TAMBAYA TA 8
Allah ne Yake Jawo wa ꞌYanꞌadam Wahala?
“Ba zai taɓa yiwu Allah ya yi mugunta ba, ko Maɗaukaki ya yi abu marar kyau ba!”
Ayuba 34:10
“Saꞌad da mutum yake shan wahala, kada ya ce: ‘Allah ne yake jarraba ni.’ Domin ba za a iya jarrabtar Allah da ayyukan mugunta ba, shi kuma ba ya jarrabtar kowa.”
“Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin yana kula da ku.”
“Jehobah ba ya ɓata lokaci wajen cika alkawarinsa, kamar yadda wasu suke tsammani, amma yana haƙuri da ku ne domin ba ya so wani ya hallaka, sai dai yana so kowa ya tuba.”

