Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya

Me Zai Faru da Matattu a Nan Gaba?

Hausa
Me Zai Faru da Matattu a Nan Gaba?
https://cms-imgp.jw-cdn.org/img/p/1001061100/univ/wpub/1001061100_univ_sqr_xl.jpg
nwt p. 23

TAMBAYA TA 12

Me Zai Faru da Matattu a Nan Gaba?

“Kada ku yi mamakin wannan, domin lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa kuma su fito.”

Yohanna 5:28, 29

“Za a yi tashin matattu na masu adalci da na marasa adalci.”

Ayyukan Manzanni 24:15

“Na ga matattu manya da ƙanana suna tsaye a gaban kujerar mulkin, kuma aka buɗe naɗaɗɗun littattafai. Amma sai aka buɗe wani naɗaɗɗen littafi, wato naɗaɗɗen littafin rai. Aka yi wa matattu shariꞌa bisa ga abubuwan da aka rubuta a cikin naɗaɗɗun littattafan nan daidai da ayyukansu. Sai teku ta fitar da matattu da ke cikinta, kuma mutuwa da Kabari sun fitar da matattu da ke cikinsu, aka kuma yi ma kowannensu shariꞌa daidai da ayyukansa.”

Ruꞌuya ta Yohanna 20:12, 13