TAMBAYA TA 15
Me Zai Taimaka Maka Ka Zama Mai Farin Ciki?
“Gwamma a ci abinci kaɗan a wurin da akwai ƙauna, da a ci naman bijimi mai ƙiba a wurin da akwai ƙiyayya.”
Karin Magana 15:17
“Ni Jehobah, ni ne Allahnku, Wanda yake koya muku don ku amfana, Wanda yake nuna muku hanyar da za ku bi.”
Ishaya 48:17
“Waɗanda suka san cewa suna bukatar ja-gorancin Allah, suna farin ciki, domin Mulkin sama nasu ne.”
“Dole ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”
“Abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma ku yi musu hakan.”
“Masu farin ciki ne waɗanda suke jin kalmar Allah, kuma suke aikata ta!”
“Ko da mutum yana da dukiya da yawa, ba za su ba shi rai ba.”
“Saboda haka, idan muna da abin da za mu ci da rigunan sakawa, za mu gamsu da waɗannan abubuwa.”
“Bayarwa tana sa farin ciki fiye da karɓa.”

