TAMBAYA TA 7
Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Annabta Game da Zamaninmu?
“Alꞌumma za ta yaƙi alꞌumma, mulki kuma ya yaƙi mulki . . . Duk abubuwan nan su ne somawar azaba.”
“Annabawan ƙarya da yawa za su taso kuma su ruɗi mutane da yawa. Da yake mugunta za ta ci-gaba da ƙaruwa, ƙaunar mutane da yawa za ta yi sanyi.”
“Idan kun ji ana yaƙe-yaƙe da kuma labaran yaƙe-yaƙe, kada hankalinku ya tashi; domin dole ne abubuwan nan su faru, amma ƙarshen bai zo ba tukuna.”
“Za a yi munanan girgizar ƙasa, kuma za a yi ƙarancin abinci da annoba a wurare dabam-dabam. Mutane za su ga abubuwan da za su ba su tsoro kuma za su ga alamu masu ban mamaki daga sama.”
“A kwanakin ƙarshe, lokuta masu tsanani da wuyan shaꞌani za su zo. Gama mutane za su zama masu son kansu, masu son kuɗi, masu taƙama, masu ji da kansu, masu saɓo, marasa biyayya ga iyaye, marasa godiya, marasa aminci, marasa ƙaunar mutane, marasa son yin yarjejeniya, masu ɓata suna, marasa kamun kai, masu mugunta, marasa son nagarta, masu cin amana, masu taurin kai, masu cike da girman kai, masu sa jin daɗi a gaba maimakon ƙaunar Allah, suna nunawa a fili cewa suna bauta wa Allah, amma ba sa nuna hakan ta wurin halayensu.”

