TAMBAYA TA 14
Ta Yaya Za Ka Yi Amfani da Dukiyarka da Kyau?
“Mai yawan son jin daɗi zai talauce; mai son ruwan inabi da māi, ba zai yi arziki ba.”
Karin Magana 21:17
“Mai cin bashi bawa ne ga mai ba da bashi.”
Karin Magana 22:7
“Wane ne a cikinku da yake so ya gina gidan sama, da ba zai fara zaunawa ya yi lissafin nawa ne zai kashe, don ya san ko yana da isasshen kuɗin da zai gama aikin ba? In ba haka ba, zai fara amma ya kasa kammala ginin, kuma dukan mutane da suka ga ginin, za su soma yi masa dariyar reni, suna cewa: ‘Mutumin nan ya fara gini, amma ya kasa kammalawa.’”
“Bayan da suka ci suka ƙoshi, sai Yesu ya ce wa almajiransa: ‘Ku tattara burbuɗin da suka rage, domin kada kome ya lalace.’”

