TAMBAYA TA 13
Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Faɗa Game da Aiki?
“Ka taɓa ganin mutumin da ya ƙware a yin aikinsa? Zai tsaya a gaban sarakuna; ba zai tsaya a gaban mutane marasa muhimmanci ba.”
Karin Magana 22:29
“Bari wanda yake yin sata ya daina yin sata; a maimakon haka, bari ya yi aiki da ƙwazo, yana yin ayyuka masu kyau da hannayensa, domin ya samu abin da zai iya rabawa da wani da yake da bukata.”
“Kowane mutum ya ci, ya sha kuma ya ji daɗi don dukan ayyukan da ya yi da ƙwazo. Gama wannan kyauta ne daga Allah.”
Mai-Waꞌazi 3:13

