Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya

Gabatarwar Littafi Mai Tsarki​—⁠Fassarar Sabuwar Duniya

Hausa
Gabatarwar Littafi Mai Tsarki​—⁠Fassarar Sabuwar Duniya
https://cms-imgp.jw-cdn.org/img/p/1001061100/univ/wpub/1001061100_univ_sqr_xl.jpg
nwt p. 39

Gabatarwa

Allah ne ya ja-goranci waɗanda suka rubuta Nassosi Masu Tsarki a Ibrananci, da yaren Aramaik, da kuma yaren Girka. Domin mutane daga “dukan alꞌummai” su amfana daga Kalmar Allah, ana bukatar a fassara Nassosin zuwa yaruka da yawa. (Matiyu 24:14) Ana kiran littattafai ashirin da bakwai, wato Matiyu zuwa Ruꞌuya ta Yohanna “Nassosin Girkanci na Krista,” domin asali an rubuta su ne a yaren Girka kuma ruhu mai tsarki ne ya ja-goranci Kristocin da suka rubuta su a ƙarni na farko bayan haifuwar Yesu.

Littafi Mai Tsarki​—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta ­Yohanna) ya fara fitowa a Turanci a shekara ta 1950. An fassara shi ne daga rubuce-rubucen yaren Girka na Westcott da Hort, waɗanda suka yi daidai da rubuce-rubucen Girka na asali. Mafassaran juyin Fassarar Sabuwar Duniya sun yi iya ƙoƙarinsu don su fassara nassosin Girkanci daidai. An yi amfani da juyin 2013 na Turanci wajen fassara wannan juyin a Hausa, kuma an yi ƙoƙari don a fassara maꞌanar daidai.

Sunan Allah, wato Jehobah, ya bayyana sau ɗari biyu da talatin da bakwai a Littafi Mai Tsarki​—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna). Da yake tsarkake sunan Allah yana da muhimmanci, kuma mutane suna bukatar su riƙa amfani da sunan don samun ceto, wannan juyin ya maido da sunan nan Jehobah a wuraren da suka bayyana a cikin Nassosi Masu Tsarki.​—Matiyu 6:9; Romawa 10:13.

An ɗauko sunan nan, Fassarar Sabuwar Duniya, daga alkawarin da Allah ya yi na sabuwar duniya inda za a riƙa yin adalci, kuma hakan zai sa dukan ꞌyanꞌadam su amfana. (2 Bitrus 3:13) Mafassaran wannan juyin, suna ƙaunar Mawallafin Nassosi Masu Tsarki, kuma a ganinsu, hakki ne na musamman su fassara tunaninsa da kuma saƙonsa daidai. Fatanmu shi ne wannan juyin zai taimaka wa masu karatu da suke da zuciyar kirki kuma suke ƙoƙari su “samu cikakken ilimin gaskiya.”​—1 Timoti 2:4.