TAMBAYA TA 17
Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai taimaka wa iyalinka?
MAZA/UBANNI
“Hakazalika, mazaje su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikinsu. Duk mutumin da yake ƙaunar matarsa, yana ƙaunar kansa, gama babu mutumin da ya taɓa ƙin jikinsa, amma yana ciyar da shi, yana kuma kula da shi . . . Dole kowannenku ya ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar kansa.”
“Ku ubanni, kada ku riƙa sa yaranku fushi, amma ku ci-gaba da renon su cikin horo da kuma umurnin Jehobah.”
MATA
“Matar kuma ta girmama mijinta sosai.”
“Ku mata, ku miƙa kanku ga mazanku, kamar yadda ya dace da masu bin Ubangiji.”
YARA
“Yara, ku riƙa yi wa iyayenku biyayya yadda Ubangiji yake so, don hakan ya dace a gaban Allah. ‘Ka girmama babanka da mamarka,’ wannan ita ce doka ta farko da ta zo da alkawarin nan cewa: ‘Don ka yi rayuwa mai kyau kuma ka yi tsawon rai a duniya.’”
“Ku yara, ku riƙa yi wa iyayenku biyayya a cikin kome, don hakan na faranta ran Ubangiji.”

