23 GA NUWAMBA, 2020
South Korea
An Kafa Tarihi Mai Muhimmanci: An Soma Aikin Farar Hula Maimakon Aikin Soja a Koriya Ta Kudu
Wannan ne karo na farko da gwamnatin Koriya ta Kudu ta yarda ma wadanda suka ki shiga soja saboda imaninsu su yi aikin farar hula. A ranar 26 ga Oktoba, 2020, ’yan’uwa 63 ne suka amince su yi irin wannan aikin, har tsawon shekara uku a gidajen gyaran hali guda biyu. Ayyukan da za a ba su sun hada da, dahuwa da yin sayayya da koyarwa da tsabtace wuri da kula da lafiya da kuma yin gyare-gyare. A yanzu dokar da aka ba su shi ne, za su yi wata biyu ba su bar kurkukun ba. Bayan haka za a dinga barin su su je taro da kuma wa’azi muddin sun gama aikin da aka ba su. Amma dole su dawo kafin karfe 9 na dare.
Dan’uwa Kim Hyun-soo, yana cikin ’yan’uwa 63 da za su yi aikin, kuma ya ce: “Ko da yake aikin bai cika duka ka’idodin da aka tsara don irin ayyukan nan ba, na yarda in yi shi domin bai shafi aikin soja ba.”
Muna da tabbaci cewa ’yan’uwanmu masu aminci a Koriya ta Kudu za su ci gaba da daukaka Jehobah ta wurin “ayyuka masu kyau” da suke yi.—Matiyu 5:16.
Dan’uwa Park Jae-hyuk yana ban kwana da ’yan gidansu kafin ya tafi aikin farar hula da aka ba shi
Dan’uwa Lee Sang-joon yana shirin tafiya ya bar gida (hagu). Iyayen Dan’uwa Kim Yeong-hoon suna rungumar sa (dama)
Dan’uwa Jeong Yeo-gyeom yana barin gida don ya tafi aikin farar hula da aka ba shi