Koma ka ga abin da ke ciki

Hagu zuwa dama: ’Yar’uwa Silaeva da ’Yar’uwa Shamsheva da Dan’uwa Khokhlov da Dan’uwa Zhinzhikov a kotu a ranar 28 ga October, 2020

28 GA OKTOBA, 2020
RASHA

Wani Kotu a Rasha Ya Goyi Bayan Hukuncin da Aka Yanke wa Wasu ’Yan’uwa Maza Biyu da Mata Biyu

Wani Kotu a Rasha Ya Goyi Bayan Hukuncin da Aka Yanke wa Wasu ’Yan’uwa Maza Biyu da Mata Biyu

A ranar 28 ga Oktoba, 2020, Kotun Yankin Bryansk ya goyi bayan shari’ar da aka yanke wa Dan’uwa Vladimir Khokhlov da Eduard Zhinzhikov da ’Yar’uwa Tatyana Shamsheva da Olga Silaeva cewa suna da laifi. Dā an yanke wa kowannensu hukuncin yin tsakanin shekara daya zuwa shekara daya da wata uku a kurkuku. Amma da yake an jima sosai ana tsare da su kafin wannan hukuncin, ba za a kai su kurkuku ba. Wannan hukuncin ya sa za a ci gaba da yi wa ’yan’uwanmu kallon masu aikata laifi. Amma suna farin ciki cewa yanzu an ’yantar da su. Ba a ba wa wadanda suka kai karar su damar sake daukaka kara don neman a kara hukuncin da aka yi musu ba.

Kafin a yi musu hukunci na farko, ’yan’uwa mazan sun riga sun yi kwana 316 suna a tsare, matan kuma kwana 245. Bayan da aka sake su, an gana da ’yan’uwa matan a cikin bidiyon 2020 Karin Bayani na #5 Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu. Sun bayyana cewa yin addu’a, da karanta Littafi Mai Tsarki, da halin nuna godiya, ya taimaka musu su ci gaba da yin farin ciki yayin da suke jimre wannan yanayin.