9 GA OKTOBA, 2020
RASHA
Wani Kotu a Rasha Ya Kama Ma’aurata Guda da Laifi Kuma Ya Hukunta Cewa Za A Rika Sa Musu Ido
A ranar 9 ga Oktoba, 2020, Kotun Gundumar Sverdlovskiy da ke birnin Kostroma ya kama Dan’uwa Sergey Rayman da matarsa Valeriya da laifi. Ya kuma hukunta cewa Dan’uwa Sergey Rayman zai yi shekara takwas ana sa masa ido, matarsa kuma za ta yi shekara bakwai. Cikin dukan ’yan’uwanmu da aka yi musu irin wannan hukuncin a Rasha, hukuncin da aka yi musu ne ya fi tsawo, tun lokacin da Kotun Koli ya hana aikinmu a shekara ta 2017. Yanzu dai ba za a kai Dan’uwa Rayman da matarsa kurkuku ba.