TAMBAYA TA 20
Ta Yaya Za Ka Amfana Sosai Daga Karatun Littafi Mai Tsarki?
KA AMSA WAƊANNAN TAMBAYOYIN YAYIN DA KAKE KARANTA LITTAFI MAI TSARKI:
Mene ne nan ya koya mini game da Jehobah?
Wace alaƙa ce ke tsakanin wannan sashen da kuma saƙon Littafi Mai Tsarki gabaki-ɗaya?
Ta yaya zan yi amfani da abin da na karanta?
Ta yaya zan yi amfani da waɗannan ayoyin wajen taimaka ma wasu?
“Kalmarka fitila ce ga ƙafafuna, haske ne kuma ga hanyata.”
Zabura 119:105

