Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya

Wane Saƙo ne Ke Cikin Littafi Mai Tsarki?

Hausa
Wane Saƙo ne Ke Cikin Littafi Mai Tsarki?
https://cms-imgp.jw-cdn.org/img/p/1001061100/univ/wpub/1001061100_univ_sqr_xl.jpg
nwt pp. 12-13

TAMBAYA TA 5

Wane Saƙo ne Ke Cikin Littafi Mai Tsarki?

“Zan sa gāba tsakaninka da macen, da kuma tsakanin zuriyarka da zuriyarta. Zai murƙushe kanka, kai kuma za ka sari diddigen ƙafarsa.”

Farawa 3:15

“Ta wurin zuriyarka, dukan alꞌumman duniya za su samu albarka, saboda ka yi mini biyayya.”

Farawa 22:18

“Mulkinka ya zo. Bari a yi nufinka a duniya kamar yadda ake yin sa a sama.”

Matiyu 6:10

“Ba da daɗewa ba, Allah mai ba da salama zai murƙushe Shaiɗan a ƙarƙashin ƙafafunku.”

Romawa 16:20

“Saꞌad da aka sa dukan abubuwa a ƙarƙashinsa, Ɗan ma da kansa zai miƙa kansa ƙarƙashin ikon Wanda ya sa dukan abubuwa a ƙarƙashinsa, domin Allah ya zama kome ga kowa.”

1 Korintiyawa 15:28

“Allah ya yi alkawuran ga Ibrahim da kuma zuriyarsa ne . . . , wato Kristi. Ƙari ga haka, idan ku na Kristi ne, ku zuriyar Ibrahim ne da gaske.”

Galatiyawa 3:16, 29

“Mulkin duniya ya zama Mulkin Ubangijinmu da na Kristinsa, kuma zai yi sarauta har abadan abadin.”

Ruꞌuya ta Yohanna 11:15

“Sai aka jefa babban macijin zuwa ƙasa, wato macijin nan na tun dā, wanda ake kira Ibilis da kuma Shaiɗan, wanda yake yaudarar dukan duniya, an jefo shi zuwa duniya, kuma an jefo malaꞌikunsa ma tare da shi.”

Ruꞌuya ta Yohanna 12:9

“Ya kama babban macijin nan, wato macijin nan na tun dā, wanda ake kira Ibilis da Shaiɗan, kuma ya ɗaura shi na shekaru dubu ɗaya.”

Ruꞌuya ta Yohanna 20:2