A yunkurinsu na hana ‘yancin gudanar da addini, hukumomi a Rasha sun shigar da kara don a ba su damar hada juyin New World Translation of the Holy Scriptures a cikin jerin littattafai da ke dauke da tsattsauran ra’ayi. Za a soma sauraron shari’ar a ranar 15 ga Maris, 2016. A shekarar da ta shige, hukumomin kwastan sun hana shigar da wannan juyin Littafi Mai Tsarki, abin da ba a taba yi ba a Rasha. Wannan matakin da suka dauka, rashin imani ne da kuma rashin daraja Littafi Mai Tsarki na Kiristoci.

Dokar kasar Rasha ta hana saka Littafi Mai Tsarki a cikin jerin littattafai da ke koyar da tsattsauran ra’ayi. Amma masu shigar da karar, wato, Leningrad-Finlyandskiy Transport Prosecutor, sun dauki abin da wani mutum da bai kware a ilimin harsuna ba ya fada game da wannan juyin. Idan masu shigar da karar sun yi nasara a kotu, za a hana rarraba juyin New World Translation a kasar Rasha.