Koma ka ga abin da ke ciki

28 GA YUNI, 2018
South Korea

Kotun Tsara Doka Na Koriya ta Yanke Hukunci: Dokar Kin Yarda a Yi Wani Aiki Dabam Ba ta Dace Ba

Kotun Tsara Doka Na Koriya ta Yanke Hukunci: Dokar Kin Yarda a Yi Wani Aiki Dabam Ba ta Dace Ba

A Ranar 28 ga Yuni, 2018 ne Kotun Tsara Doka a Koriya ta Kudu ta sanar cewa dokar tilasta wa mutane su shiga soja a kasar Koriya bai dace ba. Don dokar ta hana wadanda sun ki shiga soja saboda imaninsu su yi wani aiki dabam ba. Wannan gagarumin mataki da aka dauka yana da muhimmanci sosai domin zai sa a canja dokar da aka kafa shekaru 65 da suka shige cewa za a sa duk wanda ya ki shiga soja saboda imaninsa a kurkuku.

Tun shekara ta 1953, ’yan’uwanmu sama da 19,300 ne aka saka a kurkuku wanda in an hada shekarun da suka yi a kurkuku, ya fi shekaru 36,700. A yanzu Kotu Koli na Koriya za ta yi amfani da wannan dokar ta yanke shawara a kan duk wanda ya ki shiga soja saboda imaninsa. Kari ga haka, an umurce masu tsara doka na kasar Koriya su tsara wasu ayyuka daga ranar 31 ga Disamba, 2019 da masu kin shiga soja saboda imaninsu za su rika yi.

Muna taya ’yan’uwanmu na Koriya murna domin yanzu an soma daukan matakan kawo karshen rashin adalci da ake yi musu tun shekaru da yawa.—Karin Magana 15:30.