Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya

Abubuwan da Za Mu Koya Daga Kalmar Allah

Hausa
Abubuwan da Za Mu Koya Daga Kalmar Allah
https://cms-imgp.jw-cdn.org/img/p/1001061100/univ/wpub/1001061100_univ_sqr_xl.jpg
nwt p. 5

Abubuwan da Za Mu Koya Daga Kalmar Allah

Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da saƙo daga Allah, ko kuma kalmarsa domin mu a yau. Yana koya mana yadda za mu yi rayuwa mai kyau da kuma abin da za mu yi don Allah ya amince da mu. Ƙari ga haka, yana amsa tambayoyin nan:

YADDA ZA KA IYA SAMUN NASSI A CIKIN LITTAFI MAI TSARKI

Littafi Mai Tsarki ya ƙunshi ƙananan littattafai guda sittin da shida. An raba shi kashi biyu zuwa: Nassosin Ibrananci da Yaren Aramaik (“Tsohon Alkawari”) da kuma Nassosin Girkanci (“Sabon Alkawari”). Nassosin Girkancin ya ƙunshi littattafai ashirin da bakwai kuma ya soma ne da ba da tarihin Yesu Kristi. An kasa kowanne cikin littattafai da ke cikin Littafi Mai Tsarki zuwa surori da ayoyi. Idan aka rubuta wani nassi, lamba ta farko da ke bin bayan sunan littafin ita ce sura, saꞌan nan lamba ko kuma lambobi da ke biye da wannan su ne ayoyi. Alal misali, Matiyu 1:1 yana nufin littafin Matiyu sura 1, aya 1.