Koma ka ga abin da ke ciki

18 GA YULI, 2017
RASHA

Kotun Koli Na Rasha Ta Sake Karfafa Hukuncin da Aka Yi wa Shaidun Jehobah Kwanakin Baya

Kotun Koli Na Rasha Ta Sake Karfafa Hukuncin da Aka Yi wa Shaidun Jehobah Kwanakin Baya

A ranar 17 ga Yuli, 2017, Kotun Koli na Rasha ya yi banza da yarjejeniyar da Rasha ta yi na daukaka ’yancin bin addini ga kowane dan Adam kuma ya sake karfafa hukuncin da ya yanke wa Shaidun Jehobah a Rasha cewa ayyukansu ba su dace ba. Hukuncin da Kotun ya yanke ya hana Shaidun Jehobah yin ayyukan ibadarsu a kasar.

Lauyoyi uku a Kotun Kolin sun ki saurarar karar da Shaidun suka shigar kuma suka amince da hukuncin da Alkali Yuriy Ivanenko ya yanke a ranar 20 ga Afrilu. Ya yanke hukuncin nan ne bisa abin da Hukumar Shari’ar ta ce. Hukumar ta ce “a rufe Ofishin Shaidun Jehobah da ke Rasha kuma a kwace duk abubuwan da suke amfani da su wajen yin ibada kuma a mika su ga Gwamnatin Tarayya ta Rasha.”

Wasu lauyoyin da suka wakilci Ofishin Shaidun Jehobah

Wannan hukuncin ya saka rayukan Shaidun Jehobah a Rasha fiye da 175,000 cikin hadari. Wani da yake wakiltar Shaidun Jehobah mai suna Philip Brumley ya ce: “Shaidun Jehobah a fadin duniya sun damu sosai game da lafiyar ’yan’uwansu da ke Rasha. Lauyoyin ba su ce kome game da wulakancin da ake yi wa Shaidun Jehobah a Rasha ba kuma sun ba da goyon baya da a ci gaba da tsananta musu. Don haka, an tsani Shaidun Jehobah sosai a nasu kasar.”

Shaidun Jehobah a Rasha sun roki Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam da kuma Kungiyar Majalisar Dinkin Duniya da ke Kāre Hakkin ’Yan Adam da su sa a yi musu adalci a hukuncin nan. Kafin lokacin, ’yan’uwansu a fadin duniya suna nan suna addu’a ga Jehobah da ya sa gwamnatin Rasha ta canja ra’ayinta game da hukuncinta kuma ta daraja ’yancin Shaidun Jehobah don su ‘zauna lafiya, rai kwance, suna bin Allah sosai,’ kamar yadda littafin 1 Timotawus 2:2 ya ce.