TAMBAYA TA 16
Me Za Ka Yi Idan Kana Fama da Yawan Damuwa?
“Ka danƙa wa Jehobah nawayarka, kuma zai taimaka maka. Ba zai taɓa barin mai adalci ya faɗi ba.”
Zabura 55:22
“Shirye-shirye na mai ƙwazo sukan sa ya yi nasara, amma duk masu yin abu da gaggawa lallai za su talauce.”
Karin Magana 21:5
“Kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai. Kada ka damu, gama ni ne Allahnka. Zan ƙarfafa ka, in kuma taimake ka, zan riƙe ka da hannun damana na adalci.”
Ishaya 41:10
“Wane ne a cikinku ta yawan damuwa zai iya ƙara ko minti ɗaya ga tsawon rayuwarsa?”
“Saboda haka, kada ku riƙa yawan damuwa game da gobe, don gobe ma yana da abubuwan da za ku damu a kan su. Kowace rana na da nata isasshen matsaloli.”
“Ku . . . tabbatar da abubuwan da suka fi muhimmanci.”
“Kada ku damu a kan kowane abu, amma a cikin kowane abu, ku gaya wa Allah abubuwan da ke damun ku ta wurin adduꞌa da roƙe-roƙe sosai tare da godiya; kuma salamar Allah wadda ta fi dukan ganewar ɗanꞌadam, za ta kāre zukatanku da tunaninku ta wurin Kristi Yesu.”

