iyali ne yake hidimar firist don iyalinsa. A ƙarƙashin Dokar Musa, maza daga iyalin Haruna na kabilar Lawi ne suke hidima a matsayin firistoci. Sauran maza da suka fito daga zuriyar Lawi ne suke taimaka musu. A lokacin da aka kafa sabuwar yarjejeniya, Israꞌila ta Allah ce ta zama alꞌummar firistoci, kuma Yesu Kristi ne Shugaban Firistoci.—Fit 28:41; Ibr 9:24; R.Y 5:10.
-
Firꞌauna.
Laƙabin da ake ba wa sarakunan Masar. An ambata firꞌauna guda biyar a cikin Littafi Mai Tsarki (Shishak, So, Tirhaka, Neko, da Hofra), amma ba a ambata sunayen wasunsu ba, har da waɗanda suka yi maꞌamala sosai da Ibrahim, da Musa, da Yusufu.—Fit 15:4; Rom 9:17.
G
-
Gaba.
Yadda ake auna zurfin ruwa, kuma ya yi daidai da ƙafa shida (ko kuma mita 1.8).—A.M 27:28.
-
Gehenna.
Wannan shi ne sunan Kwarin Hinnom a yaren Girka, kuma kwarin yana kudu maso yammacin Urushalima ta dā. (Irm 7:31) Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa a wurin ne za a riƙa jefa gawawwaki. (Irm 7:32; 19:6) Ba abin da ya nuna cewa ana jefa dabbobi ko kuma mutane da ransu cikin Gehenna don a ƙona su ko a azabtar da su. Don haka, wurin ba ya wakiltar wani yanki da ake azabtar da mutane a cikin wuta har abada da ba a iya gani. A maimakon haka, Yesu da almajiransa sun ambata Gehenna don su kwatanta hukunci na har abada, wanda shi ne “mutuwa ta biyu,” kuma hakan yana nufin hallaka ta har abada.—R.Y 20:14; Mat 5:22; 10:28.
-
Ginshiƙi.
Wani abu ne mai tsayi da ke toƙare gini, ko kuma wani abu kamar haka. An yi amfani da ginshiƙai a haikali da kuma gidajen sarki da Sulemanu ya gina. A Nassosin Girkanci na Krista, an yi amfani da kalmar don a kwatanta ba da taimako (1Ti 3:15) ko kuma don a kwatanta matsayi na dindindin (R.Y 3:12).—Alƙ 16:29; 1Sr 7:21.
-
Girkanci.
Yaren da mutanen ƙasar Girka suke yi.
-
Gungume.
Miƙaƙƙen itace da ake rataye wanda ake so a kashe a kai. Wasu ƙasashe suna amfani da shi don su kashe mutum ko su rataye gawar wani don ya zama gargaɗi ga wasu ko kuma don a kunyatar da mutumin. An san Assiriyawa da mugunta sosai saꞌad da suke yaƙi, kuma sukan rataye waɗanda suka kama a kan miƙaƙƙen gungume, suna yin hakan ta wurin soka gungumen daga cikinsu sai ya fito a ƙirginsu. Amma, a Dokar Yahudawa, waɗanda suka yi laifi mai tsanani kamar saɓo ko bautar gumaka, akan kashe su ta wurin jefe su da dutse ko kuma ta wata hanya, saꞌan nan a rataye gawarsu a kan gungume ko itatuwa don ya zama gargaɗi ga wasu. (M.S 21:22, 23; 2Sm 21:6, 9) Romawa kuma sukan rataye mutum a kan gungume ne kawai, don hakan mutum zai iya rayu na ɗan kwanaki, daga baya ya mutu saboda zafi, da ƙishin ruwa, da yunwa da kuma zafin rana. A wasu lokuta kuma, kamar yadda aka yi wa Yesu, sukan manne hannaye da ƙafafun mutum da aka zarge shi a kan gungume da ƙusa. (Luk 24:20; Yoh 19:14-16; 20:25; A.M 2:23, 36)—Ka duba GUNGUMEN AZABA.
-
Gungumen azaba.
A yaren Girka, ana kiran sa stau·rosʹ, wanda yake nufin gungume ko kuma sanda da ya miƙe tsaye, kamar wadda aka kashe Yesu a kai. Babu alamar da ta nuna cewa kalmar nan a yaren Girka tana nufin giciye, kamar wanda arna suka yi amfani da shi a bautarsu na ɗarurruwan shekaru kafin zuwan Kristi. Furucin nan “Gungumen azaba” ya yi daidai da abin da asalin kalmar a yaren Girka take nufi, domin Yesu ma ya yi amfani da kalmar nan stau·rosʹ don ya bayyana irin azaba da wahala da kuma wulakancin da mabiyansa za su sha. (Mat 16:24; Ibr 12:2)—Ka duba GUNGUME.
-
Gungumen ɗaukan kaya.
Wani gungume ko ƙarfe ne da ake saka a kafaɗar mutum, sai a rataye kaya a gefe biyu na gungumen ko ƙarfen. Yana kuma iya nufin gungume ko kuma ƙarfen da ake saka a wuyan dabbobi guda biyu (a yawancin lokuta shanu) saꞌad da suke jan garmar noma ko kuma keken-doki. Da yake bayi suna yawan yin amfani da gungume su ɗauki kaya masu nauyi, an yi amfani da furucin a alamance saꞌad da ake magana game da bauta ko kuma mutum ya miƙa kai ga wani, da wulaƙanci da kuma shan wahala. Idan aka ce cire ko karya gungumen, ana nufin ꞌyanci daga bauta, da wulaƙanci da kuma cin zarafi.—Fir 26:13; Mat 11:29, 30.
-
Gunki; Bautar gumaka.
Gunki siffa ne, ko abin da ke wakiltar wani abu a zahiri ko wanda ake tunaninsa, wanda mutane suke amfani da shi wajen bauta. Bautar gumaka tana nufin jin tsoro, ko ƙauna, ko bauta wa, ko kuma ɗaukaka gunki.—Za 115:4; A.M 17:16; 1Ko 10:14.
-
Gwamna.
H
-
Hadaya.
Abin da mutum yake miƙa wa Allah don ya nuna godiya, ko don ya nuna cewa ya amince da laifinsa, kuma ya maido da dangantakarsa da Allah. Somawa da Habila, mutane sun miƙa hadayu dabam-dabam da son ransu, har da na dabbobi, kuma sun ci-gaba da yin hakan har zuwa lokacin da aka ba da Dokar Musa. A cikin Dokar, an umurci mutanen su riƙa yin hakan. Bayan da Yesu ya ba da ransa a matsayin cikakkiyar hadaya, ba a bukatar bayin Allah su miƙa hadaya. Duk da cewa Kristoci ba sa ba da hadaya, suna yin wasu abububwa da ke kama da miƙa hadayu ga Allah.—Far 4:4; Ibr 13:15, 16; 1Yo 4:10.
-
Hadaya ta abin sha.
Yana nufin hadayar ruwan inabi da aka zuba a kan bagade kuma ake miƙa da yawancin hadayu. Bulus ya yi amfani da shi a matsayin misali don ya nuna yadda yake a shirye ya taimaka wa ꞌyanꞌuwansa Kristoci.—Ƙid 15:5, 7; Fib 2:17.
-
Hadaya ta ƙonawa.
Yana nufin hadayar dabba da aka ƙona a kan bagade kuma aka miƙa ta gabaki-ɗaya ga Allah; babu wani ɓangare ko sashen dabbar da mai miƙa hadayar zai ɗauka, ko da dabbar bijimi ne, ko rago, ko bunsuru, ko kurciya, ko kuma tattabara.—Fit 29:18; Fir 6:9; Mrk 12:33; Ibr 10:6.
-
Hadaya ta wanke zunubi.
Wannan hadaya ce da ake yi don zunubin da mutum ya yi ba da gangan ba, amma domin kasawarsa da ajizancinsa. An yi hadayar da dabbobi dabam-dabam, kama daga bijimi zuwa tattabara. Akan duba matsayin mutumin ko kuma yanayinsa don a san irin dabbar da zai bayar.—Fir 4:27, 29; Ibr 10:8.
-
Hades.
Wannan kalmar yaren Girka ne da ta yi daidai da kalmar nan “Sheol” a Ibrananci. An fassara kalmar zuwa “Kabari” (da babban harafi), don a nuna bambanci da ke tsakaninta da kabari na zahiri.—Ka duba KABARI.
-
Haikali.
Wuri ne mai tsarki da aka keɓe don bauta. A yawancin lokaci yana nufin tentin saduwa ko kuma haikali da ke Urushalima, wanda ya maye gurbin tentin saduwa a matsayin cibiyar bauta na Israꞌilawa. Sulemanu ne ya gina haikali na farko kuma mutanen Babila ne suka hallaka haikalin. Zerubbabel ne ya gina haikali na biyu bayan sun dawo daga bauta a Babila, kuma daga baya, Hirudus Mai Grima ya sake gina haikalin. A wasu lokuta, Littafi Mai Tsarki ya kira shi “gidan.” (Mat 21:13; Luk 11:51; 1Tr 29:1; 2Tr 2:4; Mat 24:1) Ana kuma yin amfani da kalmar saꞌad da ake magana game da wurin zaman Allah a sama.—Fit 25:8, 9; 2Sr 10:25; 1Tr 28:10; R.Y 11:19.
-
Halin rashin kunya.
An samo furucin nan daga kalmar nan a·selʹgei·a a yaren Girka. Furucin yana nufin yin abubuwan da suka saɓa wa dokokin Allah sosai, kuma yana nuna cewa mutumin ya yi hakan da taurin kai ba tare da kunya ba, wato halin da ke nuna cewa mutum ba ya daraja ko kuma ya rena hukuma, da dokoki, da kuma ƙaꞌidodi. Wannan furucin ba ya nufin ƙananan laifuffuka.—Gal 5:19; 2Bi 2:7.
-
Hamis.
Shi ne allahn mutanen Girka, ɗan Zeyus. A Listira, mutane sun yi tsammanin cewa Bulus shi ne wakilin alloli kuma shi ne allahn da ya iya magana da kyau, shi ya sa suka yi kuskuren kiran sa Zeyus.—A.M 14:12.
-
Hanyar Ubangiji.
Wannan furuci ne da ake amfani da shi a cikin Nassosi domin a nuna halayen da Jehobah ya amince da su ko kuma bai amince da su ba. An kira waɗanda suka zama mabiyan Yesu, masu bin “Hanyar Ubangiji,” wato suna yin rayuwa da ta jitu da bangaskiyarsu ga Yesu Kristi, kuma suna bin misalinsa.—A.M 19:9.
-
Hatimi.
Wata naꞌura da ake amfani da ita a yi alama a kan wani abu don a nuna cewa abin mallakar wani ne, ko don a tabbatar da cewa abin na gaske ne, ko kuma don a tabbatar da yarjejeniya. Ƙari ga haka, an yi amfani da ita don a hana mutane buɗe takardu ko wasu abubuwa da aka hatimce, a ciki har da ƙofofi da kaburbura. A zamanin dā, ana yin hatimi ne da abubuwa masu ƙarfi (kamar dutse, ko hauren giwa, ko kuma itace) kuma ana yin rubutu a kai ko kuma zane. An yi misali da hatimi don a nuna cewa wani abu na gaske ne, ko a matsayin alama cewa wani abu mallakar wani ne, ko wani abu da aka ɓoye ko kuma sirri ne.—Mat 27:66; Yoh 6:27; Afi 1:13; R.Y 5:1; 9:4.
-
Hidima mai tsarki.
-
Hirudus.
Wannan sunan wasu mutane ne da suka fito daga iyali ɗaya, da gwamnatin Roma ta naɗa su su yi mulki a kan Yahudawa. Na farko shi ne Hirudus Mai Girma, kuma an san shi a matsayin wanda ya sake gina haikalin da ke Urushalima da kuma wanda ya ba da umurni cewa a kashe yara saꞌad da yake ƙoƙarin kashe Yesu. (Mat 2:16; Luk 1:5) An naɗa ꞌyaꞌyan Hirudus Mai Girma, wato Hirudus Arkilayus da Hirudus Antifas, su yi mulkin sassa na yankin da babansu ya yi mulki a kai. (Mat 2:22) Antifas ya yi mulki a kan kashi ɗaya cikin huɗu na yankin, kuma ana yawan kiran sa “sarki.” Shi ne yake mulki a lokacin da Yesu yake hidimarsa na shekara uku da rabi zuwa lokacin da abubuwan da aka rubuta a Ayyukan Manzanni 12 suka faru. (Mrk 6:14-17; Luk 3:1, 19, 20; 13:31, 32; 23:6-15; A.M 4:27; 13:1) Bayan haka, sai malaꞌikan Allah ya kashe jikan Hirudus Mai Girma, wato Hirudus Agirifa na Ɗaya bayan ya yi mulki na gajeren lokaci. (A.M 12:1-6, 18-23) Ɗansa, Hirudus Agirifa na Biyu, ya zama sarki kuma ya yi mulki har zuwa lokacin da Yahudawa suka yi wa Romawa tawaye.—A.M 23:35; 25:13, 22-27; 26:1, 2, 19-32.
-
Hissof.
Wani itace ne da ke da rassa da ganye masu kyau; an yi amfani da shi wajen yayyafa jini ko kuma ruwa a lokacin tsabtacewa. A cikin Littafi Mai Tsarki, mai yiwuwa kalmonin yaren Girka da Ibrananci da aka yi amfani da su, sun ƙunshi itatuwa dabam-dabam. Da alama, “hissof” da aka ambata a Yohanna 19:29, irin wanda yake yin tsayi sosai ne, shi ya sa aka iya yin amfani da doguwar sanda daga jikinsa da ke ɗauke da soson ruwan inabi mai tsami da aka kai bakin Yesu.—Ibr 9:19.
-
Hukumomi.
Waɗannan su ne masu mulki ko kuma gwamnati a yankunan da ke ƙarƙashin Roma. Aikinsu ya haɗa da tabbatar da doka da oda, da iko da kuɗaɗe, da shariꞌanta waɗanda suka taka doka, da kuma zartar da hukunci.—A.M 16:20.
I
-
Ibilis.
-
Ibrananci.
Yaren Ibraniyawa. A zamanin Yesu, Ibrananci ya ƙunshi furuci da yawa daga yaren Aramaik, kuma shi ne yaren da Kristi da almajiransa suka yi.—A.M 26:14.
-
Ibraniyawa.
Suna ne da aka ba wa Ibram (Ibrahim), wanda ya bambanta shi da maƙwabtansa Amoriyawa. Daga baya, an fara kiran zuriyarsa ta wurin jikansa Yakubu da wannan sunan.—Far 14:13; Fit 5:3.
-
Ikilisiya.
Rukunin mutane da suka taru domin wani abu ko kuma aiki na musamman. A Nassosin Ibrananci, ana amfani da ita saꞌad da ake maganar alꞌummar Israꞌila. A Nassosin Girkanci na Krista, tana nufin kowace ikilisiya ta Krista, amma a yawancin lokaci ana amfani da ita saꞌad da ake maganar ikilisiyar Krista gabaki-ɗaya.—1Sr 8:22; A.M 9:31; Rom 16:5.
-
Ilirikum.
Wani yankin Roma da ke arewa maso yammacin Girka. Bulus ya yi tafiya zuwa wannan wuri mai nisa a hidimarsa, amma Littafi Mai Tsarki bai faɗa ko ya yi waꞌazi a Ilirikum ko kuma ya je wurin ne kawai ba.—Rom 15:19.
-
Israꞌila.
Sunan da Allah ya ba wa Yakubu. Daga baya, an soma kiran dukan zuriyarsa da wannan sunan. Sau da yawa ana kiran zuriyar yaran Yakubu goma sha biyu ꞌyaꞌyan Israꞌila, ko gidan Israꞌila, ko mutanen Israꞌila, ko kuma Israꞌilawa. Israꞌila ne kuma ake kiran kabilu goma da suka kafa mulkinsu a arewacin ƙasar, waɗanda suka ware kansu daga mulkin kabilu da ke kudanci. Daga baya kuma an kira shafaffun Kristoci, “Israꞌila ta Allah.”—Gal 6:16; Far 32:28; A.M 4:10; Rom 9:6.
-
Itacen rai.
Wani itace ne a lambun Adnin. Littafi Mai Tsarki bai nuna cewa ꞌyaꞌyan itacen suna da abubuwan da ke ba da rai ba, a maimakon haka, yana nufin tabbacin da Allah ya ba ma waɗanda zai ba su damar cin ꞌyaꞌyan itacen cewa za su yi rayuwa har abada. A littafin Ruꞌuya ta Yohanna, yana nufin abin da Allah zai tanadar don mutane su yi rayuwa har abada.—Far 2:9; 3:22; R.Y 2:7; 22:19.
J
-
Jehobah.
Wannan shi ne yadda aka fassara sunan Allah da aka rubuta da baƙaƙen nan huɗu (יהוה) na Ibrananci. Sunan ya bayyana sau ɗari biyu da talatin da bakwai (237) a wannan juyin Nassosin Girkanci na Krista.—Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.
K
-
Kabari.
Idan aka rubuta shi da ƙaramin harafi, ana nufin kabarin da aka binne mutum a zahiri; idan kuma aka rubuta shi da babban harafi, ana nufin “Sheol” a Ibrananci da kuma “Hades” a yaren Girka. Kuma a Littafi Mai Tsarki, su biyun suna nufin yanayin da matattu suke ciki domin ba sa yin kome kuma ba sa yin tunani.—Far 47:30; M.W 9:10; Mat 27:61; A.M 2:31.
-
Kabarin tunasarwa.
Wurin da ake binne gawar wanda ya mutu. Yadda aka fassara furucin nan a yaren Girka shi ne mne·meiʹon, wanda aka samo daga kalmar da ke nufin “a tunasar da.” Kuma hakan na nufin cewa ba a manta da mutumin da ya mutu ba.—Fir 8:15; 1Sr 2:28; R.Y 9:13.
-
Kaciya.
-
Kaisar.
Wannan sunan wani iyali ne a Roma wanda ya zama laƙabi na sarakunan Roma. A Littafi Mai Tsarki, an ambaci sunan Agustus, da Tibariya, da Klaudiyus, ko da yake ba a ambaci Sarki Nero da sunansa ba, yana cikin waɗanda aka kira Kaisar. An kuma yi amfani da sunan nan “Kaisar” a cikin Nassosin Girkanci na Krista saꞌad da ake magana game da hukuma ko kuma Ƙasa.—Mrk 12:17; A.M 25:12.
-
Kakaki.
Wani abu da ake busawa wanda aka yi da ƙarfe. Ana amfani da shi a jawo hankalin mutane ga wani abu kuma ana amfani da shi a yi kiɗi. A yawancin lokuta, ana busa kakaki kafin a sanar da hukuncin Jehobah ko kuma a sanar da wani abu mai muhimmanci da Allah zai yi.—1Ko 15:52; R.Y 8:7–11:15.
-
Kaldiyawa.
Su ne mutanen da suke zama kusa da Kogin Tigiris da kuma Yufiretis. A zamanin dā, birni mafi muhimmanci na Kaldiyawa shi ne Ur, wato garin su Ibrahim.—A.M 7:4.
-
Karin magana.
Maganar hikima ko gajeren labari da ke koyar da darasi ko kuma bayyana gaskiya da kalmomi kaɗan. A Littafi Mai Tsarki, karin magana na iya zama maganar da ke da wuyar ganewa ko kuma kacici-kacici. Karin magana, magana ce da ake yi domin a faɗi gaskiya, kuma a yawancin lokuta akan yi shi ne ta wurin misali. Ana amfani da wasu karin magana ne domin a zolaye wasu ko kuma a rena su.—M.W 12:9; 2Bi 2:22.
-
Karuwa.
Mai yin lalata don samun kuɗi. (Kalmar yaren Girka da aka fasara zuwa “karuwa,” ita ce porʹne, kuma tana nufin “a sayar da wani abu.”) An fi amfani da kalmar ga mata, ko da yake Littafi Mai Tsarki ya ambata karuwai maza. A Dokar Musa, an hana yin karuwanci, kuma idan karuwa ta kawo kuɗin da ta samo daga karuwancinta a haikali, Jehobah ba zai amince da shi ba. Amma ba haka masu bautar gumaka suke yi ba. Suna amfani da karuwai a haikalinsu don samun kuɗi. (M.S 23:17, 18; 1Sr 14:24) Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalmar a alamance, saꞌad da yake magana game da mutane, ko alꞌummai, ko kuma ƙungiyoyi da suke bautar gumaka yayin da suke cewa suna bauta wa Allah. Alal misali, Ruꞌuya ta Yohanna ya kira “Babila Babba” karuwa domin tana shaꞌani da masu iko na duniyar nan don samun iko da kuma arziki.—R.Y 17:1-5; 18:3; 1Tr 5:25.
-
Kashi goma (zakka).
Yana nufin kashi goma na abin da mutum yake da shi da yake bayarwa a matsayin kyauta ko gudummawa, musamman ma idan ya yi hakan don ibada. (Mal 3:10; M.S 26:12; Mat 23:23; Ibr 7:5) Dokar Musa ta bukaci Israꞌilawa su riƙa ba da kashi goma na amfanin gonarsu da na dabobbinsu a kowace shekara don su taimaka wa Lawiyawa. Lawiyawa kuma sukan ware kashi goma na zakka da aka ba su don su taimaka wa firistoci daga zuriyar Haruna. Akwai kuma wasu zakka da Israꞌilawa suke bayarwa. Ba a bukaci Kristoci su ba da zakka ba.
-
Katakon riƙe ƙafafu.
Wani katakon da ake amfani da shi a hukunta mutum ta wurin ɗaure mutumin a jikin katakon. Ana amfani da wasu katakan a ɗaure ƙafafun mutum ne kawai, amma wasunsu kuma ana amfani da su a sa mutum a yanayin da zai sa jikinsa ya yi masa zafi, mai yiwuwa ta wurin ɗaure ƙafafu da hannaye da kuma wuyarsa.—Irm 20:2; A.M 16:24.
-
Kayan kāriya.
Waɗannan kaya ne da sojoji suke sakawa don su kāre kansu, kayan sun haɗa da hular kwano, da rigar ƙarfe, da ɗamara, da abin tsaron ƙafafu, da kuma garkuwa.—1Sm 31:9; Afi 6:13-17.
-
Keken-doki.
-
Kogin Yufiretis.
Shi ne kogi mafi tsawo kuma mafi muhimmanci a kudu maso yammacin Asiya, yana ɗaya daga cikin manyan koguna biyu da ke Mesofotamiya. An fara ambata sunan kogin a Farawa 2:14 a matsayin ɗaya daga cikin koguna huɗu da ke Adnin. Ana yawan kiran sa “Kogin.” (Far 31:21) Yana kan iyaka a arewancin yankin da aka ba wa Israꞌilawa.—Far 15:18; R.Y 9:14; 16:12.
-
Kor/Koros.
Awon abu mai ruwa-ruwa da kuma hatsi. Ya yi daidai da lita ɗari biyu da ashirin, (ko kuma galan 58.1).—1Sr 5:11; Luk 16:7, ƙarin bayani.
-
Krista.
Sunan da Allah ya ba wa mabiyan Yesu Kristi.—A.M 11:26; 26:28.
-
Kristi.
-
Kubit.
Awon tsayin abu da ake yi daga gwiwan hannu zuwa ɗan yatsa na tsakiya. Israꞌilawa sukan yi amfani da kubit da ya kai wajen inci goma sha bakwai da rabi (ko kuma santimita 44.5), amma kuma sukan yi amfani da kubit da ya fi tsayi, da ya kai wajen inci ashirin da ɗigo huɗu (ko kuma santimita 51.8).—Far 6:15; Mat 6:27; Luk 12:25; R.Y 21:17.
-
Kujerar shariꞌa.
Wuri ne da aka ɗan gina shi sama a waje da ake hawa ta matakala, daga wurin ne mahukunta suke yi wa jamaꞌa jawabi kuma su sanar da hukuncinsu. An yi amfani da furucin nan “kujerar shariꞌa na Allah” da “kujerar shariꞌa na Kristi” a alamance don a nuna shirin da Jehobah ya yi na yi wa mutane shariꞌa.—Rom 14:10; 2Ko 5:10; Yoh 19:13.
-
Kuturta; kuturu.
Wata cutar fata ce mai tsanani. A cikin Nassosi, kuturta ta ƙunshi wasu cututtuka ba wadda muka sani a yau kawai ba, domin ba mutane kawai take shafa ba, amma har da riguna da gidaje. Ana kiran mutumin da ya kamu da kuturta, kuturu.—Fir 14:54, 55; Luk 5:12.
-
Kwalbar alabasta.
Wani ƙaramin kwalbar turare wanda asali aka yi da dutsen da ake samuwa kusa da yankin Alabastron a Masar. Akan yi wannan kwalbar ta yadda za a iya rufe ta da kyau don kada turare mai daraja da ke ciki ya yi yoyo.—Mrk 14:3.
-
Kwanakin ƙarshe.
Saꞌad da Littafi Mai Tsarki yake annabta abubuwan da za su faru a nan gaba, ya yi amfani da furuci nan “kwanakin ƙarshe” da wasu furuci kamarsa, don ya yi magana game da lokacin da wasu abubuwa da za su faru kafin ƙarshen ya zo. (Eze 38:16; Dan 10:14; A.M 2:17) Bisa ga irin annabcin, wannan lokacin zai iya zama ꞌyan shekaru ko shekaru da yawa. A yawancin lokaci, Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da wannan furucin ne saꞌad da yake magana game da “kwanakin ƙarshe” na wannan zamanin, wato lokacin dawowar Yesu.—2Ti 3:1; Yaƙ 5:3; 2Bi 3:3.
-
Kyauta ga talakawa.
Kyauta da ake bayarwa domin a taimaka wa mutumin da ke cikin bukata. Ko da yake Nassosin Ibrananci ba su yi magana game da irin kyautar nan kai tsaye ba, amma Dokar Musa ta ce wajibi ne Israꞌilawa su taimaka wa talakawa.—Mat 6:2.
Ƙ
-
Ƙaho.
Yana nufin ƙahonnin dabba, waɗanda ake amfani da su domin shan abubuwa, ana zuba māi, da tawada da kayan kwalliya a ciki, kuma an yi amfani da shi a matsayin kayan ƙida ko kuma abin jawo hankalin mutane. (1Sm 16:1, 13; 1Sr 1:39; Eze 9:2) A wurare da yawa, an yi amfani da “ƙaho” don kwatanta iko, da kuma cin nasara.—M.S 33:17; Mik 4:13; Luk 1:69.
-
Ƙahonnin bagade.
Wannan yana nufin wasu abubuwa da suke kama da ƙahonni da ke ɓangarori huɗu na wasu bagade.—Fir 8:15; 1Sr 2:28; R.Y 9:13.
-
Ƙarshen zamani.
Lokaci ne da zai kai ga ƙarshen duniya ko kuma alꞌamura da ke ƙarƙashin ikon Shaiɗan. Wannan lokaci, ɗaya ne da lokacin da Littafi Mai Tsarki ya kira dawowar Kristi. Yesu zai ja-goranci malaꞌiku, kuma za su “ware mugaye daga masu adalci” saꞌan nan su hallaka su. (Mat 13:40-42, 49) Almajiran Yesu sun so su san lokacin da “ƙarshen” zai zo. (Mat 24:3) Kafin Yesu ya koma sama, ya yi wa mabiyansa alkawari cewa zai kasance tare da su har zuwa lokacin.—Mat 28:20.
-
Ƙazanta; marar tsabta.
Yana iya nufin rashin tsabta na jiki ko kuma kasancewa da halaye marasa kyau. Amma a Littafi Mai Tsarki, kalmar tana nufin abin da ba a amince da shi ba ko kuma abin da bai da tsabta bisa Dokar Musa. (Fir 5:2; 13:45; Mat 10:1; A.M 10:14; Afi 5:5)—Ka duba TSABTA.
-
Ƙunci mai girma.
A yaren Girka, kalmar nan “ƙunci” tana nufin wahalar da mutum ke sha domin yanayin rayuwa. Yesu ya yi magana game da wani “ƙunci mai girma” da zai faɗa ma Urushalima. Ƙari ga haka, ya yi magana game da “ƙunci mai girma” da zai faɗo wa dukan mutanen duniya a nan gaba saꞌad da ‘zai zo a cikin ɗaukaka.’ (Mat 24:21, 29-31) Bulus ya kwatanta wannan ƙuncin a matsayin aikin adalci na Allah a kan “waɗanda ba su san Allah ba, da waɗanda ba sa biyayya ga labari mai daɗi” game da Yesu Kristi. Ruꞌuya ta Yohanna sura 19 ta nuna cewa Yesu ne zai ja-goranci rundunonin da ke sama wajen yaƙan “dabbar dajin da sarakunan duniya da sojojinsu.” (2Ta 1:6-8; R.Y 19:11-21) An kuma nuna cewa “taro mai girma” ne za su tsira a lokacin ƙuncin. (R.Y 7:9, 14)—Ka duba ARMAGEDDON.
-
Ƙungiya.
Rukunin mutane da ke bin wata koyarwa ko wani shugaba kuma suna bin abin da suka yi imani da shi. An yi amfani da kalmar saꞌad da ake magana game da sanannun rukunoni biyu na addinin Yahudawa, wato Farisiyawa da Sadukiyawa. Waɗanda ba Kristoci ba sun kira Kristoci ‘ƙungiya’ ko kuma ƙungiyar Nazarawa, mai yiwuwa sun kira su hakan ne domin suna ganin su a matsayin waɗanda suka bar addinin Yahudawa. Daga baya an sami ƙungiyoyi dabam-dabam a cikin ikilisiyar Krista; an ambata “ƙungiyar Nikolas” a Ruꞌuya ta Yohanna.—A.M 5:17; 15:5; 24:5; 28:22; R.Y 2:6; 2Bi 2:1.
-
Ƙuriꞌa.
Ƙananan katako ko kuma duwatsu da ake amfani da su wajen yanke shawara. Akan tara su a cikin riga ko kuma tukunyar ƙasa, sai a jijjiga su. Wanda ya faɗo ko kuma wanda aka ciro daga ciki, shi ne aka zaɓa. A yawancin lokaci, ana adduꞌa kafin a yi hakan.—Mat 27:35; A.M 1:26.
L
-
Labari mai daɗi.
-
Labule.
Zane mai kyau da aka yi masa zubi da sifoffin malaꞌiku da ake kira cerub da ya raba Wuri Mai Tsarki da Wuri Mafi Tsarki a tentin saduwa da kuma haikali.—Fit 26:31; 2Tr 3:14; Mat 27:51; Ibr 9:3.
-
Lalata.
Kalmar nan a yaren Girka ita ce por·neiʹa. Ana amfani da kalmar a cikin Nassosi saꞌad da ake magana a kan ayyukan jimaꞌi da Allah ya hana. Ayyukan sun haɗa da zina, da karuwanci, da duk wani shaꞌani na jimaꞌi tsakanin namiji da ta mace da ba su auri juna ba, da jimaꞌi tsakanin namiji da namiji, da jimaꞌi tsakanin mace da mace, da kuma jimaꞌi tsakanin mutum da dabba. A littafin Ruꞌuya ta Yohanna, an ce “Babila Babba,” wadda take wakiltar dukan addinan ƙarya na duniya ta yi lalata. An faɗi hakan ne domin tana shaꞌani da masu mulkin wannan duniyar don ta sami iko da kuma arziki. (R.Y 14:8; 17:2; 18:3; Mat 5:32; A.M 15:29; Gal 5:19)—Ka duba KARUWA.
-
Lawi; Balawi.
Shi ne ɗan Yakubu na uku ta wurin matarsa Liyatu; ana kuma kiran wata kabila da sunan nan. ꞌYaꞌyansa uku ne suka zama tushen rukunoni uku masu muhimmanci da aka san su a matsayin firistoci Lawiyawa. A wasu lokuta, kalmar nan “Lawiyawa” tana nufin kabilar gabaki-ɗaya, amma a yawancin lokuta, hakan bai haɗa da firistoci daga iyalin Haruna ba. Kabilar Lawi ba ta samu rabon fili a cikin Ƙasar Alkawari ba, amma an ba ta birane arbaꞌin da takwas a cikin filayen da aka raba ma sauran kabilun.—M.S 10:8; 1Tr 6:1; Ibr 7:11.
-
Laꞌana.
Tana nufin yin barazana ko kuma a ce abu marar kyau zai faru da mutum ko wani abu. Ba ɗaya take da yin saɓo ko kuma tsananin fushi ba. A yawancin lokaci, laꞌana tana nufin abubuwa marasa kyau da mutum ya faɗa a fili cewa za su faru. Kuma idan Allah ne ko kuma wani mutum mai iko ne ya faɗa, tana nan kamar annabci kuma takan faru da gaske.—Far 12:3; Ƙid 22:12; Mrk 11:21; A.M 23:12; Rom 12:14; Gal 3:10.
-
Lefton.
A zamanin da aka rubuta Nassosin Girkanci na Krista, shi ne kwandalar tagulla ko jan ƙarfe mafi ƙanƙanta na Yahudawa. Ana kiran lefton fiye da ɗaya lefta.—Mrk 12:42; Luk 21:2; ka duba ƙarin bayani da ke ayoyin.
M
-
Maginin tukwane.
Wanda yake yin amfani da laka ya yi tukwane, da kwanuka, da kuma tuluna. Furucin nan a Ibrananci yana nufin “maƙeri.” Ana yawan amfani da yadda maginin tukwane yake da ikon yin abin da ya ga dama da laka don a kwatanta ikon mallaka na Jehobah a kan mutane da ƙasashe.—Ish 64:8; Rom 9:21.
-
Mai duba.
Mutumin da yake cewa zai iya faɗan abubuwan da za su faru a nan gaba. Littafi Mai Tsari ya ce masu duba sun haɗa da firistoci masu yin tsafi, da masu yin sihiri, da masanan taurari, da dai sauransu.—Fir 19:31; M.S 18:11; A.M 16:16.
-
Mai gadi.
Wanda yake kāre mutane ko kuma dukiya don kada wani ya yi musu lahani ko ya sace su, musamman ma da dare. Kuma shi ne yake sanar da mutane idan an kawo hari. A yawancin lokaci, masu gadi sukan saya a kan katangar birni da kuma hasumiyoyi, don su ga waɗanda suke zuwa tun suna nesa. Akan kira sojan da yake sayawa a kan hasumiya ko katangar birni mai gadi.—Mat 27:65; 28:4.
-
Mai kula.
Mutumin da aikinsa shi ne ya lura da kuma ƙarfafa ikilisiya. Ainihin maꞌanar kalmar nan e·piʹsko·pos a yaren Girka shi ne lura da mutane da nufin kāre su. Furucin nan “mai kula” da kuma “dattijo” suna nufin matsayi ɗaya a ikilisiyar Krista. “Dattijo” yana nuna cewa mutumin da aka naɗa yana da halaye da suka nuna cewa ya manyanta. “Mai kula” kuma yana nuna ayyukan da mutum zai yi idan an naɗa shi.—A.M 20:28; 1Ti 3:2-7; 1Bi 5:2.
-
Mai Tsayawa Tsakani.
-
Mai yin sihiri.
Mutumin da ke yin amfani da ikon da ake ganin ya samu daga mugayen ruhohi.—A.M 13:6.
-
Mai ꞌyanci; wanda aka ba wa ꞌyanci.
A zamanin da Romawa suke mulki, “mai ꞌyanci” yana nufin wanda aka haifa da ꞌyanci, kuma yana da izinin zama cikakken ɗan ƙasa. Amma, “wanda yake da ꞌyanci” yana nufin wanda aka fitar da shi daga bauta. Idan gwamnati ce ta ba shi ꞌyanci, zai zama ɗan Roma, amma ba zai iya samu matsayi na siyasa ba. Idan ubangijin bawan ne ya ba shi ꞌyancin, ba zai sami cikakken izini na ɗan Roma ba.—1Ko 7:22.
-
Majamiꞌa.
Kalmar da ke nufin “tara wuri ɗaya ko kuma taro,” amma a yawancin nassosi, kalmar tana nufin gini ko wurin da Yahudawa suke taro don su karanta Nassi, a koyar da su, su yi waꞌazi da kuma adduꞌa. A zamanin Yesu, kowane babban gari a Israꞌila na da majamiꞌa, kuma manyan birane suna da majamiꞌa fiye da ɗaya.—Luk 4:16; A.M 13:14, 15.
-
Makidoniya.
Wani yanki da ke arewacin Girka, wanda ya zama sananne a ƙarƙashin mulkin Alekzanda Mai Girma kuma yankin ya ci-gaba da kasancewa da ꞌyancin kai kafin lokacin da Romawa suka mallake shi. Makidoniya yankin Roma ne saꞌad da manzo Bulus ya kai ziyararsa ta farko a Turai. Bulus ya ziyarci yankin nan sau uku.—A.M 16:9.
-
Maƙiyin Kristi.
A yaren Girka, furucin yana da maꞌana biyu. Yana nufin yin gāba da Kristi. Yana kuma iya nufin Kristin ƙarya, wato wanda ya ɗauki matsayin Kristi. Dukan mutane, ko ƙungiyoyi, ko rukunoni, da suke cewa suna wakiltar Kristi, ko sun ce su Almasihu ne, ko kuma waɗanda suke gāba da Kristi da almajiransa, ana iya kiran su maƙiyan Kristi.—1Yo 2:22.
-
Makoki.
Abin da mutum yake yi don ya nuna baƙin cikinsa saboda mutuwa ko kuma wani balaꞌi. A zamanin dā, mutane sukan ɗau lokaci suna makoki. Ban da yin kuka da babbar murya, masu makoki suna saka riguna na musamman, da zuba toka a kansu, da yayyage rigunansu, da kuma buga ƙirjinsu da hannu. A wasu lokuta, akan gayyaci masu makoki na musamman a wurin janaꞌiza.—Est 4:3; Mat 11:17; Mrk 5:38; Yoh 11:33; R.Y 21:4.
-
Malaꞌiku.
An samo kalmar ne daga kalmar Ibrananci mal·ʼakhʹ da na yaren Girka agʹge·los. Kalmomi biyun suna nufin “ɗan aika,” amma idan ana magana game da ꞌyan aika na ruhu, akan fassara su zuwa “malaꞌika.” (Far 16:7; 32:3; Yaƙ 2:25; R.Y 22:8) Malaꞌiku halittun ruhu ne masu iko sosai, Allah ya halicce su da daɗewa kafin ya halicci mutane. A cikin Littafi Mai Tsarki, ana kuma kiran su “ꞌyaꞌyan Allah,” da kuma “taurarin safe.” (Ayu 1:6; 38:7) Allah bai halicce su yadda za su iya haifan wasu malaꞌiku ba, amma ya halicce su ɗaɗɗaya. Yawansu ya fi miliyan ɗari. (Dan 7:10) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa suna da sunaye da halaye da sun bambanta kowannensu, duk da haka sun ƙi a bauta musu, kuma yawancinsu ma ba sa faɗan sunayensu. (Far 32:29; Luk 1:26; R.Y 22:8, 9) Suna da matsayi da ayyuka dabam-dabam, kuma hakan ya haɗa da yin hidima a gaban kujerar mulki na Jehobah, da gaya wa mutane saƙonninsa, da taimaka wa bayin Jehobah a duniya, da zartar da hukunce-hukunce na Allah, da kuma goyon bayan waꞌazin labari mai daɗi. (2Sr 19:35; Za 34:7; Mat 4:11; Luk 1:30, 31; R.Y 5:11; 14:6) A nan gaba, za su taimaka wa Yesu a yaƙin Armageddon.—R.Y 19:14, 15.
-
Manna.
Shi ne abincin da Israꞌilawa suka ci a yawancin lokaci a cikin shekara arbaꞌin da suka yi a daji. Jehobah ne ya tanadar da abincin. Kowace safiya, ban da Ranar Assabaci, Jehobah ya sa manna ya bayyana a ƙasa a ƙarƙashin raɓa. Da Israꞌilawa suka fara ganin sa, sun ce “Mene ne wannan?” ko kuma, a Ibrananci, “man huʼ?” (Fit 16:13-15, 35) Yesu ma ya yi kwantanci da manna.—Yoh 6:49, 50.
-
Manzo.
-
Marar yisti.
Yana nufin burodi da aka yi ba tare da yisti ba.—M.S 16:3; Mrk 14:12; 1Ko 5:8.
-
Marubuci.
Mutumin da ke kwafan Nassosin Ibrananci. A lokacin da Yesu yake duniya, kalmar tana nufin rukunin mutanen da suka san Doka sosai. Sun yi gāba da Yesu.—Ezr 7:6; Mrk 12:38, 39; 14:1.
-
Masanin taurari.
Yana nufin mutumin da yake nazarin yadda rana, da wata, da taurari suke tafiya don ya yi hasashen abin da zai faru a gaba.—Mat 2:1.
-
Masu Gadin Sarki.
Rukunin sojojin Roma da aka kafa don su riƙa gadin sarkin Roma. Daga baya sun kasance da iko sosai a batun siyasa don ana amfani da su wajen goyon bayan sarki ko kuma yi masa juyin mulki.—Fib 1:13.
-
Midiyawa.
Mutane ne da suka fito daga zuriyar ɗan Jefta mai suna Madai; sun yi rayuwa a yankunan tuddai na ƙasar Iran wanda daga baya ya zama ƙasar Midiya. Midiyawa suna Urushalima a Ranar Fentikos na shekara ta talatin da uku bayan haihuwar Yesu.—A.M 2:9.
-
Mil.
Yadda ake gwada nisan wuri, kuma ya bayyana sau ɗaya a cikin rubuce-rubucen Nassosin Girkanci na Krista na asali a Matiyu 5:41, mai yiwuwa yana nufin mil na Romawa da nisansa ya kai mita 1,479.5 (ƙafa 4,854).
-
Mina.
A Nassosin Girkanci na Krista, mina ɗaya ya yi daidai da drakma ɗari. Nauyinsa ya kai giram ɗari uku da arbaꞌin.—Luk 19:13.
-
Molok.
Wannan shi ne allahn Ammonawa; mai yiwuya ɗaya yake da Malkam, da Milkom, da kuma Molek.—A.M 7:43.
-
Mugun nan.
-
Mulkin Allah.
Furucin na nufin gwamnatin da ke nuna cewa Allah ne ya cancanci ya yi mulki, kuma Ɗansa, Yesu Kristi ne sarki.—Mat 12:28; Luk 4:43; 1Ko 15:50.
-
Mur.
Wani gam mai ƙamshi da ake samuwa daga ƙananan itatuwan kaya da ake kira Commiphora. Mur yana ɗaya daga cikin abubuwan da ake haɗawa wajen yin māi da ake shafa wa mutum don a nuna cewa an zaɓe shi. Ana amfani da shi wajen sa riguna ko gado su yi ƙamshi, kuma ana sakawa a cikin māi da ake matsa jiki da shi da kuma wanda ake shafawa a jiki. Ana haɗa shi da ruwan inabi don ya bugar da mutum ko kuma ya hana shi jin zafi. Ana kuma amfani da mur wajen shirya gawa don bizina.—Fit 30:23; K.M 7:17; Mrk 15:23; Yoh 19:39.
-
Murfin hadaya ta sasantawa.
Wannan shi ne murfin akwatin yarjejeniya, wanda a gabansa ne shugaban firistoci yakan yayyafa jinin hadayu na zunubi a Ranar Neman Gafara. A Ibrananci, kalmar nan “murfi” an samo ta ne daga kalmar da ke nufin “a rufe (zunubi)” ko kuma wataƙila “a share (zunubi).” An yi shi da zinariya zalla, da siffofin cerub guda biyu, ɗaya a gefen nan, ɗaya kuma a wancan gefen.—Fit 25:17-22; 1Tr 28:11; Ibr 9:5.
-
Mutanen da ke goyon bayan Hirudus.
Masu kishin ƙasa ne da suke goyon bayan siyasar ꞌyan iyalin Hirudus a sarautarsu a ƙarƙashin Romawa. Mai yiwuwa wasu Sadukiyawa suna cikin magoya bayan Hirudus. Waɗannan mutanen sun haɗa kai da Farisiyawa don su yi adawa da Yesu.—Mrk 3:6.
-
Mutumin Girka.
Wanda iyalinsa sun samo asali daga Girka. A Nassosin Girkanci na Krista, ana amfani da furucin a yanayoyi dabam-dabam, yana nufin duk wanda ba Bayahude ba ne ko kuma wanda yare da kuma alꞌadar mutanen Girka suka shafa.—Jow 3:6; Yoh 12:20.
-
Mutumin Itiyofiya.
Duk wanda ya fito daga Itiyofiya, wata ƙasa a zamanin dā da ke kudancin ƙasar Masar, wadda ta haɗa ta kudancin ƙasar Masar da Sudan na yau.—A.M 8:27.
-
Mutumin Nazaret.
N
-
Nad.
Wani irin māi ne mai jar kala, mai ƙamshi, kuma mai sada sosai da ake samuwa daga wani irin itace da ake kira Nardostachys jatamansi. Da yake yana da sada sosai, ana yawan haɗa nad da wasu māi da ba su da sada, ko kuma a yi jabun sa. Shi ya sa Markus da Yohanna suka ce “nad zalla” ne matar ta zuba a kan Yesu.—Mrk 14:3; Yoh 12:3.
-
Naɗaɗɗen littafi.
Dogon takarda ne da aka yi da fatar dabba ko kuma wata ciyawa da ake kira papyrus kuma yana ɗauke da rubuta a gefe ɗaya. Ana kuma naɗe shi a jikin sanda. An rubuta nassosi a kan naɗaɗɗen littafi kuma an kwafe su a kan naɗaɗɗen littafi, shi ne irin littafin da ake amfani da shi a zamanin dā.—Luk 4:17-20; 2Ti 4:13.
-
Nassosi.
Kalmar tana nufin rubuce-rubuce masu tsarki na Kalmar Allah. A Nassosin Girkanci na Krista ne kawai kalmomin nan suka bayyana.—Luk 24:27; 2Ti 3:16.
-
Nisan.
Sabon sunan da aka ba ma watan Abib, bayan da Yahudawa suka dawo daga bauta a Babila. Shi ne wata na farko a kalandar Yahudawa, amma wata na bakwai a kalandarsu ta yau da kullum. Watan yakan soma daga tsakiyar Maris zuwa tsakiyar Afrilu. (Neh 2:1) A ranar 14 ga watan Nisan ne Yahudawa sukan yi Bikin Ƙetarewa, kuma Yesu ya kafa taron da ake kira Abincin Yamma na Ubangiji a ranar. (Luk 22:15, 19, 20) A ranar ce kuma aka kashe shi a kan gungumen azaba.—Luk 23:44-46.
-
Nunan fari.
ꞌYaꞌyan itatutuwa na farko da suke fitowa a lokacin girbi; abu na farko da ake samuwa daga kome. Jehobah ya bukaci alꞌummar Israꞌila su riƙa ba shi nunan fari, ko na mutum ne, ko na dabba, ko kuma na amfanin gonarsu. Kuma a matsayinsu na alꞌumma, Israꞌilawa sun miƙa nunan fari a Bikin Burodi Marar Yisti da kuma Bikin Fentikos. An yi amfani da furucin nan “nunan fari” a matsayin misali ga Yesu da kuma mabiyansa shafaffu.—1Ko 15:23; Ƙid 15:21; K.M 3:9; R.Y 14:4.
P
-
Porneia.—
Ka duba LALATA.
-
Psy·kheʹ.
Binciken yadda aka yi amfani da kalmar nan a cikin Littafi Mai Tsarki, yana nuna a bayyane cewa an yi amfani da kalmar ne saꞌad da ake magana game da (1) mutane, (2) dabbobi, ko kuma (3) ran mutum ko na dabba. (1Bi 3:20) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa psy·kheʹ na kamar sauran abubuwa da Allah ya halitta a duniya, waɗanda za mu iya taɓa su, mu gan su, kuma za su iya mutuwa. A wannan juyin, an fassara wannan kalma ta asali bisa ga maꞌanar abin da ake magana a kai, ta wurin amfani da kalmomi kamar “rai,” “halitta,” “mutum,” ko kuma “dukan jikin mutum.”
R
-
Rabbai.
Kalmar nan a yaren Girka, tana nufin ‘maigirmana.’ Idan aka yi amfani da kalmar a magana ta yau da kullum, ‘Rabbai’ na nufin ‘malami’ (Yoh 1:38), amma daga baya an soma amfani da kalmar a matsayin laƙabi na ban girma. Wasu mutane masu ilimi, da marubuta, da kuma malaman koyar da Dokar Musa, sun bukaci a kira su da wannan laƙabin.
-
Ranar Assabaci.
An samo furucin ne daga kalmar Ibrananci da ke nufin “a huta ko a daina aiki.” Rana ta bakwai ce a makon Yahudawa (wato daga faɗuwar rana ta ranar Jummaꞌa zuwa faɗuwar rana ta ranar Asabar). Wasu bukukuwa da ake yi a shekara, da ma shekara ta bakwai, da shekara ta hamsin ma ana kiran su assabaci. Ba a yin aiki a Ranar Assabaci, sai dai ayyukan da firistoci suke yi a haikali. A shekarun Assabaci, Ibraniyawa ba sa nome ƙasarsu, kuma ba sa matsa wa ꞌyanꞌuwansu su biya su bashin da suke bin su. A cikin Dokar Musa, abubuwan da aka hana yi a Ranar Assabaci ba su da wuyan bi, amma a hankali shugabannin addinai sun ƙara abubuwan da bai kamata mutum ya yi ba. Shi ya sa a zamanin Yesu, ya yi wa mutane wuya su bi abubuwan nan.—Fit 20:8; Fir 25:4; Luk 13:14-16; Kol 2:16.
-
Ranar Neman Gafara.
Ita ce rana mafi muhimmanci a cikin ranaku masu tsarki ga Israꞌilawa. Ana kuma kiran ranar Yom Kippur (daga Ibrananci yohm hak·kip·pu·rimʹ, wato “ranar rufewa”). Akan yi shi a ranar 10 ga watan Etanim. A wannan rana ce kawai shugaban firistoci yake shiga Wuri Mafi Tsarki na tentin saduwa don ya miƙa jinin hadayu na zunubansa, da zunuban sauran Lawiyawa, da kuma zunuban mutane. Waɗannan hadayun suna nuna irin hadayar da Yesu zai bayar, wadda za ta sa ꞌyanꞌadam su sami gafara daga zunubansu sau ɗaya tak har abada, da kuma ba su damar yin sulhu da Jehobah. A lokacin, suna yin taro mai tsarki da azumi, kuma ranar Ranar Assabaci ce, da mutane ba sa yin ayyukan da suka saba yi.—Fir 23:27, 28; A.M 27:9; Kol 1:20; Ibr 9:12.
-
Ranar Shariꞌa.
Rana ce ko kuma lokaci, da wasu rukunoni, ko ƙasashe, ko kuma dukan mutane suke ba da lissafin ayyukansu ga Allah. Za ta iya zama lokaci da za a hallaka waɗanda aka yanke musu hukuncin kisa. Shariꞌar za ta iya ba wasu daman samun ceto kuma su yi rayuwa har abada. Yesu da almajiransa sun yi magana game da “Ranar Shariꞌa” da za ta zo a nan gaba, kuma a lokacin, za a yi wa masu rai da kuma matattu shariꞌa.—Mat 12:36.
-
Ranar Shiri.
Sunan da ake kiran rana kafin Ranar Assabaci. A ranar, Yahudawa sukan yi shirye-shirye don Ranar Assabaci. Ranar takan ƙare ne bayan faɗuwar rana ta ranar Jummaꞌa ta zamaninmu, kuma a lokacin ne Ranar Assabaci take somawa. Ranar Yahudawa takan soma daga yamma zuwa yammar washegari.—Mrk 15:42; Luk 23:54.
-
Rantsuwa.
Magana ce da mutum yake yi don ya nuna cewa wani abu gaskiya ne, ko kuma alkawari na musamman cewa mutum zai yi wani abu ko kuma ba zai yi ba. A yawancin lokaci, alkawari ne da ake yi ga wanda ya fi iko, musamman ga Allah. Jehobah ya daɗa nanata yarjejeniyarsa da Ibrahim ta wajen yin rantsuwa.—Far 14:22; Ibr 6:16, 17.
-
Ridda.
Wannan kalmar a yaren Girka (a·po·sta·siʹa) an samo ta ne daga wata kalma da ke nufin “yin tsayayya da.” Kalmar tana kuma iya nufin, “barin abu, ko yin watsi, ko kuma tawaye.” An yi amfani da kalmar nan “ridda” a cikin Nassosin Girkanci na Krista saꞌad da ake magana game da waɗanda suka bar bauta ta gaskiya.—K.M 11:9; A.M 21:21; 2Ta 2:3.
-
Rigar makoki.
Wani yadi marar laushi da ake amfani da shi wajen yin buhuna ko kuma jakunkuna, kamar waɗanda ake ɗaukan hatsi da su. Akan saƙa yadin ne da gashin baƙin akuya kuma shi ne aka saba sakawa saꞌad da ake makoki.—Far 37:34; Luk 10:13.
-
Ruhu.
Ana yawan fassara kalmar Ibranancin nan ruʹach da kalmar nan pneuʹma, a yaren Girka zuwa “ruhu,” amma tana da maꞌana dabam-dabam. Dukansu suna nufin abin da ꞌyanꞌadam ba za su iya gani ba, amma za su iya ganin abubuwan da yake yi. A Ibrananci da yaren Girka, kalmar tana iya nufin (1) iska, (2) numfashi na rai da ke cikin halittu da ke duniya, (3) abin da ke sa mutum ya faɗa ko ya yi wani abu a wata hanya, (4) saƙonni da suka fito daga halittun da ba a iya gani, (5) halittun ruhu, da kuma (6) ikon da Allah yake aiki da shi ko kuma ruhu mai tsarki.—Fit 35:21; Za 104:29; Mat 12:43; Luk 11:13.
-
Ruhu mai tsarki.
-
Rumfar Sulemanu.
A haikali na zamanin Yesu, wannan wata hanya ce da ke da rumfa a gabashin farfajiyar haikalin. Mutane da yawa sun yi imani cewa wannan wani ɓangare ne da ya rage daga haikalin Sulemanu. Yesu ya bi wurin a “lokacin sanyi” kuma a wurin ne Kristocin ƙarni na farko suke haɗuwa su yi ibada.—Yoh 10:22, 23; A.M 5:12.
S
-
Sa hannu a kai.
-
Sabon wata.
Rana ta farko a kowane wata na kalandar Yahudawa. A ranar, Yahudawa sukan taru, da yin biki, da kuma miƙa hadayu na musamman. Daga baya, ta zama ranar da ake yin biki na musamman a ƙasa gabaki-ɗaya, kuma mutane ba sa yin aiki a ranar.—Ƙid 10:10; 2Tr 8:13; Kol 2:16.
-
Sadukiyawa.
Wani sanannen rukunin addinin Yahudawa. Rukunin ya ƙunshi manyan mutane masu arziki da firistoci da suke nuna iko sosai a ayyukan da ake yi a haikali. Sun ƙi bin alꞌadun da Farisiyawa suka faɗa da baki da kuma wasu abubuwan da Farisiyawa suka yi imani da su. Ba su yarda cewa za a yi tashin matattu ba, kuma ba su yarda cewa akwai malaꞌiku ba. Sun yi gāba da Yesu.—Mat 16:1; A.M 23:8.
-
Salka.
Wata jaka da aka yi da fatar dabba zalla, kamar fatar akuya ko ta rago, da ake amfani da ita a zuba ruwan inabi. Akan zuba sabon ruwan inabi a cikin sababbin salkuna, domin yayin da ruwan inabin yake ƙara tsami, yana tara iska da ke sa salkunan su kumbura. Sababbin salkuna sukan ƙara girma, amma maimakon tsofaffin salkuna su ƙara girma, sukan fashe.—Jos 9:4; Mat 9:17.
-
Samariya.
Wannan shi ne babban birnin kabilu goma da suka kafa mulkinsu a arewacin Israꞌila, na wajen shekaru ɗari biyu. Shi ne kuma sunan yankin gabaki-ɗaya. An gina birnin a tudun da ke ɗauke da sunan. A zamanin Yesu, Samariya sunan yankin Roma ne da ke tsakanin Galili da ke arewa da kuma Yahudiya da ke kudu. Yesu yakan ƙi yin waꞌazi a yankin saꞌad da yake tafiye-tafiyensa, amma a wasu lokuta ya bi ta wurin kuma ya yi wa mazaunan yankin waꞌazi. Bitrus ya yi amfani da mabuɗin alama na biyu na Mulkin saꞌad da Samariyawa suka karɓi ruhu mai tsarki.—1Sr 16:24; Yoh 4:7; A.M 8:14.
-
Samariyawa.
Asali kalmar tana nufin Israꞌilawa daga kabilu goma da suka kafa mulki a arewancin ƙasar. Amma bayan da mutanen Assiriya suka ci Samariya da yaƙi a shekara ta ɗari bakwai da arbaꞌin kafin haifuwar Yesu, Samariyawa sun haɗa da baƙi da mutanen Assiriya suka kawo. A zamanin Yesu, sunan ba shi da alaƙa da kabila ko kuma siyasa, amma yana nufin waɗanda suke bin rukunin addini da ke yankin Shekem da Samariya na dā. Wannan rukunin suna bin wasu imani da suka yi dabam da na addinin Yahudawa.—Yoh 8:48.
-
Sandar mulki.
Wani sanda ne da sarakuna suke riƙewa da ke nuna cewa suna da ikon sarauta.—Far 49:10; Ibr 1:8.
-
Sanhedrin.
Shi ne kotun ƙolin Yahudawa da ke Urushalima. A zamanin Yesu, kotun yana da membobi sabaꞌin da ɗaya, hakan ya haɗa da shugaban firistoci, da wasu da suka riƙe matsayin shugaban firistoci a dā, da membobin iyalan shugabannin firistocin, da dattawa, da shugabanin kabilu, da iyalai, da kuma marubuta.—Mrk 15:1; A.M 5:34; 23:1, 6.
-
Shafe.
Kalmar Ibrananci da aka fassara zuwa “shafe,” tana nufin a “zuba abu mai ruwa-ruwa a kan wani abu.” Akan zuba māi a kan mutum ko kuma wani abu don a nuna an keɓe mutumin ko kuma abin don aiki na musamman. An kuma yi amfani da kalmar a Nassosin Girkanci na Krista don a nuna yadda Allah ya zuba ruhu mai tsarki a kan waɗanda ya zaɓa su je sama.—Fit 28:41; 1Sm 16:13; Luk 4:18; A.M 10:38; 2Ko 1:21.
-
Shaiɗan.
-
Shugaba.
-
Shugaban firistoci.
A Dokar Musa, shi ne firist na musamman da ke yi wa Allah hidima a madadin mutane, kuma shi ne ke kula da aikin sauran firistocin. Shi kaɗai ne yake shiga Wuri Mafi Tsarki, wato wurin da ke cikin-cikin tentin saduwa kuma daga baya a haikali. Yakan yi hakan ne kawai a Ranar Neman Gafara. An kuma kira Yesu Kristi “shugaban firistoci.”—Fir 16:2, 17; 21:10; Mat 26:3; Ibr 4:14.
-
Shugaban malaꞌiku.
-
Shuki Mai Ɗaci.
Wannan yana nufin shuke-shuke dabam-dabam masu ɗaci sosai kuma suna da ƙamshi sosai. A Ruꞌuya ta Yohanna 8:11, “shuki mai ɗaci” (a yaren Girka, aʹpsin·thos) yana nufin abu mai ɗaci da kuma guba.
-
Sihiri.
Abu ne da mutane suke yi domin sun yi imani cewa saꞌad da mutum ya mutu, akwai wani abu da ke jikinsa da ba ya mutuwa, kuma mutanen da suka mutu za su iya magana kuma suna magana da mutanen da suke da rai. Sun yi imani cewa, a lokuta da yawa, mutanen da suka mutu suna amfani da mutum (ko kuma wani abu) don su yi magana da mutane. Kalmar yaren Girka da ke nufin “yin sihiri” ita ce phar·ma·kiʹa, kuma a zahiri tana nufin “buguwa da ƙwaya.” An soma amfani da furucin nan saꞌad da ake magana game da sihiri, domin a zamanin dā, mutane suna amfani da ƙwayoyi su kira aljanu don su ba su iko.—Gal 5:20; R.Y 21:8.
-
Sihiyona; Tudun Sihiyona.
Sunan birni mai katanga na Jebusiyawa ne da ake kira Jebus da ke kudu maso gabas na tudun Urushalima. Bayan da Dauda ya ci nasara a kan birnin, ya gina fādarsa a wurin, kuma aka soma kiran wurin “Birnin Dauda.” (2Sm 5:7, 9) Sihiyona ya zama tudu mai tsarki ga Jehobah saꞌad da Dauda ya kaurar da Akwatin Yarjejeniya zuwa wurin. Daga baya, an soma kiran wani ɓangaren haikali da ake kira Tudun Moraya, da wannan sunan. A wasu lokuta ma, haka ake kiran birnin Urushalima gabaki-ɗaya. An kuma yi kwatanci da shi sosai a cikin Nassosin Girkanci na Krista.—Za 2:6; 1Bi 2:6; R.Y 14:1.
-
Siriya; Siriyawa.
A Nassosin Girkanci na Krista, Siriya wani yanki ne da ke ƙarƙashin mulkin Roma, kuma Antakiya ne babban birninsa. Yankin ya haɗa da yawancin wuraren da ke Siriya (ana kuma kiran sa Aram) a Nassosin Ibrananci. Gwamnan Siriya ne kuma yake kula da dukan yankin Falasɗinu.—Luk 2:2; A.M 18:18; Gal 1:21.
-
Sirri mai tsarki.
-
Sirtis.
Manyan wurare biyu ne da ke gaɓar tekun Tunisiya da Libiya, a Arewacin Afrika. Wurare biyun ba su da zurfi kuma matukan jirgin ruwa a zamanin dā suna tsoron wuraren saboda yashin da rakuman ruwa suke tarawa a wuraren.—A.M 27:17.
T
-
Tafkin wuta.
Wuri ne na alama “da ke ci da wuta da kuma sulfur,” an kuma kira shi “mutuwa ta biyu.” A ciki ne aka jefa masu zunubi da ba su tuba ba, da Ibilis, da mutuwa da kuma Kabari (ko Hades). Tun da yake an haɗa abubuwa kamar halittu na ruhu, da mutuwa, da Hades, waɗanda dukansu wuta ba ta cin su, ya nuna cewa wannan tafkin alama ne na hallaka ta har abada maimakon na azaba har abada.—R.Y 19:20; 20:14, 15; 21:8.
-
Talenti.
A Ibrananci, shi ne maꞌauni mafi girma na gwada nauyin abu ko na gwada yawan kuɗi. Nauyinsa ya kai kilo 34.2. Talentin Girka ƙarami ne, kuma nauyinsa wajen kilo 20.4.—1Tr 22:14; Mat 18:24.
-
Tashin matattu.
Furucin nan a yaren Girka shi ne a·naʹsta·sis kuma yana nufin “tashi tsaye.” A cikin Littafi Mai Tsarki, an ambata tashin matattu guda tara, a ciki har da ta da Yesu da Jehobah ya yi. Ko da yake Iliya, da Elisha, da Yesu, da Bitrus, da kuma Bulus sun ta da mutane daga mutuwa, sun yi hakan ne da ikon Allah. Tashin matattu “na masu adalci da na marasa adalci” da za a yi a duniya yana da muhimmanci wajen cika nufin Allah. (A.M 24:15) Littafi Mai Tsarki ya kuma yi magana game da tashin matattu na waɗanda za su je sama. An kira shi “tashin matattu na farko.” Waɗanda za a ta da su ne ꞌyanꞌuwan Yesu waɗanda aka shafe su da ruhu mai tsarki.—Fib 3:11; R.Y 20:5, 6; Yoh 5:28, 29; 11:25.
-
Tataros.
A cikin Nassosin Girkanci na Krista, yana nufin wani yanayi da ke kama da kurkuku da aka jefa malaꞌiku marasa biyayya na zamanin Nuhu. A littafin 2 Bitrus 2:4, an yi amfani da kalmar nan tar·ta·roʹo (wato “jefa cikin Tataros”), amma hakan ba ya nufin cewa an jefa “malaꞌikun da suka yi zunubi” cikin wani wurin da masu bautar gumaka suke kiran Tataros (wato kurkuku da ke ƙarƙashin ƙasa da kuma wuri mai duhu don ƙananan alloli). Maimakon haka, yana nufin cewa Allah ya ƙore su daga sama kuma ya ƙwace matsayinsu, ya kuma sa tunaninsu ya yi duhu sosai har ba za su iya gane nufin Allah ba. Duhun kuma yana nufin abin da zai faru da su a ƙarshe, wato hallaka ta har abada tare da Shaiɗan Ibilis kamar yadda Nassosi suka nuna. Saboda haka, Tataros yana nufin cewa an saka waɗannan malaꞌiku masu tawaye cikin yanayin da za su sha wulaƙanci sosai. Tataros ba ɗaya yake da “ramin nan marar iyaka” da aka ambata a Ruꞌuya ta Yohanna 20:1-3 ba.
-
Tauraron safe.
Tauraro na ƙarshe da ke taso daga gabas kafin rana ta fito, hakan na nuna somawar sabuwar rana.—R.Y 22:16; 2Bi 1:19.
-
Tsabta.
A Littafi Mai Tsarki, wannan kalmar ba ta nufin tsabta na zahiri kawai, ana kuma amfani da kalmar saꞌad da ake magana game da yanayi ko kuma maido da yanayi marar tabo. Ƙari ga haka, ana amfani da ita saꞌad da ake magana a kan wani abu da ba zai iya sa wani abu datti ba, ko wani abin da ba zai iya ɓata wani abu ko ɓata halin mutum da yadda yake bauta wa Allah ba. A Dokar Musa, kalmar tana nufin mutum ya kasance da tsabta yadda Doka ta ce.—Fir 10:10; Za 51:7; Mat 8:2; 1Ko 6:11.
-
Tsarki.
Wanda yake da tsarki shi ne wanda halayensa suke da tsabta kuma bai da tabo ko kaɗan. Jehobah ne kaɗai yake da tsarki ta kowace hanya. (Fit 28:36; 1Sm 2:2; Yoh 17:11) Saꞌad da ake magana game da ꞌyanꞌadam (Mrk 6:20; A.M 3:21), da abubuwa (Rom 7:12; 11:16; 2Ti 3:15), da wurare (Mat 4:5; A.M 7:33; Ibr 9:1), da kuma ayyuka (Fit 36:4), kalmar nan a Ibrananci da yaren Girka tana nufin a ware ko kuma a tsarkake abu don Allah mai tsarki; yana kuma nufin mutum ya keɓe kansa don yin hidimar Jehobah. A Nassosin Girkanci na Krista, kalmar nan “tsarki” tana kuma iya nufin mutum ya kasance da tsarki a halinsa.—2Ko 7:1; 1Bi 1:15, 16.
-
Tuba.
-
Turaren wuta.
Busasshen gam daga itatuwa da kuma wasu irin ciyayi da ake kira Boswellia. Idan aka ƙona, yakan yi ƙamshi sosai. Akan saka shi a cikin turare mai tsarki da aka yi amfani da shi a tentin saduwa da kuma haikali. An kuma yi amfani da shi tare da hadayun hatsi, ƙari ga haka an saka shi a kowane layi da ake sa burodi a cikin Wuri Mai Tsarki.—Fit 30:34-36; Fir 2:1; 24:7; Mat 2:11.
W
-
Wuri Mafi Tsarki.
Wannan shi ne ɗakin da ke cikin-cikin tentin saduwa da kuma haikali, inda ake ajiye akwatin yarjejeniya. Ban da Musa, wani da aka amince masa ya shiga Wuri Mafi Tsarki shi ne shugaban firistoci, kuma zai yi hakan ne kawai a Ranar Neman Gafara.—Fit 26:33; Fir 16:2, 17; 1Sr 6:16; Ibr 9:3.
-
Wuri Mai Tsarki.
Shi ne ɗaki na farko kuma mafi girma a tentin saduwa ko haikali, kuma ya bambanta da ɗaki da ke ciki-ciki, wato Wuri Mafi Tsarki. A tentin saduwa, abubuwan da suke cikin Wuri Mai Tsarki su ne sandar riƙe fitila na zinariya, da bagaden zinariya na ƙona turare, da teburin da ake ajiye burodi, da wasu abubuwan da aka yi da zinariya. A haikali kuma, abubuwan da suke cikin Wuri Mai Tsarki su ne bagaden zinariya, da sandar riƙe fitila guda goma na zinariya, da tebura goma na ajiye burodi.—Fit 26:33; Ibr 9:2.
-
Wurin matse ꞌyaꞌyan inabi.
Wannan ramuka biyu ne da aka tona a cikin farar ƙasa, ɗaya ya fi ɗayan zurfi, kuma akwai ɗan ƙaramar hanya da ta haɗa ramuka biyun. Yayin da ake matse ꞌyaꞌyan inabi a cikin rami marar zurfin, ruwan inabin yana gangarowa zuwa cikin rami mai zurfin. An yi amfani da furucin nan don a kwatanta hukuncin Allah.—R.Y 19:15.
Y
-
Yahuda.
Ɗan Yakubu na huɗu ta wurin matarsa Liyatu. Saꞌad da Yakubu yake gab da mutuwa ya annabta cewa wani mai iko da zai yi mulki har abada zai fito daga iyalin Yahuda. A matsayinsa na mutum, Yesu ya fito daga zuriyar Yahuda. Ana kiran kabilar da suna Yahuda, kuma daga baya an kira wani mulki da suna Yahuda.—Far 29:35; 49:10; Ibr 7:14.
-
Yakubu.
Ɗan Ishaku da Rifkatu. Daga baya, Allah ya ba shi suna Israꞌila, kuma ya zama uban mutanen Israꞌila (an kuma kira su Israꞌilawa kuma daga baya Yahudawa). Shi ne uban ꞌyaꞌya goma sha biyu waɗanda tare da zuriyarsu suka zama kabilu goma sha biyu na alꞌummar Israꞌila. An ci-gaba da kiran alꞌummar ko kuma mutanen Israꞌila da sunan nan Yakubu.—Far 32:28; Mat 22:32.
-
Yarjejeniya.
Alkawari ne tsakanin Allah da mutane, ko kuma tsakanin mutane biyu don su yi wani abu ko su ƙi yin wani abu. A wasu lokuta, mutum ɗaya ne yake yin abin da ke cikin yarjejeniyar. A wasu lokuta kuma, mutane biyu ne ke yin abin da ke cikin yarjejeniyar. Ban da yarjejeniya da Allah ya yi da ꞌyanꞌadam, Littafi Mai Tsarki ya ambata yarjejeniya tsakanin mutane, da kabilu, da alꞌummai, ko kuma rukunin mutane. Yarjejeniya da Allah ya yi da Ibrahim, da Dauda, da alꞌummar Israꞌila (yarjejeniya da aka yi ta wurin Dokar), da Israꞌila ta Allah (sabuwar yarjejeniya) suna cikin yarjejeniyoyi da suka fi shafan mutane.—Far 9:11; 15:18; 21:27; Fit 24:7; 2Tr 21:7; Luk 22:29; A.M 3:25; 2Ko 3:6; Ibr 8:6.
-
Yin ibada da dukan zuciya.
-
Yisti.
Wani abu ne da ake sakawa a cikin fulawa da aka kwaɓa don a sa shi ya kumbura, ko kuma a saka a cikin abin sha don a sa ya yi tsami; musamman fulawar da aka yanka daga ƙullun fulawar da ya kumbura kuma aka ajiye shi. Sau da yawa, kalmar a Littafi Mai Tsarki tana wakiltar zunubi ko kuma ruɓewa. Ana kuma amfani da shi don bayyana abin da ke girma da yaɗuwa a ɓoye.—Fit 12:20; Mat 13:33; Ga 5:9.
Z
-
Zabura.
Waƙa ce ta yabo ga Allah. Ana amfani da kalmomin zabura a shirya kiɗi, kuma masu bauta wa Jehobah Allah suna rera ta saꞌad da suke sujada a haikalinsa da ke Urushalima.—Luk 20:42; A.M 13:33; Yaƙ 5:13.
-
Zamani.
Yadda ake fassara kalmar Girkanci nan ai·onʹ ke nan, idan ana magana game da abubuwan da suka sa wani lokaci ya yi dabam da sauran lokuta. Littafi Mai Tarki ya yi amfani da furucin nan “zamanin nan,” saꞌad da yake magana game da abubuwan da suke faruwa da kuma irin rayuwar da mutane suke yi a duniya. (2Ti 4:10) Ta wurin yarjejeniyar da aka yi da Doka, Allah ya kawo wani zamani da wasu suke kira zamanin Israꞌilawa ko kuma zamanin Yahudawa. Saꞌad da Yesu ya ba da ransa a matsayin fansa, Allah ya yi amfani da shi ya soma wani zamani dabam. Zamanin ya ƙunshi musamman shafaffun Kristoci. Hakan ya soma wani sabon zamani wanda ya nuna asalin abubuwan da yarjejeniya da aka yi da Doka take wakilta. Idan kuma aka ce zamanai, ana nufin lokuta da yawa da yanayoyi dabam-dabam da suka wuce ko kuma wanda suke zuwa.—Mat 24:3; Mrk 4:19; Rom 12:2; 1Ko 10:11.
-
Zeno.
Mai koyar da ilimin duniya ne wanda ya ce mutane suna bukatar su riƙa yin tunani sosai don su fahimci yadda abubuwa suke faruwa yau da kullum. Kuma ya ce mai hikima, shi ne wanda bai damu da baƙin ciki ko kuma farin ciki ba. Ana kuma kiran mabiyan Zeno ‘Sitokiyawa.’—A.M 17:18.
-
Zeyus.
Shi ne allah mafi girma a cikin allolin da mutanen Girka suke yi wa bauta. A birnin Listra, an kira Barnabas Zeyus cikin kuskure. An samu wasu abubuwan dā kusa da Listra da ke ɗauke da rubutu da ya ce “firistocin Zeyus” da kuma “Zeyus allahn rana.” Jirgin ruwa da Bulus ya shiga daga tsibirin Malta na ɗauke da siffar “ꞌYaꞌyan Zeyus,” wato ꞌyanꞌuwa tagwaye masu suna Castor da Pollux.—A.M 14:12; 28:11.
-
Zina.

