TAMBAYA TA 9
Me Ya Sa ꞌYanꞌadam Suke Shan Wahala?
“Ba a kullum ba ne mai saurin gudu yake yin nasara a tsere, ba a kullum ba ne mai ƙarfi yake yin nasara a faɗa, ba a kullum ba ne mai hikima yake samun abinci, ba a kullum ba ne mai basira yake samun arziki, ba a kullum ba ne masu ilimi suke yin nasara, domin lokaci da kuma abubuwan da ba su yi tsammani ba sukan same su duka.”
Mai-Waꞌazi 9:11
“Zunubi ya shigo duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi, ta haka mutuwa ta shafi dukan mutane da yake kowa ya yi zunubi—.”
“Saboda wannan ne aka bayyana Ɗan Allah, domin ya rushe ayyukan Ibilis.”
“Dukan duniya tana ƙarƙashin ikon mugun nan.”

