27 GA SATUMBA, 2018
LABARAN DUNIYA
Kotuna da ke Jamhuriyar Czech da Sulobakiya Sun Wanke ’Yan’uwanmu Daga Laifi
An Wanke Wadanda suka ki shiga soja daga laifi bayan an yi Shekaru da Yawa Ana Tuhumarsu.
A cikin ’yan shekaru da suka shige, kotuna da ke Jamhuriyar Czech da Sulobakiya sun wanke ’yan’uwanmu daga laifi. An tuhumi wadannan ’yan’uwa a dā da laifin kin shiga soja ko kuma don sun yi wa’azi. A yanzu, ba laifi ba ne mutum ya ki shiga soja ko kuma ya yi wa’azi. Daya cikin karar da aka kai shi ne na wani dan’uwa da aka hukunta a shekara ta 1925. (Ka duba labarin Dan’uwa Martin Boor, wanda aka ce ba shi da laifi bayan shekara 90 da aka hukunta shi.) Alkalan kotunan sun ce ’yan’uwanmu suna da ’yanci kin shiga soja kuma ba laifi ba ne su yi wa’azi.
A lokacin gwamnatin Kwaminis, an kama da kuma hukunta ’yan’uwanmu da yawa da suka ki shiga soja. Amma daga watan Mayu 2017, Kotun Koli na Jamhuriyar Czech ta kawar da hukuncin da aka yanke wa ’yan’uwanmu 45. A watan Oktoba 2017, Kotun Koli ta wanke Dan’uwa Martin Magenheim daga laifi. An saka wannan dan’uwan a kurkuku ne a 1978 don yana wa’azi.
A Sulobakiya, da ake shari’a a District Court na yankin Bratislava na Daya, an wanke wa ’yan’uwanmu hudu cewa ba “laifi” ba ne kin shiga soja. Kuma kotun da ke Trenčín ta wanke wani dan’uwa daga laifi. A shekara ta 1974, an hukunta wata ’yar’uwa mai suna Eva Borošová don tana wa’azi, amma kotun da ke Rimavská Sobota ya wanke ta daga laifi. An saka Dan’uwa Miloš Išky Janík sau da yawa a kurkuku domin ya ki ya yi wa gwamnati aiki a hanyar da yake ganin ba ta dace ba. Amma, a ranar 9 ga Janairu, 2018, kotun da ke Michalovce ya ce hukunci da aka yanke masa a 1993 ba daidai ba ne kuma aka canja hukuncin.
Wani lauya mai suna André Carbonneau da ke wakiltar Shaidun Jehobah ya ce: “An hukunta Shaidu da yawa a shekaru da suka shige don sun ki shiga soja ko domin imaninsu ko kuma don suna wa’azi. Yayin da wadannan kotuna suka yarda cewa yadda suka hukunta wadannan Shaidu ba daidai ba ne, sun nuna cewa kowa yana da ’yanci bin imanin da yake so kuma ya zabi yadda zai yi ibada. Wadannan kotuna suna kokari su daidaita muguntar da suka yi a dā ga mutanen da suka ki shiga soja. Don a lokacin, hukumomi da yawa ba sa amincewa da ’yancin ’yan Adam. Ta yin hakan wadannan kotuna suna kafa misali mai kyau ga wasu kasashe da ba sa amincewa da ’yancin ’yan Adam. Kari ga haka, wadannan kotunan sun wanke sunayen ’yan’uwanmu marasa laifi da aka bata. Muna farin ciki sosai don hakan, tun da yake Littafi Mai Tsarki ya ce suna mai kyau abu ne mai tamani sosai.”—Mai-Wa’azi 7:1.