Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya

Wane ne Allah?

Hausa
Wane ne Allah?
https://cms-imgp.jw-cdn.org/img/p/1001061100/univ/wpub/1001061100_univ_sqr_xl.jpg
nwt pp. 6-7

TAMBAYA TA 1

Wane ne Allah?

“Bari mutane su san cewa kai wanda sunanka Jehobah ne, kai kaɗai ne Mafi Ɗaukaka a dukan duniya.”

Zabura 83:18

“Ku san cewa Jehobah Allah ne. Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne.”

Zabura 100:3

“Ni ne Jehobah. Sunana ke nan; ba na ba wa kowa ɗaukakata, ko in ba wa siffofi yabon da ya kamata a ba ni.”

Ishaya 42:8

“Duk wanda ya kira ga sunan Jehobah zai sami ceto.”

Romawa 10:13

“Hakika, kowane gida yana da wanda ya gina shi, amma Allah ne ya gina kome.”

Ibraniyawa 3:4

“Ku ta da idanunku sama ku duba. Wane ne ya halicci abubuwan nan? Shi ne Wanda yake musu ja-goranci kamar sojoji, ya san yawansu; yana kiran kowannensu da sunansa. Saboda yawan ƙarfinsa da ikonsa mai ban mamaki, babu ko ɗayansu da ya ɓata.”

Ishaya 40:26